Abdullahi Bin Saba’ - 3
Littafin: Hakikar Shi'anci
Maudu’i: Abdullahi dan Saba’ - 3
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Ra’ayinmu Kan Abdullahi dan Saba’
Mu dai muna ganin mutum ne na rudu kirkirarre kuma muna kafa hujja a kan cewa shi tatsuniya ce kawai saboda abubuwa masu zuwa:
1- Yin sabani a kan cewa shi ne dan bakar mace, ko kuwa, tare da cewa wanda ya aikata dukkanin wadannan musibu shi ne dan bakar mace, kuma Ibn Dahir da Isfarayini suna cewa lalle dan bakar mace wani mutun ne daban da ya yi tarayya da Abdullah dan Saba’ a cikin abin da ya ke da’awa.
2- Yin sabani a kan lokacin bayyanar sa, Dabari ya tare da wasu jama’a sun tafi a kan cewa ya bayyana ne a lokacin Usman a yayin da wasu kuma suka tafi a kan cewa ya bayyanan ne a lokcin Ali (a.s) ko kuma bayan mutuwarr sa, daga cikin su akwai Sa’id dan Abdullah ba’ash’are, a cikin littafinsa Makalat, haka ma Ibn Dahir a cikin Alfarak bainal frak, da wasun su masu yawa.
3- Yin maganganu masu karo da juna a cikn ruwayoyin dangane da aslin kiran sa, a yayin da Dabari da wasu jama’a suke ganin cewa lalle da’awar sa ta takaitu da gullatanci, da kuma kira zuwa taimaka wa Ali da ma dai dukkanin abin da ya shafi Ali, a yayin da kuma muka sami wasu daga cikin `yan baya suke ganin cewa daidai da yadda masdarin su su ke cewa lalle ya na da’awar da yake yi a kowane gari. Muhibbud dinul Khadib yana cewa bisa isnadin da ya ambata.
Dago cikin kaifin basirar Ibn Saba’ da makircin sa, ya kasance yana yada kira zuwa Ali a cikin mutanen Fusdad, a cikin mutanen Kufa kuma yana yada kira zuwa Dalhatu, a cikin mutanen Basara kuma ga Zubair.
4- Lalle sashin ruwayoyi sun ambaci cewa ya takaitu a kan yada falalar Ali a yayin da wasu kuma suka tafi a kan cewa ya kasance yana harzuka jama’a a kan Usman yana ta kafa dasisa, kuma shi ne ma ya ingiza Abuzar zuwa yin tawaye, ko dai ga Mu’awuya ko kuma Usman a wasu ruwayoyin.
5- Wadanda suka kirkiri kissar dan Saba’ ba su fada mana dalilin da ya sa Usman ya kyale shi ba shi da mabiyan sa tare da cewa sun daddaki wadanda suka yi fito na fito tare da mafi munin tsanantawa da rashin tausayi, alhali suna daga cikin mafi zababbubu daga cikin Sahabbai. Kamar Ammar da Ibn Mas’ud, da makamancin su.
6- Saboda me ingantattun masadarori suka wofinta da ga ambaton wannan kissar ta Dan Saba’ kamar Balazuri da Ibn Sa’ad da makamancin su daga cikin wadanda ake dogaro da maganganunsu.
7- Lalle ruwayar Abdullah Dan Saba’ makirkira kuma makaryata ne suka ruwaito ta kamar yadda muka ambata a baya.
8- Daga cikin abin da zai dada fito da kiren a fili kasantuwar cewa ba wannan ce kadai kissar ta karya da a ka jinginawa Shi'a ba, lalle wannan ba komai ba ce face sai wani dan bangare daga cikin karerakin da a ke yi wa Shi'a, wanda da sannu zamau bayyana maka su a nan gaba, kuma mukafa maka dalili a kan kasantuwar su gabaki daya karya ce. Har kasan cewa kissar Abdullah dan Saba’ ta fito ne daga macira daya da kuma ainihin manufa guda. Amma yanzo bari mu dan bijiro da ra’ayoyin mawarwara (masu nakadi) da masu bincike wannan kissar domin mu isa zuwa gaskiya.
Ra’ayin Daha Husain
Dakta Daha Husain ya bijiro da surar da aka kera wa Abdullah dan Saba’ sannan ya yi kaca-kaca da ita bayan warwara mai zurfi, kuma ya tuke a kan cewa lalle Ibn Saba’ mutum ne nawahami da makiyan Shi,a suka kirkira kuma ya karfafi ra’ayin sa da abubuwa masu zuwa:
Na daya: Lalle dukkanin masana tarihi amintattu ba su ruwaito kissar Abdullah dan Saba’ ba kuma ba su fadi komai a kan sa ba.
Na biyu: Madogarar labarinsa mutum daya ne kawai, shi ne Saifu dan Umar kuma shi mutum ne da aka san shi da karya, kai an tabbatar kuma an yanke a kan cewa shi makirin hadisai ne.
Na uku: Abubuwan da aka jingina wa Abdullahi dan Saba’ suna bukatar mu’ujizojin da suka wuce hankali, kamar yadda ya zama dole musulman da Abdullah dan Saba’ ya yaudara kuma ya sihirce su zama wadanda suke zartar da hadafofinsa ba tare da ja-inja ba, da kai mutuka da rashin ko in kula.
Na hudu: Rashin samun wani gamsashshen bayani a kan yin shirun Usman shi da wakilan sa, tare da cewa sun doki wanin sa daga cikin masu yin ja-in-ja, kamar su Muhammad dan Abi Huzaifa da Muhammad dan Abubakar da Ammar da makamancin su.
Na biyar: Labarin konawa da kuma ayyana irin sunnar da dan Saba’ ya tsira da ga konawa a sakamakon ta, ta wufinta daga cikin litattafan tarihi ingantattu, kuma babu iri-irin alamar ta a cikin su.
Na shida: Rashin samun wata alama ta Abdullah dan Saba’ da jama’ar sa a yakin Siffin da yakin Nahrawan, kuma lalle Daha Husain ya tuke a kan cewa: Hkika dan Saba’ mutum ne da makiya Shi'a suka tanade shi domin yakar Shi'a, kuma ba samamme ba ne a sarari, kuma da yawa daga cikin marubutan yamma sun dace da Daha Husai a kan wahamcin samuwar Abdullahi dan Saba’, daga cikin su akwai:
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi