Saudiyya da Isra'ila
Gidan radiyon Haramtacciyar kasar Isra'ila ya bayar da wani rahoto a jiya da ke cewa, gwamnatin Saudiyya ta kulla cinikin sayen wasu makamai daga gwamnatin Isra'ila a kan kudi dalar Amurka miliyan 50, domin aike wa da su zuwa ga masu tayar da kayar baya a cikin kasar Syria. Mahukuntan na Saudiyya dai har yanzu ba su ce uffan a kan wannan rahoto ba. Rahoton ya ce cinikin ya hada da makamai da ake amfani da su domin tarwatsa tankokin yaki da kuma kai hare-hare, gami da motoci masu sulked a ake dora wa manyan bindigogi, tun kafin wanann lokacin dai jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto makamancin haka, inda ta ce tana da cikakken bayani kan yadda gwamnatin Saudiyya take jigilar 'yan kungiyar Alkaida daga kasashen duniya daban-daban tana kais u Syria domin kai hare-hare da sunan yaki da gwamnatin basher Assad. A bangare guda kuma rundunar sojin kasar ta Syria ta sanar da gagarumin ci gaban da aka samu a cikin kwanaki biyu da suka gabata a kan kungiyoyin 'yan ta'adda da ke dauke da makamai a kasar, inda aka kwace wasu daga cikin yankunan da suke da a cikin gundumar Homs da kuma Aleppo, tare da kashe wani adadi mai yawa daga cikinsu da kuma kame wasu.
Ƙara sabon ra'ayi