Abdullahi Bin Saba’ - 4
Littafin: Hakikar Shi'anci
Maudu’i: Abdullahi dan Saba’ - 4
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Ra’ayoyin Marubutan Yamma
1- Dakta Barnad Luwuis: Yana cewa: Sai dai bincike ya tabbatar da cewa lalle rigyangyantu ne da `yar tsere, da aka shirya a kan abubuwan da suka faru, kuma lalle wannan mutumin – wato Abdullahi dan Saba’- wani mutum-mutumi ne da aka misalta shi bisa abin da ya gabata, kuma ma’abota hadisan karni na biyu bayan hijira suka sauwara shi bisa yanayin su, da kuma irin nasu tunanin da yake yawo a wannan zamanin.
2- Falhozan: Ya tafi akan cewa, mutum-mutumin da kiraye-kiraye da kuma abubuwan da ake jinginawa ga dan Saba’ yana daga cikin kiren karyar mutanen da suka zo daga baya, kuma lalle ya tantance nassosin kuma ya karanto yanayin daga karshe ya zo da warwara mai zurfi.
3- Kayitani: Ya yi shakka a cikin samuwar Abdullahi dan Saba’ kuma ya yi magana a kan abubuwan da ake jingaina masa na daga manya- manyan ayyuka, da kuma irin wannan tashifadin bisa irin wannan tunanin da kuma tsarin, ba zai taba yiyuwa duniyar larabawa wadda aka sani ta shekara talatin da biyar, wacce take tafiyar da mulkin ta bisa tsarin `yan’ubanci, lalle kacokaf lokacin sa ya saba da lokacin abbasawa na farko.
Ra’a’yoyin Wasu Daga Cikin Malaman Musulumci Akan Dan Saba’:
Akwai wasu ra’ayoyin akan Abdullahi dan Saba’ wadanda suke kaikawo a tsakanin samuwar sa da rashin ta da kuma rashin alakar sa da Shi'a, da kuma tsakanin rashin gasgata abin da ake jinginawa a gare shi domin yana daga cikin abin da ba mai yiwuwar faruwa ba ne daga dan Adam na dabi’a ba, kuma da tsakanin jingina wadannan ayyukan ga wani mutum na daban wanda aka kira da dan bakar mace, don haka bari mu ji wadannan ra’ayyoyin.
A- Muhammad kard Ali ya fadi a cikin Hudadush Sham:
Amma abin da wasu daga cikin marubuta suka tafi a kan cewa mazhabar Shi'a tana daga cikin bidi’ar Abdullah dan Saba’ wanda aka sani da dan Baka, wannan rudu ne da karancin ilimin sanin hakikanin mazhabarsu, kuma wanda ya san matsayin wannan mutumin a wajen Shi'a da kuma barrantar su daga gare shi da maganganun su da ayyukan su, da kuma maganganun malaman su a wajen sukar sa ba tare da sabani ba a tsakanin su a cikin wannan, zai san mutukar gaskiyar wannan maganar.
3- Dakta Ahmad Mahmud Subhi A Cikin Nazariyyatul Imamah:
Ba abin da zai hana Yahudawa su yi amfani da fare- faren da suka gudana a lokacin Usman ba, su kara mata huruwa kuma su dada zuga mutane akan Usman, kai har ma su yi kira a kan tunanunnukan da ba a san su ba, sai dai abin da ya rigayi lokacin sa, shi ne cewa, shin dan Saba’ yana da irin wannan tasirin mai tsananin da har zai iya haifar da wannan rarrabar ta akida tsakanin wani bangare mai girma daga musulmai?.
4- Daktoci guda biyu, Aliyul Wardi Da Kamilush Shaibi sun hadu a kan abin da zai zo.
Lalle wanda ake nufi da dan Baka Ammar Bin Yasir ne, domin yana da girma da matsayi a cikin Sahabbai kuma ya kasance a gaba- gaban yan tawaye ga Usman, kuraishawa ba sa so su ajiye shi daura da Uaman kuma a gefen Ali, domin yana rinjayar da dangaren Ali ya kuma rusa na Usman, don haka sai suka yi masa ramzi (suka bashi take) suka ambace shi da dan Baka domin Babarsa Baiwa ce Baka kuma babu wani dan Baka ba shi ba.
Ra’ayin daktocin nan guda biyu ya yi daidai da ra’ayin Asfarani da Ibn Dahir Babaadade wanda mukayi nuni a kan sa a cikin abin da ya gabata a yayin da muke yin bayani a kan ayyana hakikanin dan Saba’
Bayan wannan `yar jaular (kewayen) a kan ra’ayoyin, ya bayyana a sarari cewa babu samuwar dan Saba’ domin sallamawar mu akan samuwar sa ya na bukatar mu wurgar da hankulan mu, kuma tafarkin bincike na ilimi ya ki yarda da samuwar sa domin masdarorin sa sun saba, kuma saboda wadanda suka halitto Abdullahi dan Saba’ sun halitto masa yan’uwa na daga da’awoyin da dasannu zamu dora hannun ka a kan sun a nan kusa- kusa, duk da cewa da sannu zasu girgiza tunanin ka su kuma rusa sikkar ka (amincin ka) da wadanda kake ganin su daga cikin kololuwa a Musulumci, domin abubuwan kece al’adan da ake jinginawa dan Saba’ ba zai taba yiyuwa a gasgata su ba, kuma saboda yin shurun Usman a kan sa yana da ban mamaki tare da cewa ya nisanta (kora) Abuzar zuwa Rabza tare da cewa Abuzar yana daga cikin mamaya-manyan Sahabbai, ba don komai ba sai don Abuzar ya kasance yana da ra’ayin a kyautata rayuwar Musulmai a lokacin Usman, don me ake yin irin wannan mafarkin a kan dan Saba’, kuma saboda kasantuwar Ali mai tsauri ne a kan lamarin Ubangiji ta yaya zai yi shiru a kan dan Saba’ kuma ya ki kona shi kamar yadda ya yi wa wanin sa, kuma saboda ma’awiya shi ne wanda ya ke kashewa a sakamakon tuhuma da zato, ta yaya a ka yi ya yi shiru game da lamarin dan Saba’ alhai shi ne wanda ya aika Busir ya kaiwa makiyan sa hari kuma harin ya kai ga kashe mutun dubu talatin, dukkanin irin wadannan abubuwan na labarin Dan Saba’ suna daga cikin dalilan da suka sa ya zama labari abin kirkira, kadai an kikire shi ne domin manufar da muka ambata a baya domin a sa shi a matsayin masdarin ko tushen na akidun Shi'a baki dayan ta, kamar yadda kowanne daga cikin Muhyuddin Abdulhamid a cikin ta’alikin da yayiwa littafin Makalatul Islamiyyin da kuma Ali Samin Nashshar a cikin littafinsa Nasha’atul Fikiril Falsafi, kuma kowanne daga cikin Aliyun Nashshar da Muhyid Din ba sa daga cikin wadanda suka jahilci akidun Shi'a, ko kuma wadanda ba su da hanyar da zasu sami masdaran su ba, alhali a inda suke akwai masdaran da suke dauke da dukkanin abin da ake bukata, kuma ga ayyakan nan na akida a gaban idanun su kuma a sarari ana gabatarwa wanda yake nuna yadda akidar Shi'a take, kuma tare dadukkanin hakan suka rubuta abin da bai yi daidai da amanar tarihi da kuma tarbiyyar Musulumci ba, a kan Shi'a, bai kamata misalin irin wadannan su rika sa rigar masu kawo gyara a cikin mihimman al’amuran musulmi ba wadanda su wadannan bisa hakika, yan saddu ne (masu tare hanya ne) masu wautar da wadansun su, in ba haka ba, ai alamomin tambaya na nan birjik a cikin abin da suka rubuta, a yayin da marubutan da suka san abin da suke yi, su na karfafa cewa lalle labarin dan Saba’ kire ne. Ahmad Abbas Salih yana cewa: Abdullah dan Saba’ mutum ne na kire ba tare da wani shakku ba, ina shi ina dukkinin wadannan fare- fare, kuma lalle babu wani kokwauto sakarai ne zai yi kokarin halittar wani mutum kamar wannan domin ya ba shi wani irin tasiri a cikin fare- faren da suka kasance, lalle dukkanin abin da aka hakaito na daga labari a kan Abdallahi dan Saba’ yana daga cikin kiren mutanen baya domin babu wata hujja ta samuwar sa a cikin litattafai.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi