Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 2

Littafi: Hakikar Shi'anci
Amsar soke-soke kan Ismar Ma'asumai - 2
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Ismar Annabawa Da Dalilanta Na Hankali
Dalili Na Farko:
Allma Hilli yana cewa a cikin littafain sa Al’alfain: Samammu cikin samuwar su da rashin samuwar su suna bukatar mai samar da su wanda ba irin jinsin su ba domin da zai kasance daga jinsin su, da zasu bukaci wani mai samarwar daban wanda samuwar sa ta tsayu da shi kan- kan sa (wanda ya dogara da kan sa), kuma wanda ba samar da shi aka yi ba, kuma samun kuskure daga dan Adam abu ne mai yiwuwa, idan kuma muka so mukawar da kuskure daga abin samarwa ya zama wajibi mukoma zuwa wanda ya wofin ta daga sabo wanda shi ne Ma’asumi, kuma ba zai yiwu mu kaddara rashin ismar sa ba saboda zai kai mu ga tasalsul ko dauri, amma tasalsuli, lalle idan Imami bai zamo Ma’sumi ba zai bukatu zuwa wani Imamin daban, domin dalilin da ya bukatar da samuwar sa shi ne, halarcin yin kuskuren mutane, don haka da yin kuskure zai halatta a gare shi to da ya bukaci wani Imamin daban, idan ya zamo na biyun ya zama ma’asumi to! In ba haka ba wannan zai lazimta mana tasalsuli. Amma dauri saboda bukatuwa zuwa Imami, da bai zamo Ma’asumi ga mutane ba da ya yi kaikawo a kan daidai, tare da bukatuwar mutane zuwa yin koyi da shi.
Dalili Na Biyu
Shi'a suna cewa: Lalle ma’anar Imami ta tattaro ma’anar isma, domin Imami a luga shi ne wanda ake yin koyi da shi: Kamar (misalin), mayafi suna ne abin da ake yafawa, da ya halallta ga Imami ya yi zunubi, a yayin da ya yi zunubi, ko dai a yi koyi da shi ko kuma kada a yi, idan na farko ne to ke nan Allah Madaukaki ya yi umarni da a yi zunubi, wannan kuma korarre ne, idan kuma na biyun ne imamin ya fita daga kasancewar sa Imami, kuma kawar da tanakudi tsakakin wajabcin kasancewar sa wanda za a yi koyi da shi, da kuma wajabcin yin umarni da kyakykyawa da yin hani daga mummuna abu ne dab a zai yiwu ba, sai dai in za a yi tasauwurin cewa lalle isma tana cikin mafhumin imamanci kuma ta lazimci samuwar sa.
Dalili Na Uku
Imami hujjar Allah ne a wajen isar da sakon shari’a ga bayi kuma shi ba kawai yana kusantar da bayi zuwa yin biyayya kadai ba ne, sannan ya nisantar da su daga sabo ta bangaren kasancewar sa mutum ba ne kadai, ba kuma don yana shugaba ba, domin sashin shuwagabannin da suka yi da’awar Imamanci sun kasance fajiran da bai halatta a yi koyi da su ba , idan suka yi umarni da a yi biyayya ga Allah sun zama matabbatar fadin Allah Madaukaki:"Shi kwa yi umarni da kyakykyawa sannan ku manta da kanku" surar Bakara/44.
A irin wannan yanayin baligi ba zai amintu da maganar su ba kuma yana da uzuri, ka ga ya tabbata ke nan don a kusanta mutane da Allah ne ba kawai don Imami yana Imami ba, kadai yana zamowa ma’asumi ne domin kada mutane su zama suna da uzurin saba masa, domin gasgatawa ga fafin Allah Madaukaki "domin kada mutane su zama suna da uzuri akan Allah bayan aiko manzanni". Surar Nisa’i/165. Kuma Imamai hujjojin Allah ne kamar dai manzanni daidai- wa- daidai domin Allah ne ya nada Imami domin ya shiryar da mutane.
Wadannan dalilai guda uku ke nan daga cikin da yawa daga dalilan hankali wadanda suka dogara da su wajen kafa hujja da dalili a kan Isma.

Hujjojin Nakali Kan Ismar Imami
A. Allah madaukaki a cikin surar Bakara aya ta 124 ya ce da Annabin sa Annabi Ibrahim: "lalle zan sanya ka Imami a doron kasa, sai ya ce haka ma daga cikin zuriya ta sai ya ce azzalumai ba za su rabauta da wannan alkawarin nawa ba". Wannan ayar ta yi nuni a kan isma domin mai yin sabo azzalumi ne, ko da kuwa a kan kan sa ne. saboda fadinsa madaukaki "daga cikin su akwai wanda yake zaluntar kansa"32/fadiri.
B. Allah Madaukaki ya ce:"Ya ku wadanda kuka yi imani ku bi Allah da Manzo da shuwagabanni daga cikin ku"49/Nisa’i. A nan hujjar da ke kunshe a cikin wannan ayar ita ce cewa ma’abota al’amarin da ya wajaba a bi su, wajibi ne umarnin su ya zama daidai da hukunce-hukuncen Allah Madaukaki, domin ainihin wannan biyayyar ta zama wajiba a gare su, kuma hakan ba zai taba samuwa ba sai in suna da isma, domin da kuskure zai gangaro daga gare su to da ya zama wajibi a musanta musu wannan kuma yin hakan ya ci karo da umarnin Allah Madaukaki na cewa a yi musu biyayya.
C. Aya ta talatin da biyu ta surar Ahzab da ta sauka a kan Ahlul-baiti tana baya ni ne, a kan ismar su, ita ce: "Lalle Allah yana so ya tafiyar da dauda daga gare ku ya ku `ya`yan gida (na Manzo) kuma ya tsarkake ku tsarkakewa". Bayan ya tabbabta cewa ta sauka a kan Ahlulbaitn da kowanne daga cikin Imam Ahmad Bin Hambali a musnadinsa da Musatadrakus Sahihaini da Durrul Masur da Kanzul ummal da Sunanu Turmuzi, da Tafsirul dabari da Khasa’isul Nisa’i da Tarihi Bagdad, da Istii’ab na Ibn Abdul Bar da Riyadhun Nadhra na Muhibbul Din Addabari da Musnadi Abu Dauda da Usudul gaba, suka zo da nassi a kan su. Kuma dukkanin su sun ce ta sauka a kan Annabi (s.a.w) da Ali (a.s) da Fadima da Hasan da Husain (a.s).
Kuma malamai na ta sa alamar tambaya a kan ma’anar gusar da najasa? domin su tuke zuwa cewa ana nufin kore kowane irin zunubi da kuskure daga garesu kuma irada anan takwiniya (ta halitta) ce ba ta shari’a ba ce, saboda a sarari yake cewa irada ta shari’a dukkanin mutane sun yi tarayya a cikin ta. Kuma bai zama yiwu a gare shi ya jingina da abin da muka fadi a baya ba na cewa lalle isma gudun mawa ce daga Allah da kuma tanadi da dagewa daga bawa ba. Wadannan su ne sashin dalilan Shi'a a kan isma, kuma kamar yadda kake gani dukkanin su an ciro su ne daga Kur'ani da Sunna da kuma hankali, ta wace fuska za a iya jingina wannan da Abdullahi dan Saba’? ina mahallin gasgata wannan daga waccen dangantakar. Lalle mai karatu yana da hakkin ya tambayi wadannan marubutan cewa shin sun leka masdarorin akidar Shi'a a lokacin da su ke yin rubutu a kan ta, ko kuwa, idan har ta farkon ce amsar ta me kuma ya kawo wannan gutsuri tsamar da wannan kuskurarriyan dandantakar, idan kuma ta biyu ce daidai, to mai ya kai su ga yin ruko da abin da ba su da tsinkaye a cikin sa, ashe yanzu ba suda mai tsawatarwa daga cikin ladubba na kyawawan dabi’ar koyarwar Musuluncin da Allah Madaukaki ya tsara a cikin fadinsa: "kada ka tsaya a kan abin da ba ka da ilimi a kan sa lalle ji da gani da zuciya dukkkanin su abababan tambaya ne a kan sa" isra’i/36 a lokaci guda kuma, tafarkin da tsarin koyarwa da amana ta ilimi ta ki ta yardar musu da wannan kage-kagen da kuma dangana abu zuwa ga wanin masdarinsa, idan haka ne ke nan, koda kuwa dalilan lamarin isma ba su zam karbabbu ba, to bai halatta ba a nisanta ta daga masadarin ta zuwa wani mutum na daban wanda gaba da kiyayya ta haifo shi kuma son rai ya fitar da ayyukan sa a fili ba.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi