Asalin Larabawa da Mazhabobi - 4

Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 4
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id

5- Lamari Na Biyar:
Ustaz Faragal yana ganin cewa ruwaoyin Shi'a suna tatter da yanayin da ya dace da samuwar gullawa, a nan ina so in yi wa Ustaz Fragal sharhi a kan matsayin Shi'a daga gullanci da kuma gullawa: Dabrasi ya yi ta’arifin gullanci a cikin tafsirin sa a yayin da yake yin sharhin aya ta 77/ Ma’ida: "Ka ce ya ku ma’abota littafi kada ku yi shisshigi a cikin addinin ku ba bisa gaskiya ba" da cewa shi ne abin da yake kishiyantar takaitawa, kuma shi a ke kira wuce iyaka, sai ya ce ai "Ana nufin kada ku wuce iyakar da Allah ya ajiye ku a kan ta har ku zama kun wuce iyaka kuma kishiyar wannan shi ne takaitawa, takaitawa kuma ita ce fita daga iyaka zuwa tauyewa, kuma ka ga yin sama da abin da ya kamata da kuma yin kasa da shi dukkanin su barna ne, kuma addinin mu wanda Allah ya umarce mu da shi yana tsakanin wuce iyaka da kuma takaitawa wannan ake kira tattali ko tsakaitawa- .
Amma dalilan da ke jawo wuce iyaka mafi bayyanar su kuma mafiya mihimmanci daga cikin su a mahangar mu dalilai ne duga hudu kamar haka:
A- Mafara (Sababi) ta farko:
Idam mutum ya wuce iyaka a kan wani mutum ko wani tunani, domin ya riki wannan a matsayin dallilin da yasa shi ya riki wannan tunanin ko kuma muutmin, domin yana so ya yi riko da abin da zai zame masa kariya a gaban mutane kuma abinada zai zama gamsarwa a gare shi, ya kuma ta yin kokarin zuzzuta wannan tunanin, sosan gaske bisa akidantuwarsa da wannan mutumin, domin su mabiya a ko da yaushe suna yin kokarin daukaka matsayin wanda suke yin koyi da shi zuwa wani matsayi da ya wuce na dabi’a, kuma wannan ma’anar samammiya ce a fagen addini da na siyasa, an siffanta Sarki Hubar da cewa mutum ne da yake fassara iradar Allah da kuma ta mutane, ta yadda ya bashi iko mudlaki a wajen yin tasarrufi kuma bai ba wa mutane damar cire shi ba, shi ya sa ma ake ganin iradar sa a matsayin irada ce daga Allah madaukaki.
Malaman falsafa na Yunan sun tafi a kan wannan ra’ayin bisa la’akari da tasirin da suka tabbatarwa sarki na daga siffofi, wanda ya fisu tsananna tawa a cikin wannan shi ne, Haijal malamin Markis, a wajen sa sarki shi ne ma’abocin sarauta mudlaka kuma yana da cikakkiyar dama a kan maslahohin daidaikun mutane kuma mutumtakar sa na misalta zati na karshe wato shi ne dunkulen tarayyar al’mma a cikin mutum guda, shi ne shi ne.. kuma tuni afladul ya rigayi wadannan baki daya a yayin da ya bawa sarki tsarkakakkun matsayoyi, haka ma Farabi a ya yin da suranta sarkin gari da cewa a hade ya ke da hankali mai tasiri ta yadda yake kasancewa kusa da Allah Madaukaki .
Lalle wadannan matakan matakai ne bawa kai hanzari a kan yin riko da wani tunani bisa wani yanayi ko kuma da wani yanayin na daban da zai iya kaiwa da a yi wani ko a yi riko da wani tunani na musamman.
B- Abu na Biyu da ke sa a yi Shisshigi:
Sakamakon Takura: Akan azabtar da wasu saboda a kidunsu, ta yiwu a aibata shi ko a zage shi ko a yi masa izgili ko sai wannan ya sa shi ya wuce iyaka saboda sakamakon dabi’ar kome ta turi in tura, saboda haka ne ma muka ga Kur'ani mai girma irin wadannan wajajen ya yi riko da dabi’a ta rai da zuciyar dan Adam tare da ba wa wannan lamarin cikakkiyar kulawa a yayin da madaukaki yake cewa: "Kada ku zagi wadanda su ke bautawa ba Allah ba, sai su zagi Allah saboda gaba bisa rashin sani"108/ Na’am. Kuma wannan masa’alar tana da tabbatattun gwaje- gwaje a tsawon tarihi a wurare da dama daga wannan ne ma Donaldus ya tafi a kan cewa: Lalle ra’ayin isma sakamako na takurawar da halifofin da suka yi kwacen mulki suka haifar da shi, kamar yadda yake tsammani.
Kai bangon takurawa ta taka rawa mai girma a tarihin Musulmai da akidunsu kuma ya zama wajibi a yi riko da wannan sosai a yayin da za a yi kokarin daidaita matakai da kuma saita nassosi a wurare da dama.

C- Mafara Ta Uku:
Shin gullatancin da yake faruwa sakamakon tsarkaka da kuma barranta da kyautata zato ga wasu sai aka jingina shi zuwa abin da suka ruwaito ba tare da tantance wa ba musamman ma ga wadanda suke yi wa Musulumci dasisa saboda wannan dalilin ko wancan kuma suka yi kokarin lullube hakikanin su sai suka yi hamasa hamasar da ke iya haifar da shubuha ga wasu mutane ko ga tunani, wannan mafarar magana a kanta na da tsawon gaske. Da yawa daga cikin masu yin dasisa sun taka rawa ta sarari domin su sajjala tunanin da kuma matakai wadanda su ke kaiwa ga wuce iyaka har ta kai ga suka bata wa Musulmai da yawa akidun su saboda manufofi mabambanta wadanda su ne su ka zuga su, kuma lalle kowace mazhaba daga cikin mazhabobi suna da wani kaso na wadannan ko kuma kaga sun karanta saboda yanayin mazhabar ita a kan kan ta kuma ta yiwu wannan ma’anar (lamarin) ta shude da mu a nan gaba dalla-dalla.
A. Dalili Na Hudu:
Ta yiwu a jarrabi wasunsu da shubuhar da za ta kai su zuwa ga sakamako kuskurarriyar fahimta ko kuma yin gamemmen hukuncin da ba a warware shi ba a ilimance kamar idan ya ga wani ra'ayi na wani mutum daga cikin wata mazhaba sai ra’ayin sa ya game dukkanin yan mazhabar gaba daya, kuma ta yiwu wasu jama’a su tafi a kan wani ra'ayi sannan kuma jama’ar su kare, sai kuma ka ga wani ya zo ya dorawa wasu ra’ayin, kuma ta yiwu fitar da wani sakamako a kan wani ra'ayi ya zama ya lazimci tafiya a kan wani ra'ayi wanda shi kan sa mai wannan ra’ayin bai fahimci hakan ba, kuma ta yiwu ya zama ya faru ne sakamakon yin kuskure a wajen dabbaka wata ka’ida gammamiya a kan wasu sasanni da makamancin wannan, babu makawa da a rika bi sannu- sannu kuma rika kiyayewa da gaske ta yayin rubutu a kan wasu matane ko kuma mazhaba, babu makawa da a riki ra’ayin ta daga masdaran ta wadanda aka yarda da su kuma aka sallama musu, idan sashin Shi'a a wani lokaci suka kasance sun wuce iyaka akan Imam Ali saboda ya cizge kofar khaibar, ba dukkanin Shi'a ne suke hake ba, idan har wani mutum ya ce da Imam Ali a lokacin da ya ke yin huduba sannan ya ce da shi kai ne! Wannan ba yana nufin dukkanin Shi'a haka su ke ba.

Matsayinmu A Kan Shisshigi Da Wuce Gona Da Iri
Bayan sharhin abubuwan da suka haifar da guluwwi, da kuma mihimmai daga cikin su, zamu iya cewa lalle Shi'a saboda biyayyar su ga Imaman su sun tsaya a matsaya ta tsaftacciya daga gullanci da gullawa sai su ka fito da su sarari kuma suka barranta daga gare su kuma suka yake su kuma suka zare takobi a gabansu, kuma su da wannan matsayin da su ke kai ba za su ketare matsayin amirul muminin (a.s) ba, a yayin da yake cewa "Mutum biyu sun hallaka a kai na mai yi min son da wuce iya ka da kuma mai ki da ya tsananta gaba". Imam Sadik ma a yayin matsayin sa, a yayin da yake cewa: "Mu ba kowa ba ne face sai bayin wanda ya yi halitta kuma ya zabe mu, na rantse da Allah ba muda hujja a kan Allah kuma wallahi ba mu da wata makubuta daga Allah, kuma lalle mu masu mutuwa ne kuma ababan tsayarwa ne kuma ababan tambaya ne, wanda ya so masu wuce iyaka (gullat ko gullawwa) ya ki mu, wanda kuma ya ki su hakika ya so mu, gullat kafirai ne, mufawwidha kuma mushirikai ne Allah ya la’anci gullat, ku saurara, su sun zamo nasara, sun zamo kadariyawa, su murji’awa ne kuma hururiyyawa".
Kuma Imamiyyawa ba sa gadar da gullat (ba su halatta aba su gado ba) kuma ga yadda nasiin maganganun su yake, ma’abocin hakki daga cikin musulmi yana yin gado tsakanin mabarnaci daga cikin su, da wanda yake mabarnaci haka ma tsakanin wanda yake kan gaskiya da kuma wanda yake mabarnaci, in banda gullat, Musulmai za su gada daga gare su su kuma ba za su gada daga Musulmai ba, kamar yadda imamiyyawa ba sa wanke gawar gullat kuma ba sa binne su, sannan kuma sun haramta a aura musu, da kuma ba su zakka, kuma zaka sami wadannan hukunce- hukuncen a ko ina a tsakaknin litattafan fikihun imamiyya a cikin babobin tsarki da zakka da gado, kuma lalle imamiyya ba sa sanya gullat a matsayin Musulmai:
Shahidai guda biyu na farko da na biyu suna fadi a cikin Lum’atul dimashkiyya¸ a cikin babin wakafi a yayin da yake yin ta’arifin musulmi: Musulmai su ne wadanda suke yin salla suna masu kallon al’kibla ai wanda ya akidantu da yin salla zuwa gare ta koda kuwa bai yi sallar ba ba tare da yana mai kore hakan ba, in ban da hawarijawa da gullat wadanda ba a sa su a cikin jerin Musulmai ko da kuwa sun yi salla suna masu kallon al’kibla saboda an yi hukunci aka kafirtar su, kuma masu bawa Allah kama da siffa (mushabbiha) ma ana sasu a cikin su, su da masu yi wa ko tabbatar wa Allah jiki, balle ma Imam Sadik yana ganin zama da gullat da kuma gasgata zancen da yake fadi na jawo mutun ya fita daga imani, kamar yadda Fadhal dan Ziyad ya ruwaito yana cewa: Baban Abdullah Assadik ya ce a yayin da aka ambaci sahabban Abil Khaddab: " Kada ku zauna tare da su kada ku ci tare da su kuma kada ku sha tare da su kuma kada ku yi hannu da su sannan kada ku gadar da su" kuma Imam Sadik ya ce wa Marazim –daya daga cikin sahabban sa "Ka gaya wa gullat ku tuba zuwa Allah domin ku fasikai ne mushirikai".

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center

Ƙara sabon ra'ayi