Ta'addancin su Kardawi
Jami’ar Azhar ta kasar Masar ta yi watsi da kuma nuna rashin amincewarta da kiran da wasu malamai irin su Sheikh Yusuf al-Qardhawi, babban muftin fadar kasar Qatar, suke yi na shailanta jihadi a kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran Fars na nan Iran ya jiyo shafin watsa labarai na al-Ahad, yana cewa jami’ar ta Azhar ta bayyana wannan matsayar ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta nesanta kanta daga wannan kiran da wadannan malamai da suke kokarin haifar da fitina a tsakanin musulmi suka yi.
Ƙara sabon ra'ayi