Asalin Larabawa da Mazhabobi
Littafi: Hakikar Shi'anci
Asalin Larabawa da Mazhabobi - 1
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Fasali Na Hudu:
Tattannawa a kan Littafin Nash’atul Ara’ab Wal-mazahib
Marubucin littafin Dakta Yahaya Hashim Fargal yana mai nufatar lamarin ismar imamai: Lalle ismar imamanci ta bayyana ne a wajen gullat, an ce lalle Zaidu dan Ali ya kasance yana musanta ta, sannan sai ya kai ga fitar da sakamakon cewa Sunna sun yi bahasi a kan ismar Annanbawa ne saboda Shi'a sun yi bahasi a kan ismar imamai, sannan sai ya ambaci hujjojin ismar imamai daga ciki akwai hadisin sakalain:
Lalle na bar muku abin da mutukar kun yi riko da shi ba zaku taba bacewa a baya na ba. Littafin Allah igiya ce wacce take nade da sama zuwa kasa da kuma yayan gida na, kuma ba zasu taba rabuwa ba har sai sun same ni a tafki, ku yi duba zuwa yadda zaku wakilce ni a cikinsu, sannan sai suka ambaci wasu kalolin na wannan hadisin, sannan sai ya ce: Wannan hadisin ya sanya `ya`yan gidan Manzo a matsayin Kur'ani kuma kwatankwacinsa kamar yadda ya sanya musu dukkanin matsayin da Annabi yake da shi na daga matsayi da martaba, in banda Annabta, domin ya zama kamar yana nan ne shi da kansa domin ya tsaya da kiyaye shari’a, wannan hadisin ya ajiye `ya`yan gidan Manzo a matsayin Kur'ani ka ga ke nan babu makawa da ya zamo a tare da su a kan dukkanin abin da yake cikin sa na daga ilimi, daga nan Imami zai zama masani dukkanin Kur'ani da Sunna dalla-dalla domin a riki ilimin su daga gare shi a kammale sannan ya gabato da ruwayoyi na Shi'a dangane da ilimin Imami daga ciki akwai abin da ya zo daga Imam Ali (a.s) ba a saukar da wata aya daga Alkur'anin ga Manzo ba face sai ya karanta mini ita ya yi tilawar ta a gare ni kuma na rubuta ta da hannuna kuma ya sanar da ni fassararta da ta’awilinta da muhkamin ta da mutashabihin ta da nasihin ta da khas dinta da Aam din ta, kuma ya roki Allah Madaukaki ya bani fahimtar ta da hardace ta kuma ya sanya hannun sa a kan kirji na ya roki Allah ya cika zuciya ta da fahimta da kuma hukunci sannan sai ya gangaro da ruwayoyi wadanda a sarari suna kamanta abin da aka furta a wannan hadisin wadannan ruwayoyin sun hada da cewa akwai jafar da jami’a da mus’hafin fadima da ke wajen Ahlul-baiti ya kuma kawo sharhin ra’ayoyin Shi'a a cikin ma’anar samuwar wadannan litattafan a wajen Ahlul-baiti kuma ya fadi cewa: Lalle Shi'a sun ce imla’in Manzo ne kuma shiftar Ali kuma lalle babu wani na Kur'ani daga cikin ta kadai abin da ke ciki ya kunshi sharhi da labarai da fituntunu, sannan ya ambaci wasu ruawayoyin da suke yin nunn a kan cewa iamamai su ne masu ruwaito hadisi kuma su ne suke rike da wadannan ruwayoyin ta hanyar ruwayoyin Sunna daga ciki akwai fadinsa wanda Ahlus-sunna suka hadu a kan sa, daga ciki akwai fadinsa Manzo (s.a.w) "Lalla a cikin ku akwai masu ruwaito hadisi" da kuma fadinsashin sahabbai : Na kasance ina bada hadisi har sai da na gajiya" sannan bayan haka ya ciratu zuwa ruwaoyin da suke yin nuni a kan kadaitakar zurin halitta tsakanin Manzo da imamai, kamar irin fadin Manzo (s.a.w): Lalle Allah ya halicce ni sannan ya halicci Ali da Hasan da Husaini daga haske daya, sannan a karshen wannan fasali ya ce: To lalle mu kam a karshe zamu kai ga wata akida ta falsafa ko ta mitafizik a cikin lamarin imamancin da ta sa manzo da imamai suka zama jauhari guda daya na haske wanda ya gabaci halittar kasa, kuma a nan ne zamu isa zuwa nukda mihimmiya waccce zamu yi tambaya a kan ta, cewa mene ne matsayin imamanci kuma shin a mtsayi daya take da annabci ko kuwa, daga wannan ne zan kara korowa in ce: Lalle mutumnin da yake dauke da wannan a kidar ba a bin mamaki ba ne a sami faruwar wata akida kamar ta gullat da da’awar annanbtaka daga kurarta ba, kuma daga wannan za a iya samun wani sabon yanayi da wannan yanayin ya haifar. A nan maganar fargal ta kare a takaice tare da yin tasarrufi a ciki lafazin jimlolin nasa, bisa kiyaye abin da ta kunsa.
Ya bayyana a sarari daga karshen wannan fasali da muka rairayo cewa Faragal yana musanta wasu abubuwa kuma yana ganin su a matsayi wani nau’i na shisshigi wanda ita ce isma, sannan kadaitakar asali da zurin halitta tsakanin Annabi (s.a.w) da tsatsonsa (a.s), sannan kuma ya musanta abin da ake jingina wa Ahlul-baiti na daga ilimomi sannan kuma a karo na hudu kuma ya musanta matsayin imamai a bayan Manzo (s.a.w), na biyar kuma ya jingina wa Shi'a gullanci.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi