Asalin Larabawa da Mazhabobi - 6

Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 6
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Me Ye Matsayin Gullat
Barin in dan dawo baya kadan in dan nunawa ustaz Faragal wasu `yan ruwayoyi daga cikin makamantan su da daruruwan ire- iren sa, wadanda suke yin nuni a bisa inda gullatanci ya ke domin yasan cewa gullatanci yana wajen wasu ba Shi'a ba. Kuma ma bisa mafi munin tabbaci, a wajen Sunna akwai ninkin wanda ya ke wajen Shi'a, bari in fara masa tun daga kan halifanci in bi da shi bisa jeri daya bayan daya.
A- Sheda na farko: Shekh Ibrahim Al’abidi Almaliki (bamalike) ya ambata a cikin littafinsa Umddatut Tahkiki Fi Basha’iri Alis Siddik, ya ce an ruwaito cewa wata rana Manzo (s.a.w) ya ce da A’isha lalle Allah yayin da ya halicci rana ya halicce ta daga lu’ulu fari gwagwadon girman duniya sau dari da arba’in- tare da la’akari da cewa girman rana kamar yadda masana ilimin falaki suke cewa miliyan ne da dubu dari uku a gajeren takdiri, -kuma ya sanya ta a bisa sauri, kuma ya sanya saurin bisa igiya dari takwas da sittin kuma ya sanya sarkar yakutu ja a kowace igiya, sannan ya umarci mala’iku sittin daga cikin makisanta da su ja ta da wannan wadannan sarkokin da karfin su wanda Allah ya kebance su da shi, kuma rana kamar falaki ta ke a wajen wannan saurin kuma ita rana tana yin zagaye a cikin koren daki kuma kyan ta yana dada bayyana ga mutanen da suke doron kasa, kuma kullun tana tsayawa a kan madaidaicin zare (haddul istiwa’a) a sama Ka’aba saboda ita ce centar duniya:- a bin la’akari: Madaidaicin zare ba a kan Ka’aba yake ba- sannan kuma tana cewa: Ya mala’ikun ubangiji na lalle ina jin kunyar Allah Madaukaki idan na isa zuwa daura da saman Ka’aba, wacce itace alkiblar musulmi, kuma in wace tasaman ta, su kuma mala’iku suna jan rana da dukkanin karfin su domin ta tsallake saman Ka’aba, sai taki jawuwa mala’ilkui su kasa jan ta sai Allah ya yi wa rana wahayi ta hanyar ilhama sai su yi shela: Yake rana mun hada ki da girman mutumin da sunansa yake a rubuce a fuskarki mai haske, ki koma daga inda kika taho, idan ta ji haka sai ta motsa da ikon Allah, sai A’isha ta ce:
Ya manzon Allah wane ne mutumin da sunansa yake rubuce a jikin ta?
Shi ne Abubakar Siddik, yake A’isha tun kafin Allah ya hallici duniya ya sani da iliminsa maras farko cewa zai halicci iska kuma zai halicci wannan saman a kan iska kuma zai halicci kogi daga ruwa kuma zai halicci abin hawa mai sauri a kan ta saboda ranar da take haske duniya kuma yasan cewa rana zata yi wa mala’iku taurinn kai ya yinda ta isa zuwa tsakiyar duniya, kuma lalle Allah ya kaddara ya halicci wani Annabi a karshen zamani abin fifitawa a kan sauran annabawa kuma shi ne mijin ki, ya ke A’isha ko da makiya sun ki, sannan sai ya zana sunan wazirinsa ina nufin Abubakar Siddik abin zabi, don haka idan mala’iku suka roke ta da sunansa sai ta gushe ta koma daga inda ta fito da ikon Allah haka ma idan mai sabo daga cikin al’umma ta ya wuce ta wutar jahannama, sai ta yi kokarin ta kawowa mumini hari, saboda son Allah da yake cikin zuciyar sa da kuma sunansa da yake rubuce a harshen sa sai ta juya baya tana mai gudu.
