Samuwar Aljanu

Samuwar Aljanu

Shin Akwai Wasu Halittu Da Ake Kira Aljanu? Ko Kuwa Abin Da Muke Ji Game Da Aljanu Camfi Ne?

Babu wani sabani tsakanin musulmi kan cewa; akwai aljanu, wannan kuwa saboda fadin Allah madaukaki cewa: “Ban halicci mutum da aljan ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da fadinsa: “Kuma ya halicci mutum daga wani tartsatsin wuta”. Surar Rahaman: 55. Da fadinsa: “Kuma aljan tun farko mun halicce shi daga wuta mai radadi”. Surar Hijir: 15. Hada da cewa akwai sura guda wacce ake kiran ta da surar “al-Jinn”, hada da ayoyi masu yawa da suka zo a cikin wurare masu yawa suna maganar samuwar “Aljanu”.

Ubangiji madaukaki yana cewa: “Kuma aka tayar wa Sulaiman rundunarsa na daga aljanu da mutane da tsuntsaye ana kange su”. Surar Namli: 17. Da fadinsa: “Yayin da muka juya wasu aljanu zuwa gareka suna sauraron Kur'ani, yayin da suka zo masa sai suka ce; Ku saurara…”. Surar Ahkaf: 29. Da fadinsa: “Yayin da muka hukunta masa mutuwa babu wani abu da ya nuna musu mutuwarsa sai wata dabba… yayin da ya fadi sai aljanu suka gane cewa; da sun san gaibi da ba su zauna cikin azaba mai radadi ba”. Surar Saba': 14.

Don haka samun alajnu wani abu ne da muke yin imani da shi koda kuwa ba ma ganin su, ba na sanin su. Sai dai mutane sun yawaita magana a kansu har sai da aka kawo camfe-camfe game da su, don haka sai a koma wa littafin Allah da sunnar manzonsa domin sanin su, da sanin abin da zai yiwu a sani game da su. Sannan muna iya ganin wasu ayoyin yadda suka yi nuni da cewa; aljanu suna iya tasiri a kan rayuwar mutum ta hanyar amfanuwa ko cutuwa.

Wasu ruwayoyi sun zo suna masu nuni da cewa; aljansu suna iya cutar da mutane kamar yadda zamu iya gani.

Imam sadik (a.s) yana cewa: “An ambaci aljanu da wannan suna ne, domin suna nisantar gani sai dai idan sun so a gan su, saboda Allah ya sanya musu ikon yin hakan…”. Biharul Anwar: j 60, Shafi: 313. Imam Ali (a.s) yana cewa: “Idan dayanku ya tube tufafinsa, to ya ambaci Allah domin kada aljanu su sanya, domin idan bai ambaci Allah ba, to sai aljanu su sanya har safiya”. Biharul Anwar: j 63, Shafi: 74.

Babu sabani tsakanin al’ummar musulmi cewa aljanu wasu halittu ne masu jiki mai taushi wanda ana iya ganin su wani lokaci, wasu lokaci kuwa ba a iya ganin su, suna da motsi mai sauri da ikon canja kamanninsu iri-iri, da karfin yin wasu ayyuka masu karfi…, kuma Allah yana yin su da shakaloli da surori iri-iri bisa maslaha,  kamar yadda sayyid murtadha yake cewa. Biharul Anwar: j 63, Shafi: 283.

Kuma Allam Diba’diba'i ya kafafa hakan, ya kuma kara da cewa; suna rayuwa, suna mutuwa, ana tashinsu ranar kiyama. Tafsirul Mizan: j 12, S; 158.

Amma game da cewa shin aljansu suna cutar da mutane? Wannan magana haka take, har ma akwai surar Nasi wacce ta sauka kuma a cikinta akwai ambaton neman tsari daga aljanu, kamar haka:

1. Ka ce ina neman tsarin ubangijin mutane. 2. Mamallakin mutane. 3. Abin bautar mutane. 4. Daga sharrin mai waswasi mai boyewa. 5. Wanda yake sanya waswasi a cikin zukatan mutane. 6. Daga aljanu da mutane. Surar Nasi: 1-6.

Da kuma addu’a da take cewa: “Kuma ina neman tsarinka daga Fasikan aljanu da na mutane…” Fikihur Ridha: 139, da sauran addu’o'i da suka zo game da hakan. Duba Misbahul Mutahajjidi: 110. Don haka; da ba su da cutarwa da zasu iya yi wa mutum, da ba a samu wannan nassosi na shari’a ba game da su.

Amma kuma batun cewa; yaya zamu kubuta daga sharrinsu to sai mu ce: Akwai addu’o'i daga surorin Kur'ani da kuma Ruwayoyi masu yawa kan yadda za a samu tsari daga sharrinsu da cutarwarsu, kamar karanta Kur'ani mai girma, da basmala, da surar Aljanu, da Ayatul Kursiyyu; Bakara: 255-257, da sauran addu’o'i da suka zo game da hakan. Fikihur Ridha: 343.

 Don haka aljanu suna da tashin kiyama, da hisabi, da ma’auni, da lada, da zunubi, da shiga aljanna, da wuta, kamar yadda muke da shi, dalilin hakan kuwa fadin Allah madaukaki: “Kuma mu akwai musulmi a cikinmu kuma akwai masu kaucewa, duk wanda ya musulunta to wadannan sun yi katarin shiriya…”. Surar Jinni: 14-15.

 Kuma wasu ayoyin sun nuna ikonsu ga hawa sama da satar sirrin maganganun sama, sai dai an hana su hakan. Kamar fadinsa: “Kuma mu mun kasance muna zama a wasu wurare a cikinta, amma duk wanda ya yi sauraro yanzu zai samu tauraro mai dako”. Surar Jinni: 9. Kamar yadda a cikinsu akwai muminai da kafirai. Surar Jinni: 11. Kuma suna kokarin ganin sun halakar da wasu mutane ta hanyar ba su wasu bayanai da suka boyu ga mutane, kuma suna da mata da maza. Surar Jinni: 6. Kuma suna iya yin ayyuka masu wahala masu girman gaske cikin sauri a lokaci kankani. Surar Namli: 39, da Surar Saba': 12-13.

A takaice muna iya cewa; aljanu wasu halittu ne da ba a ganin su, kuma mutum ba ya iya ganin su sai idan sun ga damar hakan sun so, kuma Allah (s.w.t) ya halicce su kafin ya halicci mutum, kuma ya aika musu annabawa, su kamar mutane ne da suke da mazhabobi da addinai daban-daban. A cikinsu akwai yahudawa, da kiristoci, da musulmi, a cikinsu akwai masu yin imani da Allah, da manzonsa, da imamai, kamar yadda wasunsu sukan zo wurin Annabi (s.a.w) da imamai (a.s) a lokutansu suna tambaya domin su san addininsu da hukunce-hukunce, kuma suna yi wa Annabi (a.s) hidima, suna biyayya ga umarninsa idan ya umarce su.

Sai dai yana da kyau mu kula da wani bayani muhimmi cewa; ba zai yiwu ba komai a jingina wa aljanu a rayuwar mutum, wani lokaci yana iya kasncewa saboda takaitawar mutum da rashin kulawarsa ne, don haka yana da kyau mutune su kula don kada su fada cikin camfi da surkulle, kamar yadda a bisa hukuncin shari’a bai halatta ba a koma wa wanda yake da’awar mu’amala da aljanu domin warware matsalolin mutane ko yin wasu abubuwan mamaki. Don haka tun farko ya kamata ne a yi wasu abubuwa kamar haka:

• Sanin Allah da addininsa, da sakonsa

• Kyakkyawan tsari domin fita daga matsaloli

• Aiki da kokari da nufi da gaske

• Amfani da zikirori, da addu’o’i

• Yawaita karanta Kur'ani

• Nisantar waswasi da makircin shedan

• Nisantar masu camfi da surkulle

• Nisantar masu zuwa wurin masu da'awar Aljanu

• Yakar jahilci da fadada tunani da ilimi

A nahiyarmu ta Afurka wannan bala'i ne da ya mamaye al'umma, ta yadda akwai mutanen da komai sai su mayar da shi zuwa ga aljanu. Wani lokacin akan samu haduwar jijiyoyi a jikin mutum ta yadda zasu rika ba shi wani sako na musamman, kamar su ba shi ya rika gane-ganen wasu halittu, ko wasu dabbobi, ko wasu mutane sakamakon haduwar wadannan jijiyoyin. Wani lokaci kuma akan samu malaria, ko ciwon Olsa, ko kuma cikon zazzabi mai zafi ya sanya mutun ganin wasu abubuwan suna gilmawa, wani lokaci wani yakan hadu da sharrin basir ta yadda zai ga kamar wuta ta kama daki, ko wani abu ya wuce da gudu.

Ya zo cewa; Kazanta tana da tasiri matuka wurin samun matattarar aljanu musamman shedanunsu, don haka ne ma aka yi umarni da ambaton Allah yayin shiga bayan gida, da wuraren da suke da kazanta, kuma sanannan lamari ne cewa; al'ummarmu tana tattare da wuraren kazanta, da yin bayan gida a kan hanyoyi da tituna, da yin fitsari a ko'ina, sannan wannan yana iya tara cututtuka marasa sababi, wadanda sukan kama mutane su galabaitar da su, su sanya su surutai marasa kan gado, to irin wadannan cututtukan ma al'ummarmu sun jingina su da aljanu.

Dukkan wadannan abubuwan da suke faruwa sakamakon irin wadannan cututtukan sai al'ummarmu ta mayar da su zuwa ga aljanu. Akwai wani lokacin da zaka samu kwalara, ko annoba, ko cutar shan-inna, da makamancinta ta gindaya wata makaranta ko wani gari ta kama mutane, suna ta surutai, a nan ma sai ka ga an ce ai aljanu ne, har ma wani yakan ce; tayiwu an taka musu 'ya'ya ko kwarya ne. Yana da kyau a samu masu ilimi da zasu rika wayar da kan mutanenmu, domin su nisanci duk wani camfi da jahilci, game da lamarin aljanu.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

Haidar Center For Islamic Propagation

Thursday, September 10, 2009

Ƙara sabon ra'ayi