Yakin Siriya
Sojojin Syria sun sanar da samun nasarar kame daya daga cikin manyan jagororin kungiyar Nusra Front reshen kungiyar Alqaeda a yankin Sham da ake kira 'yan tawayen Syria. Kamfanin dilalncin labaran SANA ya nakalto daga rundunar sojin kasar ta Syria cewa, an kame jigon na kungiyar alqaeda ne a kusa da hubbaren Sayyidah Zainab (AS) da ke kusa da birnin Damscus, an kuma kashe wasu mayaka 49 dukkaninsu 'yan kasashen ketare da suke tare da shi. Wasu rahotannin kuma sun tabbatar da cewa sojojin na Syria sun kwace iko da garin Baniyas da ke cikin gundumar Tartus, bayan fatattakar 'yan ta'adda daga garin tare da kashe wani adadi mai yawa daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka mika kansu da makaman da ke hannunsu.
Ƙara sabon ra'ayi