B- Dalili na biyu: Muhammad dan Abdullahi Aljardani ya ambata a ciki littafinsa, misbahul zalama: An ruwaito daga dan Abbas cewa jibril ya zo sai ya ce ya Muhammad ka karanta gaisuwa zuwa Umar kuma ka gaya masa cewa yardar sa daukaka ce, kuma fushin sa hakuri ne, kuma lalle Musulumci zai yi kuku bayan mutuwar ka saboda mutuwar Umar, sai Manzo ya ce ya Jibril bani labnari abisa falalar Umar da kuma mmatsayin da yake da shi a wajen Allah madaukaki, sai ya ce: Ya Muhammad da zan zauna da kai gwargwadon yadda Annabi Nuhu ya rayu ba zan iya lissafa maka labarin falalar Umar da matsayin da ya ke da shi a wajen Allah ba,
C- Dalili na uku: Imam Ahmad dan Hambali ya fadi a cikin musnadinsa da isnadinsa daga A’isha, cewa lalle Abubakar ya nemi izinin shiga wajen Manzo Allah (s.a.w) a lokacin da ya kasance a kishingide a cikin dakin sa cinyoyin sa a waje tare da kwaurikan sa, sai Abubakar ya nemi izinin shigowa sai ya yi masa izini sai suka yi hira sai Umar ya nemi izini sai ya yi masa izini ya shigo Manzo yana yadda yake bai canja ba, sannan sai Usman ya nemi izini sai Manzo ya daidai ta zaman sa sannan sai ya daidata tufafin sa sai A’isha ta ce: Abubakar ya shigo ba ka ji kunyar sa ba kuma ba ka kula da shi ba, sannan Umar ya shigo ba ka ji kunyarsa ba, kuma ba ka kula da shi ba, sannan da Usman ya shigo sai ka zauna sannan kuma ka daidaita zamanka. Sai Manzo (s.a.w) ya ce ashe ba na ji kunyar mutumin da mala’iku suke jin kunyar sa ba.
Wadannan su ne misalsali guda uku daga cikin gomomin irin su wadanda su kan su halifofin ba su yarda da ita ba, suna da muwafakat da cewa da darajojin da suka ishe su, su ba su bukatuwar yayime-yayime da haniniyar sakarci, kamar yadda tarihin Musulumci, shi yafi girma fiye da mu yarda mu zama abin da za a rika yin amfani da shi wajen cenja tarihi. Cikin abin da tahirnmu ya tattaro akwai abubuwan da suka isar wajen tabbatar da daukakar Danadamtaka, domin in bi bayan wadannan ruwayoyin, barin in cito maka wadannan ruwayoyin, da wasu misalsalin na daban wadanda rigimar mazhabci ta haifar da su, kuma ba tare da ya kula ba sai gashi ya zubar da kimar mazhabar baki daya. Inbul jauziyya yana fadi a cikin littaifnn sa Yakut: Abuhanifa a lokacin rayuwarsa ya san Annabi Hidhir kuma lokacin da ya mutu Hidhir ya yi bakin cikin rasa shi, kuma ya yi munajati da Ubangijinsa ya ce da shi, ya Ubangiji na idan har ina da matsayi a wajen ka, ka yi wa Abuhanifa izini ya ilimantar dani alhali yana cikin kabari, kamar yadda yakance yana yi da har sai nasan shari’ar Muhammad a kammale, sai Allah madaukaki ya raya shi sannan ya nemi ilimi a wajen sa har tsawon shekara ishirin da biyar….h.i.k. to wa ke nan ya tafi a kan raja’a ya ku Musulmai?.
Kuma Ibnul Jauziyya ya na cewa a cikin littafin, Manakib daga Ali dan Isama’il, ya ce; na ga tashin alkiyama, sai mutane suka zo wajen wata gada, ba a bari koya ya wuce sai ya zo da sutamfin (sheda ko alama) daga wani mutum da yake zaune a gefe yana yi wa muytane stamfi, yana ba su sai na ce waye wancen sai aka ce Ahmad dan Hambali ne.
Ya isar maka ka karanta ruwaya a kan Imam Malik da Imam Shafi’i da ma da yawa daga cikin fakihai, da Imamai na daga abin da son rai ya sako, sannan kuma aka sa a gaban mai karatu, na daga abin da yake cutar da kwadayin sa kuma ya ke kuntata yadda yake ihsasi (ji). Sannan kuma bayan haka me za a kira misalin irin wannan shin guluyyi ne ko kuma ba wata tambaya da za a fuskantar zuwa ga Ustaz Faragal! da sannau zan bawa Faragal wani misali guda daya kawai, mai tafsirin ruhul bayan yana cewa:
A yayin da yazo kan fassarar (A wannan ranar guda takwas ne suke rike da al’arshin ubangijin ka) lalle rabin wadanda Allah ya fadi a cikin wannan ayar su ne Abuhanifa da Malik da Shafi’I da Ahmad dan Hanbal??!!.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi