Zanga-zangar Kin Saudiyya

Rahotannin da su ke fitowa daga kasar ta Saudiyya sun ce; An gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Riyadh a jiya juma'a domin yin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da s a gidajen kurkuku ba tare da an yi musu shari'a. A garin al-Qusaim da ke tsakiyar kasar ta Saudiyya matasa da dama sun gudanar da Zanga-zangar kamen da jami'an tsaro su ka yi wa mutane da dama a yankin saboda dalilai na siyasa, tare da bada taken da a sake su da gaggawa. A cikin shekaru biyu na bayan nan Saudiyya na fuskantar Zanga-zanga da gangami a cikin yankunanta daban-daban domin yin kira da a samar da sauyi na siyasa da kuma 'yanci.

Ƙara sabon ra'ayi