Asalin Larabawa da Mazhabobi - 2
Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 2
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Rufewa
A nan zan fuskanci ustaz Faragal da tambaya ita ce: Da a ce duk wadannan abubuwan da ka musanta su ga Shi'a kuma suka zama akwai su a wajen Ahlus-sunna, shin su ma Ahlus-sunnar zai yi musu nakadi ne ko kuwa. Da sannu wannan tanbayar za ta baka mamaki, kuma harka ce ta yaya kuwa ba zai yi musu nakadi ba, alhali maudu’in daya ne kuma babu bambanci tsakanin kasantuwar Sunna ne suka fadi ko kuma Shi'a. A nan kuma zan baka amsa da cewa ba zai yi musu nakadi ba idan har suka zamo ba Shi'a ba ne, kuma wannan ne abin da ya faru a aikace, domin sun fadi wadannan abubuwan wadanda ya yi wa Shi'a nakadi a kan su, kuma da sannu zan dora hannun ka akan maganganun su a bayanai masu zuwa:
1-Lamari na farko: Abin da ya yi wa Shi'a nakadi da shi na isma, kuma ba na bukatar in maimaita abin da ya gabata na riga na fade shi, wanda kuma maganganu da yawa daga cikin malaman Sunna tuni suka yi nuni a kan sa dangane da isma, duk da cewa ba dukakkaninsu ba ne, amma tare da hakan Yahya Faragal bai musa ta hanyar yin nakadi ba, tare da cewa shi Yahya Faragal ya fi wanin sa sassauci a cikin wannan babin, saboda wasunsa sun fi shi tsanani da kuma kai farmaki, dauki misalign Dakta Nabih Hijab mamalmin adabi- ina ma a ce yana da adabin- na Darul ulum a Kahira, wannan mutumin yana zagin Shi'a zagi mai ban mamaki kuma yana ganin akidar su a kan isma alama ce daga cikin alamomin bangaranci, saurari abin da yake cewa:
Lalle wannan akidar daga Farisawa ta sudado zuwa cikin shi’anci wadanda sun kasance suna rayuwa a kan tsarkake sarki don haka ne ma larabawa suke kiran ta akidar da aka samo daga mulkin kisra- alhali ban san wani mutum guda da ya daga cikin larabawa da ya fadin wannan ba a iya bincike na, ta yiwu mafi yawan Shi'a an kasance ana jifan su da wannan a sakamakon akidar su ta tsarkake Ali (a.s) daga kuskure har ta’addancin Banu Umayya na kwace halifanci ya zamo ya fito fili, wannan ke nan. Kuma a cikin yahudanci akwai da yawa daga cikin mazhabobin da suka yi naso zuwa Shi'a.
Ka ji irin wannan shelar da na baya suke ta nakaltowa daga magabatan su bisa wauta, kuma tuni mun riga mun warware maka wannan tsammace- tsammacen a cikin abin da ya gabata na batun bafarisen shi’anci, sai dai abin da nake so in yi tambaya kan sa shi ne mene ne kuskure a cikin a cikin ayyukan Imam Ali (a.s) a mahangar Nabih Hijab, shin yakin da ya yi saboda kare tushen bubuwan da suke na dole, al’amarin da yya kai ga rashin samun tabbatacen yanayi na zaman lafiya, a daidai lokacin da yanayin Banu Umayya bai samu tabbatuwa ba sai a bisa cire wuyayen, koma dai meye, kuskurarwar Nabih Hijab ga Ali ba zai cutar da shi ba, bayan tuni Manzo (s.a.w) ya riga ya fadi cewa: Gaskiya tana tare da Ali kuma Ali yana tare da gaskiya. Kuma yana daga cikin abin da yake dabi’a ne a samu Ali tare da wadanda suke tare da shi da kuma Nabih Hijab da shi da wadanda suke tare da shi a daya bangaren.
2-Lamari na biyu: Abin da Faragal ya musanta wa Shi'a shi ne kasancewar Manzo (s.a.w) da ahlin gidansa daga haske daya suka fito, ban sani ba miye abin mamaki bayan Shi'a sun tabbatar da wannan daga masdarori ingantattu, shin ko dan wannan bai yi daidai da wasu san rai da suke cikin zukatan da ba sa bin Ahlul-baiti ba, ko kuwa? Sannan don me dan an sami irin wannan a wajen Ahlus-sunna ba ya zama abin mamaki, ga Zahabi ya ruwaito wani hadisi a cikin mizanil I’itidal, ta hanyar Abuhuraira daga Manzo (s.a.w) yana cewa: "Allah ya halicce ni da haske kuma ya halicci Abubakar da haske na kuma ya halicci Umar da hasken Abubakar kuma ya halicci Usman da hasken Umar, kuma Umar shi ne fitilar `yan aljanna , ban sani ba don me haske ya zo har kan Usman sannan ya ki karasawa kan Ali tare da cewa alal akalla shi ne halifa na hudu! Allah ne ya san girman lamarin ka ya Ali dan Abi Dalib!, ban sani ba mai Ustaz Faragal zai ce a kan wannan shin wannan gullanci ne ko kuwa?!, Ku zo mana da fatawa Allah ya gafarta malam, wannan ke nan. Tare da cewa dabi’a ne ya zama tsakanin mutum da ahlinsa akwai kadaitaka ta tsatso, alhali aalayen Muhammad (a.s) daidai suke da Kur'ani kuma taska ko kundin kuma ma’adanan ilimin Annabi ne su, to don me Ustaz Fafagal yake musanta musu abin da ba ya musanta wa wasunsu,
3-Lamari na uku: Abin da Ustaz Faragal ya musanta shi ne kasancewar ilimin Ahlul-baiti da shari’a da ilimomin Kur'ani da ilimomin Sunna madaukakiya kuma su zamo su ne masu bada hadisai, a nan za a iya cewa , lalle ilimin Ahlul-baiti ko da ya zama ta hanya ce ta al’ada kamar koyon ilimi ko zuwa makaranta, ko kuma ya zama ta hanyar ilhama da kuma cewa ana zantar da su hadisi ne, amma al’amari na daya, tabbatacce ne domin sun taso ne a gidan Muhammad (s.a.w) kuma an tarbiyantar da su a dakin sa sannan kuma sun karbi ilimomi daga wannan gidan kuma wannan lamari ne da babu wata kura a cikin ta, amma samun ilimi ta daya hanyar wato ta hanyar ilhama da kuma zantarwa kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni a kai. Musulmai baki dayan su sun tabbatar da wannan kuma da sannu zan ambaci wasu daga nassosinsu a cikin yiwuwar irin wannan ilimin:
Alusi ya na cewa a cikin tafsirin Ruhil ma’ani a yayin tafsirin ayar 65 daga surar Nahli: Shi ne fadinsa madaukaki: "Ka gaya musu ba wanda ya san abin da ke cikin sammai da kassai sai Allah" sai ya biyo bayan ta da cewa: Ta yiwu gaskiya shi ne a ce lalle ilimin gaibi da aka kore wa waninsa mai girma da buwaya shi ne wanda ya zamo da kan sa ma’ana ba da wasida ba wajen tabbatar da shi a gare shi, kuma abin da ya ke aukuwa ga kebantattun mutane baya daga cikin irin wannan da wani abu, kadai yana daga cikin wanda ya zo daga gare shi mahalicci mai girma da buwaya, yana mai kwararo baiwarsa gare su daga wata fuska daga fuskoki, ba za a ce sun san gaibu ba ta wannan ma’anar, domin lalle wannan kafircewa ne, abin da za a iya cewa anan shi ne sun bayyana ko sun yi tsankaye a kan gaibi .
Kuma abin da Alusi ya fadi, shi ne ainihin abin da ya zo daga Imaman Ahlul-baiti: Imam Ridha (a.s) na takwas daga cikin jerin Imamai yana cewa: "Yana yalwata mana ilimi sai mu sani kuma yana rike shi daga garemu sai mu zama ba mu sani ba" wannan ma’anar ita ce ainihin abin da wannan ayar take nufi: "Masanin gaibi baya bayyanar da gaibin sa ga wani sai dai wanda ya yardarwa na daga Manzo" aya ta 27/suratul Jinni. Dangane da sharhin wannan ayar ne Imam Ridha (a.s) yake cewa da Amru dan Hidab a lokacin da ya tambaye shi a kan ilimin Imamai, sai ya ce "Manzo Allah (s.a.w) shi ne yardajje a wajen Allah kuma mu ne magadan wannan Manzon wanda Allah ya tsinkayar da shi gaibin sa sai ya sanar da mu abin da ya kasance da abin da zai kasance har zuwa ranar ta shin alkiyama " a karkashin wannan ma’anar ne mafassarin nan Banaishabure ya ke cewa: Kore karama daga waliyai yana faruwa ne imma dai saboda Allah bai cencenci ya zama ahlin wannan ba, ko kuma saboda shi muminin ba ahlin wannan ba ne, kuma dukkanin wadannan korarru ne, domin dacen mumini da sanin sa, yana daga cikin mafi girman baiwar sa madaukaki ga bawan sa, idan har mai kwararowar bai yi rowar bada mafi girma da daukaka ba, hakan yana kasancewa ne saboda ba ya yin rowar bada abin da yake kasa de wannan.
Imam Sadik ya ba da haske a kan sashin ilimomin da suka ciro daga cikin Kur’anita hanya ta dabi’a, wannan ya faru ne a yayin da sashin sahabbabn sa suka tambaye shi, sai Imam Sadik ya ce: "Lalle na san abin da ke cikin sammai da kassai kuma na san abin da ke cikin aljanna da wuta kuma na san abin da ya kasance da abin da zai kasance" yayin da mai tambayar ya yi mamakin maganar sa sai Imam ya ce : "Na san wannan ne daga littafin Allah mai girma da daukaka wanda yake cewa: "Mun saukar maka da littafi yana mai bayyanawa ga komai domin shiryarwa da rahama da kuma bushara ga muninai" 89/ daga surar Nahal. Kuma lalle an ruwaito daga gare shi da kuma nazariyyar yiwuwar Ahlul-baiti su sha ililmi dan kadan ta mahanga faffada .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 2
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Rufewa
A nan zan fuskanci ustaz Faragal da tambaya ita ce: Da a ce duk wadannan abubuwan da ka musanta su ga Shi'a kuma suka zama akwai su a wajen Ahlus-sunna, shin su ma Ahlus-sunnar zai yi musu nakadi ne ko kuwa. Da sannu wannan tanbayar za ta baka mamaki, kuma harka ce ta yaya kuwa ba zai yi musu nakadi ba, alhali maudu’in daya ne kuma babu bambanci tsakanin kasantuwar Sunna ne suka fadi ko kuma Shi'a. A nan kuma zan baka amsa da cewa ba zai yi musu nakadi ba idan har suka zamo ba Shi'a ba ne, kuma wannan ne abin da ya faru a aikace, domin sun fadi wadannan abubuwan wadanda ya yi wa Shi'a nakadi a kan su, kuma da sannu zan dora hannun ka akan maganganun su a bayanai masu zuwa:
1- Lamari na farko: Abin da ya yi wa Shi'a nakadi da shi na isma, kuma ba na bukatar in maimaita abin da ya gabata na riga na fade shi, wanda kuma maganganu da yawa daga cikin malaman Sunna tuni suka yi nuni a kan sa dangane da isma, duk da cewa ba dukakkaninsu ba ne, amma tare da hakan Yahya Faragal bai musa ta hanyar yin nakadi ba, tare da cewa shi Yahya Faragal ya fi wanin sa sassauci a cikin wannan babin, saboda wasunsa sun fi shi tsanani da kuma kai farmaki, dauki misalign Dakta Nabih Hijab mamalmin adabi- ina ma a ce yana da adabin- na Darul ulum a Kahira, wannan mutumin yana zagin Shi'a zagi mai ban mamaki kuma yana ganin akidar su a kan isma alama ce daga cikin alamomin bangaranci, saurari abin da yake cewa:
Lalle wannan akidar daga Farisawa ta sudado zuwa cikin shi’anci wadanda sun kasance suna rayuwa a kan tsarkake sarki don haka ne ma larabawa suke kiran ta akidar da aka samo daga mulkin kisra- alhali ban san wani mutum guda da ya daga cikin larabawa da ya fadin wannan ba a iya bincike na, ta yiwu mafi yawan Shi'a an kasance ana jifan su da wannan a sakamakon akidar su ta tsarkake Ali (a.s) daga kuskure har ta’addancin Banu Umayya na kwace halifanci ya zamo ya fito fili, wannan ke nan. Kuma a cikin yahudanci akwai da yawa daga cikin mazhabobin da suka yi naso zuwa Shi'a.
Ka ji irin wannan shelar da na baya suke ta nakaltowa daga magabatan su bisa wauta, kuma tuni mun riga mun warware maka wannan tsammace- tsammacen a cikin abin da ya gabata na batun bafarisen shi’anci, sai dai abin da nake so in yi tambaya kan sa shi ne mene ne kuskure a cikin a cikin ayyukan Imam Ali (a.s) a mahangar Nabih Hijab, shin yakin da ya yi saboda kare tushen bubuwan da suke na dole, al’amarin da yya kai ga rashin samun tabbatacen yanayi na zaman lafiya, a daidai lokacin da yanayin Banu Umayya bai samu tabbatuwa ba sai a bisa cire wuyayen, koma dai meye, kuskurarwar Nabih Hijab ga Ali ba zai cutar da shi ba, bayan tuni Manzo (s.a.w) ya riga ya fadi cewa: Gaskiya tana tare da Ali kuma Ali yana tare da gaskiya. Kuma yana daga cikin abin da yake dabi’a ne a samu Ali tare da wadanda suke tare da shi da kuma Nabih Hijab da shi da wadanda suke tare da shi a daya bangaren.
2- Lamari na biyu: Abin da Faragal ya musanta wa Shi'a shi ne kasancewar Manzo (s.a.w) da ahlin gidansa daga haske daya suka fito, ban sani ba miye abin mamaki bayan Shi'a sun tabbatar da wannan daga masdarori ingantattu, shin ko dan wannan bai yi daidai da wasu san rai da suke cikin zukatan da ba sa bin Ahlul-baiti ba, ko kuwa? Sannan don me dan an sami irin wannan a wajen Ahlus-sunna ba ya zama abin mamaki, ga Zahabi ya ruwaito wani hadisi a cikin mizanil I’itidal, ta hanyar Abuhuraira daga Manzo (s.a.w) yana cewa: "Allah ya halicce ni da haske kuma ya halicci Abubakar da haske na kuma ya halicci Umar da hasken Abubakar kuma ya halicci Usman da hasken Umar, kuma Umar shi ne fitilar `yan aljanna , ban sani ba don me haske ya zo har kan Usman sannan ya ki karasawa kan Ali tare da cewa alal akalla shi ne halifa na hudu! Allah ne ya san girman lamarin ka ya Ali dan Abi Dalib!, ban sani ba mai Ustaz Faragal zai ce a kan wannan shin wannan gullanci ne ko kuwa?!, Ku zo mana da fatawa Allah ya gafarta malam, wannan ke nan. Tare da cewa dabi’a ne ya zama tsakanin mutum da ahlinsa akwai kadaitaka ta tsatso, alhali aalayen Muhammad (a.s) daidai suke da Kur'ani kuma taska ko kundin kuma ma’adanan ilimin Annabi ne su, to don me Ustaz Fafagal yake musanta musu abin da ba ya musanta wa wasunsu,
3- Lamari na uku: Abin da Ustaz Faragal ya musanta shi ne kasancewar ilimin Ahlul-baiti da shari’a da ilimomin Kur'ani da ilimomin Sunna madaukakiya kuma su zamo su ne masu bada hadisai, a nan za a iya cewa , lalle ilimin Ahlul-baiti ko da ya zama ta hanya ce ta al’ada kamar koyon ilimi ko zuwa makaranta, ko kuma ya zama ta hanyar ilhama da kuma cewa ana zantar da su hadisi ne, amma al’amari na daya, tabbatacce ne domin sun taso ne a gidan Muhammad (s.a.w) kuma an tarbiyantar da su a dakin sa sannan kuma sun karbi ilimomi daga wannan gidan kuma wannan lamari ne da babu wata kura a cikin ta, amma samun ilimi ta daya hanyar wato ta hanyar ilhama da kuma zantarwa kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni a kai. Musulmai baki dayan su sun tabbatar da wannan kuma da sannu zan ambaci wasu daga nassosinsu a cikin yiwuwar irin wannan ilimin:
Alusi ya na cewa a cikin tafsirin Ruhil ma’ani a yayin tafsirin ayar 65 daga surar Nahli: Shi ne fadinsa madaukaki: "Ka gaya musu ba wanda ya san abin da ke cikin sammai da kassai sai Allah" sai ya biyo bayan ta da cewa: Ta yiwu gaskiya shi ne a ce lalle ilimin gaibi da aka kore wa waninsa mai girma da buwaya shi ne wanda ya zamo da kan sa ma’ana ba da wasida ba wajen tabbatar da shi a gare shi, kuma abin da ya ke aukuwa ga kebantattun mutane baya daga cikin irin wannan da wani abu, kadai yana daga cikin wanda ya zo daga gare shi mahalicci mai girma da buwaya, yana mai kwararo baiwarsa gare su daga wata fuska daga fuskoki, ba za a ce sun san gaibu ba ta wannan ma’anar, domin lalle wannan kafircewa ne, abin da za a iya cewa anan shi ne sun bayyana ko sun yi tsankaye a kan gaibi .
Kuma abin da Alusi ya fadi, shi ne ainihin abin da ya zo daga Imaman Ahlul-baiti: Imam Ridha (a.s) na takwas daga cikin jerin Imamai yana cewa: "Yana yalwata mana ilimi sai mu sani kuma yana rike shi daga garemu sai mu zama ba mu sani ba" wannan ma’anar ita ce ainihin abin da wannan ayar take nufi: "Masanin gaibi baya bayyanar da gaibin sa ga wani sai dai wanda ya yardarwa na daga Manzo" aya ta 27/suratul Jinni. Dangane da sharhin wannan ayar ne Imam Ridha (a.s) yake cewa da Amru dan Hidab a lokacin da ya tambaye shi a kan ilimin Imamai, sai ya ce "Manzo Allah (s.a.w) shi ne yardajje a wajen Allah kuma mu ne magadan wannan Manzon wanda Allah ya tsinkayar da shi gaibin sa sai ya sanar da mu abin da ya kasance da abin da zai kasance har zuwa ranar ta shin alkiyama " a karkashin wannan ma’anar ne mafassarin nan Banaishabure ya ke cewa: Kore karama daga waliyai yana faruwa ne imma dai saboda Allah bai cencenci ya zama ahlin wannan ba, ko kuma saboda shi muminin ba ahlin wannan ba ne, kuma dukkanin wadannan korarru ne, domin dacen mumini da sanin sa, yana daga cikin mafi girman baiwar sa madaukaki ga bawan sa, idan har mai kwararowar bai yi rowar bada mafi girma da daukaka ba, hakan yana kasancewa ne saboda ba ya yin rowar bada abin da yake kasa de wannan.
Imam Sadik ya ba da haske a kan sashin ilimomin da suka ciro daga cikin Kur’anita hanya ta dabi’a, wannan ya faru ne a yayin da sashin sahabbabn sa suka tambaye shi, sai Imam Sadik ya ce: "Lalle na san abin da ke cikin sammai da kassai kuma na san abin da ke cikin aljanna da wuta kuma na san abin da ya kasance da abin da zai kasance" yayin da mai tambayar ya yi mamakin maganar sa sai Imam ya ce : "Na san wannan ne daga littafin Allah mai girma da daukaka wanda yake cewa: "Mun saukar maka da littafi yana mai bayyanawa ga komai domin shiryarwa da rahama da kuma bushara ga muninai" 89/ daga surar Nahal. Kuma lalle an ruwaito daga gare shi da kuma nazariyyar yiwuwar Ahlul-baiti su sha ililmi dan kadan ta mahanga faffada .
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi