Kyawawan Halaye 2

Kyawawan Halaye 2

Kamalar Mutum Halaye Nagari – 2

 

Kyawawan Dabi’u

Kyawawan dabi’u su ne ruhin shari’a, kuma asasin addini, babu wani Annabi da ya zo sai da ya yi kira tsakanin mutane da kyawawan dabi’u, da kuma tilascin tsarkake su daga abin da yake iya kai su ga aikata munanan dabi’u, da kuma nesantar da su daga abin da yakan iya lalata hadafinta, sai ya zana mana tafarki da hanya, ya gina mana dokoki da zamu yi amfani da su domin kawo canji ga mutum zuwa ga mafi kamalar samuwa wacce mutum zai dogara da ita domin ya kai ga matsayi mai girma na kyawawan halayen, ya kuma zamanto daga zababbu tsarkaka daga bayinsa.

Ilmin Kyawawan Dabi’u

Ilmin kyawawan dabi’u ilmi ne da yake da ma’auni da za a iya dogara da shi, shi ne tattararrun dokoki da ya kamata dabi’ar dan adam ta kasance a kanta bisa wadannan dokokin kamar yadda aka gindaya a zance ko a aiki ko a zuciya. Da wadannan ma’aunai zamu zana hanyar kyawawan dabi’u abin yabo, mu kuma yi kokarin iyakance hadafinsu da abubuwan da suka ginu a kan su.

 

Kyawawan Dabi’un Musulunci

Kyawawan dabi’u su ne halayen rai da suke sanya ta aikata kyakkyawa ga mutane, da kyautata musu a magana, aiki, nufi, cudanya, sakin fuska, da makamantansu. Muna iya cewa kyawawan dabi’u sun shafi gyara kai ne domin a samu daidaikun mutane na gari a cikn al’umma don samar da jama’a saliha mai wadata. Allah da Manzonsa sun yabi kyawawan dabi’u da kalmomi masu girma, Allah yana cewa: "Lallai kai kana da halayen kirki nagari manya". Kyawawan dabi’u suna da alamomi kamar sakin fuska, da magana mai dadi, da zaman lafiya da mutane .

Dabi’un musulunci su ne tattararrun zantuttuka da ayyuka na zahiri da na badini da suka doru bisa ka’idoji, da kuma ayyuka madaukaka da ladubban da suka doru a kansu, wadanda suka dogara a kan akida da shari’ar musulunci da dogaro mai karfi daga kur’ani mai girma da sunnar Manzon Allah (s.a.w) da imamai tsarkaka (a.s). Kyawawan dabi’u a musulunci shi ne babban bangaren addini na aiki, kuma shi ne kashin baya da ruhin addini ma .

Hadafin Kyawawan Dabi’u

Hadafin kywawan dabi’u shi ne kare ayyukan mutum, na zahiri da na badininsa da kuma tsarkake tunaninsa da samuwarsa daga karkacewa; wato hadafin shi ne samar da mutum ko kuma al’ummar da take takawa zuwa ga kamala, ta kuma tsayar da adalci, da rikon amana, da taimakekeniya, da kuma kama hannun juna domin kare rayuwar al’umma daga fadawa cikin fasadi da zalunci da sauran miyagun al’adu da dabi’u.

Da lizimtar kyawawan dabi’u ne mutum ko al’umma zata samu kariya daga karkacewa da kuma lizimtar tafarkin shiriya na gaskiya. Hadafin ilimin kywawan dabi’u bai takaita a kan daidaikun mutane kawai ba, ya hada har da al’ummu da jama’u daban-daban, ta yadda kyawawan dabi’u zasu mamaye rayuwarta da siffofinta domin kai wa ga mafi daukakar ci gabanta.

Wani baiti yana cewa:

Al’umma kawai ita ce kyawawan dabi’unta matukar ta wanzu

Idan kuwa al’umma ta kau to kyawawan dabi’unta ne suka kau

 Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Ƙara sabon ra'ayi