Asalin Larabawa da Mazhabobi - 5

Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 5
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

Ra’ayin Sashin Masu Bincike
Daga wannan ne shehul Mufid ya ke cewa: Gullawa suna daga cikin masu bayyana Musulumci kuma su ne wadanda suka jingina wa shugaban muminai Ali dan Abi Dalib da zuriyar sa allantaka da annabta kuma suka siffanta su da matsayin da ya wuce iyaka a cikin addini kuma suka wuce iyaka don haka su kafirai ne".
Ba ina son in cika ku da nassosi a kan kubutar Shi'a daga gullanci ba ne, amma wane matsayi ne ya fi zama a sarari fiye da wadannan matakan da na ambata. A she bai isar wa munini ya zamo ya yi imani da Allah da kuma Manzonsa ya kuma yi riko da koyarwar Musulumci a cikin ayyukansa ba, har sai ya kai ga yin guluwwi a cikin wata akida ko kuma ga wani mutum, sai dai in wanda Allah ya shafe masa basira ba ne shi. Kuma saboda yadda matsayin Shi'a ya ke a sarari a kan gullawa ne ya sa mutanen da suka san abin da suke, su ke bayyana barrantar su gada gare su, daga cikin masu shelanta hakan akwai mawallafan Da’iratu Ma’ariful Islamiyya, ya zo a cikin Da’iratu Ma’arif cewa:
Zaidiyya da imamiyya su ne wadanda su ka yi riko da mazhabar tsakiya kuma suna yakar hululiyyin yaka mai tsanani kuma hululiyyun ba ma sa su a cikin Shi'a kamar yadda ya gabata kuma suna ganin su a matsayin gullawa wadanda suke bata mazhabar ,kai suna ma ganin su a matsayin wadanda suka fita daga cikin Musulumci.
Kuma Dakta Ahmad Mahmud a cikin Nazariyatul Imamiyya a yayin da ya bijiro a kan Mazhabar Babiya da Baha’iyya: A cikin bayabiyya akwai ra’ayoyi wadanda suka wuce iyaka wadanda suka sa ta zama mazahabar da ta ke wajen Musulumci dari bisa dari, kuma malaman Azhar a Misra da malaman Shi'a a Iraki da Iran sun hadu a kan kafircin Babiyya da Baha’iyya, sannan aka rife wajen haduwar Baha’iyya a Misra . Kuma Dakta Ahmad Amin ya bijiro da magana a kan motsin gullkawa, sannan ya ce: Lalle wasu daidaikun wawaye ne (basidai) wadanda suke allantar da Ali kuma lalle Shi'a sun barranta daga gare su, kuma a wajen su bai halattaba a yi musu salla. Wadannan kananan misalsali ne a kan lamarin gullanci da kuma gullawa da na ajiyye su a gaban wadanda suka saba da jifan Shi'a da wace iyaka, ba kuma ina kore yiwuwar sunan ya hau kan su ba da nufin cewa sun jingina kansu da mutanen da suke fifita Ali ko suke kiran kansu da Shi'a da yanayi na wuce iya ka ba, wadanda suka riga suka jingina masa wasu maganganu da ra’ayoyi da suke tattare daukaka, alhali tuni an yi wadannan mutanen an gama dasu da ra’ayoyin su baki daya, babu sauran irin su a yanzu sai a cikin litattafai, kuma yana daga cikin irin wannan abin da Bagdadi ya ruwaito, a cikin A lfirak bainal firak, a inda yake cewa: Imamaiya su na daga cikin Rafidhawa kuma sun kasu zuwa kaso goma sha biyar, sun e: Kamaliyya da Muhammadiyya da Bakiriyya da Nawusiyya da Shamdiya da Imariyya da Isma’iliyya da Mubarikiyya da Musawiyya da Kadiyya da Isna ashariyya da Hishamiyya da Zarariyya da Yunusiyya da kuma Shaidaniyya. Domin mukamala maganar Bagdadi sai mu ce: Imamiyya su ne Isna ashariyya kuma sune jamhurun Shi'a a yau kama babu samuwa ga wasun su a yau in banda Zaidiyya da kuma Isma’iliyya a wannan zamanin. Sannan Isna ashariyyan wadanda su ne bugiren binciken mu sun fifice wasun su da akidun su, kuma bai halatta a jingina musu ra’ayiyin wasun su ba, domin su ne kawai wadamda suna da kuma wasu abubuwa suka hada su da su, wani abu kuma shi ne wadanda Bagdadi ya ambata ta yiwu ya zama kowace firka bai yan wasu mutane yan kadan take da su ba wadanda su suke misalta ta. Wannan irin kwashi kwaraf da kuma sakaci wajen tantancewa mun dade muna ganin irin sa a cikin litattafan mazhabobi, na su Ibn Dahir da wasun sa, dauki misalign abin da Ibn Dahir ya ke fadi a cikin littafinsa Alfirak bainal firak an karbo daga Jabir dan Yazidul Ja’afi yana cewa:
Jabir dan Yazidul Ja’afi yana daga cikin Muhammadiyya, su ne sahabban Muhammad dan Abdullahi dan Hasan, sana sauraren bayyanar sa, kuma ya kasance yana tabbatar da (raj’a) (dawowa) dunuya bayan mutuwa kafin ranar alkiuyama.
Jabir baya daga cikin mabiyan Muhammad dan Abdullahi dan Hasan ba kuma bai kasance wanda ya tafi a kan raj’ar matattu kai tsaye ba, kadai abin da ya ke fadi shi ne raj’ar sashin wasu daga cikin Imaman Ahlul-baiti saboda ruwayoyin da ya ji, ba wani abu sama da hakan. To ka ga yadda tahkiki ya ke a wajen irin su Dahir marubuta kai ka ce lamarin akida abu ne mai sauki kamar haka, ta yadda zai rika jinginawa mutane abin da ba su fadi ba kuma ya sa su a cikin wasu mutanen da ba sa daga cikin su.
Bari in dawo kan lamarin gullat, tuni matsayin Shi'a a kan gullat ya riga ya bayyana ga mai karatu a sarai, amma tare da haka sai ka samu mai bincike kamar Zubaidi ma’abocin littafin Tajul arus, yana yin ta’arifin Imamaiyya a cikin littafin na sa da cewa: Imamiyya wasu bangare ne na gullatun Shi'a , sai ga Dakta Mahmud Hilmi a ciin littafinsa Tadwirul Mujtama’il Islamil Arabi yana cewa: An kira su da Shi'a saboda sun bi Ali kuma sun fifita shi a kan sauran sahabban Manzo (s.a.w) kuma yan Shi'a sun kafa dalilai da nasossi na Kur’ani wadanda suka fassara su bisa nazarin su kuma wasu daga cikin Shi'a sun wace iyaka a wajen tabbatar da cancantar Ali dan Abidalib kuma suka rubanya masa da sashin suffofin na tsarkaka da kuma allantaka , lalle zaka yi mamakin furucin wadannan marubutan, musamman sashin marubutan misra, domin su suna suranta Shi'a kamar wasu mutane ne da ba su da imani da addini, suna wasa da nassosi ba tare da mai bin diddigi daga Allah Madaukaki ba kuma ba tare da wasu ka’idoji na ilimi ba, na rantse da Allah su suka fi kusa da wannan, in ba haka ba meye dalili a kan abin da Mahmud Hilmi ya fada? Alhali ga littafain Shi'a nan a gaban sa, ya nuna mana wajen da Shi'a suka jingina hululiyya da allantaka ga Ali, kuma tabbas yanke ba zai sami wannan ba, sun kasance suna fitarda abin da suke fadi ba tare da jin cewa akwai wani nauyi a kan su ba: "Kalma ta girmama wacce take fita daga bakunan su, ba komai suke fadi ba sai karaya" kahafi/5. A bin da yafi wannan zama bala’i shi ne samun wadanda suke tasirantuwa da wadannan marubutan daga na kusa da su ko wanda ya ke nesa da su alhali kama shi dan Shi'a ne kuma kaga shi ma yana yin rubutu da irin wannan salon, Allah ya jikan wanda yake cewa:
Zaluncin makusanta ya fi tsananin daci*
*Ga mutum fiye da sara da takobin hindu
Dakta Kamil Musdafi yana fadi a cikin littafinsa: Bisa wannan ne zai a bayyane cewa lalle gullawa ko da kuwa sun kasance wadanda Shi’a da Imamansu, suke kin su, to tuni dai sun riga sun assasa akidun Shi'a na asali tun farkon farawa, kuma isma da ilimi na daga Allah sun zama tabbatattun rubutattun akidun Shi'a daga baya sai dai bisa sassauka yanayi, wannan ke nan, sai ta bayyana a gare ni cewa Dakta Kamil ya Dauki wannan ne daga Dakta Tasrihi dan Naufi, kuma shi dan daya ne daga cikin sahabban mukhtar, bari kuma in kara tuna mana da cewa lalle Shi'a sun riki akidun su ne daga Kur'ani da Sunna kamar yadda muka kafa dalili a kan sa a cen baya. Sannan da zamu kaddara cewa dan Naufi din nan ko kuma mukhtar sun riga sun fadi wata magana wacce ta shafe su, to mene ne lefin Shi'a? Kuma shi dan Naufal din shi waye har da zai taka rawa da sunan Shi'a? Idan har Dakta Kamil ya yi i’itirafi da cewa Shi'a da Imaman su ba sa son gullawa to ta yaya kuma Shi'a zasu karba daga gare su alhali saboda wuce iyaka su ka yi fushi da su? Idan kuma har wadannan akidun sun kasance daga cikin gullanci kuma shi baya yin sa a she wannan bai zama zunzurutu tanakudhi (maganganu guda biyu su ci karo da juna) ba?. Idan har mun kasance muna yi wa Hilmi da makamancin sa uzuri saboda ba su rike mu masdaran mu ba, to mene ne uzurin irin su Kamil Sha’abi wanda ya ke daga cikin Shi'a kuma yana rayuwa tare da masdarorin su, ba wannan ne kadai abin da Dakta Kamil ya fitar ba wanda ba mu yarda da shi ba, balle ma yana da wasu abubuwan da ya rubuta masu yawa irin su daga ciki akwai: Yayin da ya bijiro da masdarori a kan lamarin raj’a a wajen Shi'a ya fadi cewa asalin ta wasu kalmomi ne na Imam Ali (a.s) wadanada suka zo a cikin nahjul balaga yayin da Allah ya bashi nasara a kan mutanen jamal (rakumi) (a yakin jamal) a lokacin da sashin sahabban sa suka ce da shi na so a ce lalle dan’uwan wane ya halarci mu domin ya ga yadda Allah ya baka nasara a kan makiyan ka, sai Imam Ali (a.s) ya ce shin zuciyar dan’uwan ka yana tare da mu? Sai ya ce na’am, sai ya ce ya halarce mu.
Ta yiwu ya zama Imam yana yin nuni ne zuwa ayar nan "Kada ku yi tsammanin cewa wadanda a ka kashe a cikin tafarkin Allah matattu ne, balle ma rayayyu ne a wajen ubangijin su ana azurta su"Ali imrana/169. Alhali labarin yana komawa ne zuwa aj’a tare da dukkanin abin da ke cikin ta na daga ma’ana mai zurfi, balle ma sauran labarin yana kutsawa zuwa wani fage mafi zurfin ma’ana da falsafar raja’a da kuma hikimar ta, domin Imam yana cewa:
Wasu mutane daga cikin tsatson wasu mazaje da mahaifar wasu mataye sun halarce mu a cikin rundunarmu wannan kuma da sannu zamani zai rayu da su kuma imani ya karfafa da su, daga wannan, ya bayyana cewa lalle Ali a nan ba kawai ya tabbatar da dawowar wadanda suke gabata ba ne a cikin wannan jihadin domin suma su tsinki nasu `ya`yan itaciyar, kai ya ma tabbatar da cewa hatta majahidai na nan gaba suma sun halarci wannan nasarar domin ya kara karfafar su a kan wannan kuma ya hada zukatan su, kuma wadannan lamura ne wadanda da suke da kafa babba a cikin afladoniyya ta da da ta yanzu, wannan ne karshen maganar sa.
Bari in sanya wannan nassin a gaban mai karatu mai girma domin ya gani da kan sa, mene ne gwargwadon abin da yake na daidai daga cikin wadannan sakamakon wadanda Dakta ya fitar da kuma shaidun da ya jero da kuma fitar da ra'ayi irin na afladon din da ya ambata, sannan sai ya rufe maganar sa da abin da zai zo:
Na farko: Idan wannan nassin ya zo ne a kan raja’a to mene ne ma’anar cewa Imam Ali ne ya kirkiro akidar raja’a ba gullat ba kamar yadda Dakta kamila yake fadi.
Na biyu: Wannan nassin da dukkanin fahimta ta kusa- kusa bako ne kamar yadda Dakta yake fadi kuma ko kadan bai da sila da ma’anar da ya ambata, ko ma dai mene ne lalle wannan nassin abin da yake nunawa kuma yake nufi shi ne ruwayar nan da ta ke cewa: "Wanda ya so wasu mautane za a tashe shi a cikin su kuma zai yi tarayya da su a cikin ayyuakan su" don haka ne ma Imam Ali ya tambayi mutumin game da abin da zuciyar dau’uwan na sa take so, shin yana tare da amirnl muminina ne da sahabban sa? Sai ya amsa masa da na’am, sai ya ce lalle ya halarce mu. Ai ya yi tarayya da mu da shu’urin sa, sannan Imam ya ce da shi: Lalle baki dayan wadanda zamani zai rayu da su, wadanda mu a ra’ayin mu da sannu zasu yi musharaka da mu bayan haka a cikin samun lada da kuma farin cikin samun nasara, kuma misalsali da kwatamkwacin irin wadannan kalamai sun yawaita a cikin maganganun Imam sa, daga cikin wannan akwai abin da marubuta tarihin duffi suka ruwaito a in da suke cewa: Jabin bin Abdullahil Ansari ya ziyarci kabarin Imam Husain bayan kashe shi sai ya ce a cikin ziyara tasa: "Na shaida cewa mun yi tarayya da ku a cikin abin da kuke a kan sa" sai Rafi’atal A’amash ya ce: An yanke kawunan mutanen kuma sun yi jihadi har sai da aka ka she su, ta yaya muka zama mun yi tarayya da su a abin da suke cikin sa?" sai Jabir ya ce da shi "Lalle niyya ta da niyyar sahabbai na tana kan abin da Husain ya shude a kan sa da shi da sahabban sa" dukka nin ma’abota litattafan jiyarar Imam Husain sun ambaci wannan baki dayan su, wannan itace ma’anar maganar Imam Ali (a.s) ba kamar yadda Dakta ya tafi a kai ba.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi