Rikicin Guinea
Ma'aikatar shari'ar kasar Guinea Conakry ta sanar da cewar ta fara gudanar da bincike kan musabbabin bullar rikicin kabilanci da ya lashe rayukan mutane akalla 54 a yankunan da suke kudu maso gabashin kasar.
Kakakin ma'aikatar shari'ar kasar Guinea Conakry Muhammad Bouwighi a yau Laraba ya bayyana wa manema labarai cewa; an fara gudanar da bincike kan musabbabin bullar rikicin kabilanci da ya lashe rayukan mutane tare da jikkata wasu masu yawa musamman a garin Nzerekore da kauyukan Beyla da kuma Koule da suke kudu maso gabashin kasar Guinea Conakry.
Ƙara sabon ra'ayi