Ra'ayin Musulmi Game Da Sahabbai

Ra'ayin Musulmi Game Da Sahabbai

Magana kan wannan lamari tana daga cikin mafi girman abin da ake ta jayayya a kanta, ta yadda masu sukan Shi’a suka shahara da tuhumarsu da rashin yarda da adalcin wasu daga cikin sahabbai. Shi’a suna ganin wannan tuhumar a matsayin kage ne da ya dade ana yi musu shi. Sharrin ya kai ga wasu suna cewa Shi’a suna ganin sahabbai kafirai ne, da sauran kage da ake jifan Shi’a da su game da mas'alar sahabbai. Dogaro da wannan kagen ya kai ga wasu masu zafin rai daga masu kiyayya da Shi’a suna halatta jininsu ko kafirta su.

Lamarin sahabbai wani abu ne da masu gaba da Shi’a suka fake da shi domin su samu cimma burinsu na yi wa Shi’a bita-dakulli domin kawar da su, ko sanya su abin kyama a cikin al'ummar musulmi yayin da suka ga babu wata hanya da zasu iya gamawa da su.

Shi’a suna ganin girman sahabbai sabanin yadda masu kiyayya da su suke nuna wa duniya, don haka ne ma ya kasance suna da addu'o’i na musamman da suke yi wa sahabbai da suka taimaki Annabi (s.a.w) wadanda suka bayar da rayukansu da dukiyoyinsu da dukkan abin da suka mallaka domin musulunci ya tsayu da kafafunsa. Shi’a suna ganin cewa ba don wadannan sahabbai ba, da babu wani abu da zai zo mana na shiriyar musulunci, don haka ne suka cancanci wannan yabo da addu'a gun su.

Idan dai Shi’a haka suke gani to ina ne matsalar take, ina ne aka samu wannan kage da ake yi musu? sannan don me masu sukan su suke wannan kagen, an ya kuwa babu wani abu da ya kawo hakan? Wadannan tambayoyi ne da dole a bayar da amsar su domin samun gaskiyar hakikanin inda matsalar take, don haka ne zamu fara da wata shimfida kamar haka:

 

Wane ne Sahabi?

Suna cewa shi ne wanda ya ga Annabi (s.a.w) ko ya yi zama gunsa wani lokaci. (Zubdatul Afrak: 144)

Sai dai wannan bayani game da sahabi kuskure ne babba, domin a lugga ba a kiran mutum aboki, sai wanda yake ya lizimci mutum wani lokaci da bisa al'ada mutane suke kiran sa da cewa shi abokinsa ne, ko sahibinsa ne. Ga dukkan alamu an kirkiro wannan ne domin a wanke laifin da wasu littattafai kamar sahihul Buhari, da Masnad Ahmad bin Hambal, suka yi nuni da shi na shigar mafi yawancin sahabbai wuta. Don haka sai aka gyara ma'anar sahabi domin fitar da wadanda suka shahara daga cikinsu daga cikin wancan hadisi.

A dukkan al'adar rayuwar zaman tare da 'yan Adam suke da shi ba mu taba ganin ana kiran abota ga wanda kawai ya ga mutum ba. Idan dai wanda ya ga mutum ana iya kiran sa sahabinsa, ko sahibinsa, ko abokinsa, to da yara da mata, da wanda ya zo ya yi tambaya sau daya ya wuce garinsa, da wanda ma ya hango manzo (s.a.w) kamar mutanen da suka halarci hajjin ban kwana, da makaho kamar Abdullahi bn Ummu Maktum da sauran makafi daga sahabbai duk da sun fita daga cikin sahabbai.

 

Darajojin Sahabbai:

Sahabbai ba duka suke daya ba a daraja, da tunani, da ilimi, da matsayi, da fahimta, da ganewa, da halaye, da dabi'a, da wayewa, da sani. Su suna kamar sauran musulmi ne a kowane lokaci a halaye da rayuwa, da tunani, kamar yadda kowane zamani mutanensa suke sassabawa a wadannan janibobi na halitta da rayuwa.

Wato idan muka kalli mutane tun daga Annabi Adam (a.s) har zuwa yau, zamu samu cewa; ba su da bambanci a kowane zamani a dabi'arsu ta 'yan adamtaka, a matsayin masu tunani da hankali, da son kawukansu, da kin abin da bai yi musu daidai ba. Don haka babu wanda yake fita daga dabi'ar dan Adam ta halitta, suna nan kamar yadda sauran mutane suke a dukkan abin da ya shafi wannan.

Ibn Khaldon yana cewa: Sahabbai duka ba daya suke ba a matsayi da darajoji na ilimi da bayar da fatawa, wannan lamari ne da ya kebanta da masu iliminsu kawai, masu dauke da ilmin Kur'ani. (Al’irshad, shafi 5, bugun Bairut)

Kamar yadda zamu ga nuni a cikin littafin sahih Muslim da cewa iliminsu yana tukewa zuwa ga mutane shida ne daga cikin sahabbai, kamar yadda mai Dabakat ma ya kawo shi. (Dabakat: Ibn Sa'ad, j 2, shafi: 109-110)

 

Sahabbai a Kur'ani

Littafin Allah da sunnar manzonsa sun yi magana kan sahabbai a wurare masu yawa, magana kan wannan lamarin tana da yawa matuka, sai dai zamu wadatu da mafi muhimmanci da inganci ne kawai.

 

1.    Ayoyin Da Suka Yabi Wasu Sahabbai

Akwai ayoyin da suka zo suna nuni da darajojin wasu daga sahabbai da imaninsu da yardar da Allah ya yi musu saboda wasu ayyuka da suka yi na alheri kamar surar Fathi: aya; 18.

Da kuma mai nuna wasu sahabbai da siffofinsu na gari da abin da Allah ya yi musu alkawari na lada sakamakon imani da aiki na gari a surar Fathi: aya; 29, da Tauba: 100.

 

2.    Ayoyin Da Suka Soki Wasu Sahabbai

Akwai ayoyi masu yawa da suka kausasa magana ga wasu jama'a daga sahabbai da cewa munafukai ne, kuma sun goge a kan munafunci da hatta wannan ya buya ga musulmi da manzo (s.a.w) kansa kamar a surar Tauba: aya; 101. Da wadanda suka siffanta su da cewa makaryata ne kamar surar Bakara: aya; 8. Da akwai ayoyi masu yawa kamar a surar Tauba: ayoyi; 74, Bakara: 14, domin samun wannan ana iya duba surorin Bakara, Munafikun, Ahzab, Nisa’i, Amfal, Hashar, da sauransu.

Sannan zamu ga manzon Allah (s.a.w) ya hana sare wuyan Abdullahi dan Ubayyu, don gudun kada a ga yana kashe sahabbansa, sai wanda yake nesa ya kasa ganewa ya ki shiga musulunci. Duba: Kitabu fadha’ilu kur'an: surar munafikun; j 6, shafi; 56, da Dabaka na Ibn Sa'ad: j 2, shafi; 56.

Amma yawasu suna da yawa, muna iya ganin yakin Uhud adadin sahabbi su dubu daya ne, amma a cikinsu akwai munafukai kusan dari uku da suka koma suka ki zuwa. (sahihul Buhari: j 5, s; 181, Baihaki: j 9, s 13).

Sannan zamu ga a cikin larabawan kauye sun fi yawa kamar yadda ya zo a tarihin musulunci, su kuwa Allah ya yi musu sheda da cewa: su suka fi kowa kafirci da jahilci. Surar Tauba: 98, 101, 97, surar Fathi: 11, Hujurat: 14.

Kasancewar ayoyin Kur’ani duk sadda suka yi magana kan su suna nuna kafirci da munafuncinsu ne ya sanya ra'ayin musulunci ya nuna mana su a matsayin mafi yawansu ne hakan, sai dai wadanda Allah ya toge su daga ciki a surar Tauba: 99, da cewa daga cikinsu akwai wadanda ake samu muminai ne.

A wancan zamanin na manzon Allah (s.a.w) zamu ga musulmi sun yawaita, kuma ya rasu ya bar kusan 100 000, a cikin akwai larabawan kauye kusan 30 000. (Tadribur rawi: s 206, al’isaba na Ibn Hajar).

Sa'annan muna iya ganin cewa hatta da wadanda suke Madina a matsayin masu zama tare da Annabi (s.a.w) suna fifita wasu abubuwan rayuwa a kan na addini, wannan yana da misalin wadanda suka watse saboda sun ga kayan kasuwa ya iso, suka bar manzon Allah da mutane kusan 12 kawai alhalin yana hudubar sallar juma'a. Surar Juma'at: 11.

 

Sahabbai a Sunna

Abin mamaki da aka samu wasu daga mabiyar mazhabar Sunna suna sukan Shi’a da cewa suna zagin sahabbai, ko tuhumar cewa suna kafirta su. Idan mun duba littattafai ingantattu daga malaman da wadancan mutane suke riko da su sai mu ga abin sabanin hakan, wato maganar tana koma wa wanda yake sukan ne.

Sahihul Buhari: Kitabul Imani s 28, da Tirmizi: j 5, s 87, Mazma'uz Zawa’id: j 9, s 367, da Masnad Ahmad Bn Hambal: j 5, s 50, alfitan: j 4, s 94, da littattafai masu yawa da sanadodi ingantattu sun yi nuni da wasu siffofi na sahabbai a ranar lahira kamar haka:

•    Sun farar da bidi'o’i bayan Annabi (s.a.w)

•    Sun yi ridda bayan wucewar Annabi (s.a.w)

•    Manzon Allah (s.a.w) ya yi rayuwa tare da su

•    Za a kai su wuta, a hana Annabi (s.a.w) ganin su

Ga mai adalci shin wannan me yake nufi, mu kaddara Shi’a suna da irin wadannan ruwayoyin to me ye bambancinsu da wadannan da suke cikin littattafan da mabiya mazhabar Sunna suke tinkaho da su.

 

Tawilin Hadisai

Sai dai mabiya Sunna sun so su yi kokarin ganin sun yi tawilin hadisan ta yadda ba zasu shafi wasu mutane da suke so ba, don haka duk abin da wasu mutane suka yi na rushe sunnar Annabi (a.s) a fili, da kashe muminai, da ma halaka zuriyarsa, sai suka samo masa tawili.

Mafi muni da suka yi kokarin ganin sun fitar da kowa daga ciki sai munafukai, sun manta cewa wannan hadisin ba yana magana kan munafukai ba ne, yana magana kan na gari ne da suka canja bayan wafatin manzon Allah (s.a.w), sun kasance tare da manzon Allah (s.a.w) kuma sun yi yaki tare da shi, sun taimaka masa, amma bayansa ne suka canja, mai karatu ya koma wa hadisai sosai ya gani.

Amma munafukai ba a cewa; sun canja bayan manzon Allah (s.a.w), su tun farko Kur’ani da Sunna tun lokacin manzon Allah (s.a.w) ba su dauke su a cikin muminai ba, sun dauke mafi muni da kafirai ne, kuma su ba su yi wani abin yabo ba sai neman rushe musulunci ta kowane hali ne.

Ma'abota mazhabar Sunna duk da suna yin tawili amma abin mamaki sai ga shi suna kawo hadisai kan wasu sahabbai da wannan lafazin na ban san me zaku yi ba a bayana. Duba yadda manzon Allah yake gaya wa Abubakar halifa na farko cewa: (Ba zai nema masa gafara ba) domin bai san me zai yi ba a bayansa. Wannan ya zo a littafin Muwadda na Malik, game da ziyarar Shahidan Uhudu.

Sannan Barra dan Azib bayan an yi masa murnar cewa; ga shi zaka mutu, ka yi zama da Annabi (s.a.w), sai amsa da cewa: Ba ku san abin da muka yi ba ne bayansa. (Sahihul Buhari: Gazwatul Hudaibiyya, a Kitabu Bad'ul Khalk). Sannan Uwar muminai A’isha an nemi a binne ta tare da Annabi (s.a.w) sai ta ce a binne ta gun da aka binne matansa, domin ta farar da abubuwa masu yawa bayan manzon Allah (s.a.w), (Akdul Farid: j 4, s 231, da Majma'uz zawa’id: j 7, s 463).

Idan mun duba zamu ga babu wani munafuki a cikin wadannan kuma babu wani daga masu ridda a yakokin da aka yi da masu ridda, amma ga shi suna cewa sun canja bayan wafatin manzon Allah (s.a.w), har ma suna tsoron kada a binne su a kusa da shi. Hada da abubuwa da yawa da aka ruwaito game da Amru dan Asi, da Abubakar, da Umar yayin mutuwarsu da maganganu masu nauyi da ba zamu iya kawo su ba, saboda gudun tsawaitawa. Ga kuma abin da wasu suka yi munana a tarihi da misali daya daga cikin kisan da Khalid dan Walid ya yi wa musulmi daga cikinsu harda Malik dan Nuwaira, sannan ya kwanta da matarsa da tilasci a daren da ya kashe shi. (Dabari: j 2, s 502, Kanzul Ummal: j 3, s 132, wafayatul A'ayan: j 5, s 66, da littattafai masu yawa).

Da kuma sha'anin Mugira dan Shu'uba da Ummu Jamil, wannan kissa ce shahararriya. (Dabari: j 4, s 207, Sunanul Kubura: Baihaki; j 8, s 235).

Sannan muna ganin yadda sahabbai suka saba wa wasiyyar da Annabi (s.a.w) ya yi da ya bar wa al'ummarsa Kur'ani da Alayensa (a.s) a matsayin wadanda za a bi bayansa, kuma biyayya garesu ce zata tseratar da al'ummarsa daga bace wa tafarkinsa. Hadisin Sakalain mutawatiri ne gun dukkan al'ummar musulmi, amma wannan al'umma ta yi watsi da su bayan wafatinsa, hasali ma an kashe dukkan zuriyarsa. Kuma abin da aka yi wa 'yarsa bayan wafatinsa da 'yan kwanaki kawai ya ishi misali ga wannan al'umma.

 

Zama Tare Ya Isar?

Don haka da wannan zamu ga cewa; tafarkin da Shi’a suka bi wurin bayar da matsayi ga sahabbai wadanda su ne musulmi na farko shi ne gaskiya, domin shi ne abin da musulunci ya zo da shi. Musulunci bai ware wasu musulmi ba ya ba su garanti na duk abin da suka ga dama su yi, sannan kuma ya ware wasu ya takura su da cewa idan suka yi laifi zasu tafi wuta.

Don haka ne ma ya ba mu misalai da matar Annabi Nuhu (a.s) da matar Annabi Ludu, da dan Annabi Nuhu (a.s), da Abulahab ammin manzon Allah (s.a.w), duk zamansu tare ko kasancewarsu na jinin wadannan bayin Allah bai amfanar da su daga kare su daga azaba ba yayin da suka saba ko suka canja.

Sunna da suka nemi ganin dukkan sahabbai adalai ne alhalin sun kawo wadannan hadisai, ga kuma ayoyin Kur’ani suna karyata wannan magana tasu, ba mu san yadda zasu iya samar da mafita ga alakakan da suka fada ba. Yaya zasu fassara kisan da A’isha da Dalha da Zubair da sauran sahabbai suka yi wa Usman? Sannan kuma yaya zasu yi da kafirta Usman da A’isha ta yi, wacce fatawarta tana cikin dalilan kashe shi? Yaya zasu fassara yakar Imam Ali (a.s) da wadannan sahabbai suka yi, da kuma abin da Mu'awiya ya yi na yakarsa? Da sauran dubunnan tambayoyi da ba su da iyaka.

Mu sani musulunci ya sanya ma'auni ga tsira shi ne imani na gari, da ayyuka na gari, da mutuwa a kai. Allah ba shi da alaka ta jini da kowa koda kuwa Annabi (s.a.w) ne, hatta da Annabi (s.a.w) da zai yiwu ya canja da Allah ya azabtar da shi balle sauran mutane.

Hafiz Muhammad Sa’id

hfazah@yahoo.com

Haidar Center For Islamic Propagation

www.hikima.org

Monday, Nobember 02, 2009

Ƙara sabon ra'ayi