Abdullahi Bin Saba’ - 1
Littafin: Hakikar Shi'anci
Maudu’i: Abdullahi dan Saba’ - 1
Wallafar: Sheikh Wa'ili (r)
Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
Fasali Na Biyu: Abdullahi Bin Saba’
Duk dayawan masdari da su ke magana a kan Shi'a da kuma hadarin yin rubutu a kan lamarin akida, da kuma dukkanin yadda hakikanin Shi'a ya ke a sarari ta hanyar muassasoshi da kuma ayyukan na akida, da masallatai da suke ta maimaita kalmar kira zuwa hadin kai dare da rana, tare da dukkanin wadannan, mu ba mu gushe ba muna ganin mai yin rabutu a kan Shi'a yana barin wannan gaskiyar a bayansa kuma ya na juya fuskarsa zuwa rubuce-rubucen mutanen da su da wadanda suka gabace su, sun ta rubuta abubuwan da ba ingantattuba sabo da dalilai daban-daban maimako su koma zuwa litattafan Shi'a kansu, sai mu ga suna koma wa zuwa maganganu da rudani ya kirkira, sannan keta ta haifo su, sannan kuma kiyayya ta halitto su, kuma ta yiwu ma jahilci ya zama daya daga cikin dalilan samun su, daga cikin abin da wadannan marubutan suka raya shi ne cewa, akidojin Shi'a wani mutum ne bayahude mugu mai dasisa ya kirkiro su a cikin farfajiyar malamai wanda ake kiran sa Abdullahi dan Saba’.
Wannan bawan da aka kaddaro shi (a ka yi mutum- mutumin sa) lamarin sa mai ban mamaki ne, wasu matane sun sana’anta shi kuma suka kirkire shi kirkira, kuma suka ba shi siffofin da suka gajiyar da dan Adam a tunani, kama suka kirkiro masa damar yin abu irin wanda ba zai yiwu a jingina shi ba sai ga ifritan da muridan aljanun nan na cikin tatsuniya, kai harma da abin da al’umma mai karfi ba zata iya cimma sa ba sun jingina masa, ballana tana kuma mutum daya, lalle irin wannan maganar kan dakin tunanin mukafin ta ta zama tatsuniya a cikin tarihin mu, kuma da sannu zamu gani! Shin wane ne ya kirkiri Abdullah dan Saba’? kuma waye shi? Kuma me ya aikata? kuma saboda me yake da alaka da Shi'a.
Wa ya Kirkiri Abdullah Bini Saba’
Lalle wnada ya ke so ya san asalin inda aka haifo Abdullah dan Saba’, zai samu cewa a ruwayoyin Dabari ne, kuma ruwayoyin Dabari a wannan mahalli sun jingina da majingina biyu ne, wadanda sune:
A- Majingina ta farko:
Saifu dan Umar, kuma ga abin da masu ruwaya suka fadi a kan sa, da kalma guda kuma iri daya.
Ibn Hibban yana cewa: Saifu dan Umar ya kasance yana ruwaito kirkirarrun hadisai daga amintattu, kuma sun ce ya kasance yana kirkirar hadisai, kuma an tuhumce shi da zindikanci, kamar yadda Hakimun Nisaburi ya ruwaito a a kan sa cewa an tuhumce shi da zingikanci kuma shi fadadden mai ruwaya ne, kuma Udayyu yana fadi game da shi, cewa sashin hadisan sa mashhurai ne kuma dukkaninsu munkarai ne ba a la’akari da su, kuma ibn Mu’in yana fadi game da shi mai raunanannun hadisai ne babau alheri a tare da shi, kuma Ibn Khatam ya ce: Abin barin hadisan san sa ne, kuma maganar sa tana yin kama da ta Wakidi. Kuma abin Dawud ma’abocin Sunan ya ce shi ba komai ba ne, kuma Nisa’i ma’abocin Sunan ma ya ce shi mai rauni ne, Saifu dan Umar abin bari ne, kuma an tuhumce shi da kirkirar hadisi da zindikanci kuma ya kasance mai yawaita kire.
B- Sariyyi dan Yahya kamar yadda Dabari ya kira shi kuma ba shi ne Sariyyi dan Yahya Sikka (amintacce) ba, domin Sariyyi dan Yahya amintacce zamanin sa ya rigayi zamanin, Dabari ya rasu a a shekara ta 167 BH. A yayin da shi kuma Dabari an haife shi a shekara ta 224, bambancin da ke tsakaninsu shekara hamsin da bakwai ne (57), kuma masu ruwaya ba su da Sariyyi dan Yahaya banda shi, don haka ne ma masu raunatawa da adaltarwa suka hasashi cewa lalle Sariyyi din da Dabari yake rawaitowa daga gare shi dole ne ya zama daya daga cikin wadannan guda biyun: Kuma kowanne daga cikin su makaryaci ne, sune Sariyyu dan Isma’il bahamdane bakufe wannan ne na farkon su, na biyun su shi ne, Sariyyi dan Asim bahamdane wanda ya sauka a Bagdad, wanda ya rasu a shekara ta 258, wanda shi ne wanda Ibn Jarir Dabri ya riska, kuma ya zauna da shi sama da shekara talatin. Kuma dukkanin wadannan lalle ma’abota hadisi sun karyata su, kuma sun tuhumce shi da kire.
Ma’abocin Tahzibul tahzib ya ce su (su biyun) makaryata ne, haka ma mai Mizanul i’itidal, da mai Tazkiratul maudu’at, da mai Lisanul mizan, da wasunsu kuma sun tuhumci daukkanin su da kirkirar hadisi kuma mai karrtu zai iya komawa zuwa masdarorin da muka ambata a karkashin tarjamar wadanda muka ambata. Masu nakadi sun ce: Dabari yana da hadisai dari bakwai da daya wadanda suka shafi lokacin halifancin halifofi uku kuma sanadan wadannan hadisan dukkanin su daga Sariyyu makaryaci suke, shi da kuma Shu’aibun da ba a san da samuwar sa ba da kuma Saifui makirkrin hadisi wanda aka tuhuma da zindikanci.
Daga cikin wadannan ruwayoyinn akwai ruwayar dake dauke da halayen Abdullahi dan Saba’ kuma sanadinsa daga shu’aibu, sai Saifu dan Umar, kuma dukkanin wadanda suka yi rubutu a kan Abdullah dan Saba’ zaka samu ya jingina ne da dabari kuma daga gare shi yake dauka kuma gare shi ya jingina daga nan ne zaka san gwaurgwadon abin da ke tattare da lamarin Abdullahi dan Saba’ na daga tabbaci da gaskiya, a ra'ayi na yana daga cikin wargi mu tsaya muna waiwayar da fusakun wadannan da suka dage a kan samuwar sa da kuma abin da ya tsaya da shi na daga ayyuka, domin naga suna ta kokarin samar da shi, duk da cewa a gaske bai zama samammen ba, ba don komai ba sai don wasu abubuwa da suke cikin zukatan sa.
1- Waye Abdullah dan Saba’
Domin sanin hakikanin Abdullah Dan Saba’ da sannu zamu fara da mububbuga ta asasi wato tarihin Dabari sannan in biyo bayan sa da sauran masdarori kuma da sannu zan cirato fadin Dabair ta hanyar abin Abu Zuhrah ya cirato, ya ce: Abdullah dan Saba’ ya Kasance Bayahude ne daga cikin mutanen San’a' Babarsa bakace, sai ya musulunta a lokacin Usman sannan ya yawaita garuruwan musulmai yana kokarin ya batar da su, sai ya fara da garuruwan Hijaz sannan Basra sannan Shama, bai sami ikon cimma abin da yake so ba awajen wani daga cikin mutane Sham, sai suka fiatr da shi, har ya zo Misra sai ya ce da su, a irin maganganun da yake yi mamaki ya tabbata ga wanda yake raya cewa Isa zai dawo kuma yake karyata cewa Muhammad zai dawo, kuma lalle Allah Madaukaki yana cewa "Lalle wannan da ya farlanta maka Kur'ani zai komar dakai zuwa tashi bayan mutuwa" Alkasas/85.
Sannan lalle Muhammad ya fi cacantar dawowa fiye da Isa, sannan ya ce bayan haka lalle anyi Annabawa dubu kuma kowane Annabi yana da wasiyyi kuma Ali shi ne wasiiyin Muhammad kuma Muhammad ne cikamakin annabawa, Ali kuma cikanmakin wasiyyai.
Ana akwai wasu nukdodi da ya fadi, in so in karfafe su domin in gwama su tare da wasun su, shi ne cewa: Na farko dai shi dan bakar mace ne, na biyu kuma shi dan mutanen San’a' ne, na uku kuma shi ne yana karfafa dawowar Manzo (s.a.w) wannan duniyar, na hudu kuma yana cewa Ali wasiyyin Annabi ne, na biyar shi ne cewa ya musulunta a lokacin Usman, bayan wannan kuma, bari mu kuma komawa wajen abu zuhra a dai wannan littafin nasa abin ambato, Tarihu mazahibul islamiyya a wani wajen yana cewa, Abdullah dan Saba’ ya kasance bayahude, daga cikin mutane Haira ya bayyana musulumtar sa sai yafara yada cewa lalle ya samu a cikin attaura cewa: Lalle kowane Annabi yana da wasiyyi kuma lalle Ali shi me wasiyyin Muhammad, kuma lalle Ali yaso ya kashe shi sai Abdullah dan Abbas ya hana shi. Sai ya kora shi mada’in a maimakon kashe shi.
Tsakanin wadannan yan tsokaci kan guda biyu akwai banbance banbance masu zuwa wadanda na kallae so kallo na nazari su ne:
Cewa shi dan San’a' ne, a magana ta biyu kuma shi dan Haira ne, da kuma cewa ya musulunta a lokacin Usman a magana ta biyu kuma ya bayyana musuluncinsa kuma bai tantance lokacin musulumtar sa ba, da kuma cewa Imam Ali ya yi niyyar kashe shi kamar yadda ya fadi a magana ta biyu a yayin da bai ambaci hakan ba a ta farko, kuma lalle yana daga cikin abin yin tsakaci a kan sa sanya lamarin wasiyya na cikin attaura, a yayin da a magana ta farko bai ambaci, matsamar wannan tunanin ba, mu lura da wadannan abubuwan domin muga abin da ke tsakanin wadannan maganganun na daga banbamce- banbamce, da kebance- kebancen da suke cin karo da juna.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Ƙara sabon ra'ayi