Kyawawan Halaye

Kyawawan Halaye

Kamalar Mutum Halaye Nagari

 

Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zaba

Kuma lalle ni mai gafara ne ga wanda ya tuba ya yi imani, kuma ya aikata aikin k'warai, sa’annan kuma ya nemi shiryuwa . 

 

Shimfida

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai don ya cika kyawawan dabi’u da halaye na gari, wanda Ubangijin kasa da sama ya siffanta shi da “Hakika kai kana da kyawawan dabi’u masu girma” .

A kyawawan halaye babu wanda ya kai annabin rahama mai daraja, don haka duk wani abu da muka gani na aibi da aka kawo shi ko a littafin hadisi ne matukar yana nuna aibata annabin rahama to ba shi da wani inganci. Manzon Allah (s.a.w) shi ne wanda mutane masu neman daukaka suke koyi da shi.

Da Allah ne muke neman taimako a kan kawukanmu da kuma dukkan abin da ya halitta gaba daya, tsira da aminci su tabbata a kan wanda ubangijin halitta ya siffanta shi da cewa shi yana da kyawawan dabi’u, sai ya aiko shi domin ya cika mafi kyawawan dabi’u, Annabin rahama da mutuntaka Muhammad dan Abdullahi (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s).

Al’amarin kyawawan dabi’u al’amari ne na ‘yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama’a ne da a cikinsu akwai na nesa, na kusa, karami, babba, mace, namiji, mai neman sani, malami, mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu’amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah ya yi umarni.

Sau da yawa masu fikirori da ra'ayi sukan yi nuni da cewa kyawawan halaye sun kebanci mutum ne don gyara kansa, kuma wasu mutane suka dauka lamarin halaye na gari ya kebanta da mutum ne kawai ba tare da la'akari da al'ummar da yake rayuwa cikinta ba. Sai dai wannan fahimta ce gurguwa domin kyawawan halaye duk da sun ta'allaka da gyara kai, sai dai gyaran kai ne da bai fita daga abin da ya shafi lamarin mutane ba.

Domin misali idan mutum ya kasance mai kyawawan halaye ya kasance mai gaskiya da rikon amana, to zai samu gyara a kan kansa, kuma al'umma zata samu nutsuwa da amintuwa daga duk wani sharri daga gare shi, kuma ba zata samu komai daga gare shi ba sai alheri. A nan zamu ga cewa gyaran da ya samu da tsarkin da yake da shi, da kyawun halin da ya samu sun yi tasiri a kansa kai tsaye, kuma sun amfani al'ummarsa kai tsaye, don haka ke nan suna da alaka da al'ummarsa kai tsaye ma.

Don haka ne ma kyawawan dabi’u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu’amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu’amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka’idar “Yin mu’amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu’amala da kai”. Ko kuma “Kamar yadda ka yi za a yi maka” .

Saboda haka mutum ba ya wadatuwa ga barin dabi’ar da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al’ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.

Wannan shi ne abin da ake kira (Kyawawan dabi’u) wato "Akhlak” Wanda ya kasu zuwa na fikira ko nazari (theorical) da na aiki (practical), wanda shi ne zamu karfafa magana kansa a nan. A littafinmu na gaba mai zuwa kuwa zamu karfafi bangaren (Halaye a Nazari) "theorical". Don haka ne zamu kutsa bincike kan abubuwan da suke wajibi ne a nisatar da kai daga yin su, kamar karya, ha’inci, hassada, riya, rudin kai, jiji da kai, mugun kuduri, giba, a matsayinsu na daudar da take addabar ran mutum, sannan sai bahasin siffantuwa da gaskiya, amana, burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi’u a matsayin kayan ado da mutum zai kwalliyar ruhinsa da su. Sai ya siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da ‘yan’uwa, da makwabta, da na gefe, da al'ummar kasarsa da duniya baki daya, wannan shi ne ake kira [Ilimin] Kyawawan Halaye na aiki.

Da mun kula mun yi la’akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi’u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda sababin aiko shi ya zama domin ya cika manyan dabi’u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa da amana da gaskiya kafin aiko shi saboda gaskiyar zancensa da rikon amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: “Lallai kai kana da kyawawan dabi’u masu girma” .

Ashe ke nan kyawawan dabi’u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen ‘yan Adam Muhammad (s.a.w).

Wannan rubutu zai kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi’un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko’ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci ta hanyar mutanen da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga gare su. Musulunci addinin kyawawan dabi’u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna.

 Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Ƙara sabon ra'ayi