Hakkokin Makusanta

Hakkokin Makusanta
Hakkin Matar Aure: "Kuma hakkin wacce kake kula da ita da mallakar aure shi ne ka san cewa Allah ya sanya ta mazauni, wurin hutu, wurin nutsuwa gareka, da kariya, kuma haka nan ya wajabta wa kowannenku gode wa Allah game da samun abokin zamansa, ya san cewa wannan ni'ima ce tasa daga gareshi, kuma ya wajaba ya kyautata zaman ni'imar Allah ya girmama ta ya tausasa mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi karfi, biyayyarta gareka ta fi lizimtuwa cikin abin da ta so da wanda ta ki matukar ba sabo ba ne, sannan tana da hakkin tausayawa da debe kewa, da wurin zama gareta, biyan bukatar jin dadin da babu wakawa da ita, wannan kuwa abu ne mai girma, Babu karfi sai da Allah".

Hakkin Bawa: "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka ne na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halitta masa ji ko gani ba, ba ka gudanar masa da arzikinsa ba, sai dai Allah ne ya isar maka da dukkan wannan da wanda ya hore maka shi ya ba ka amanarsa, ya ba ka ajiyarsa, domin ka kare shi, ka yi masa halayen da Allah yake yi (wa bayinsa), sai ka ciyar da shi daga abin da kake ci, ka sanya masa abin da kake sanyawa, kada ka dora masa abin da ba zai iya ba, idan kuwa ka ki shi, to sai ka (mayar da lamarinka) zuwa Allah ka bar shi (ka rabu da shi), ka canja wani da shi, kada ka azabtar da halittar Allah, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Uwa: "Ka sani hakkin babarka cewa ita ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da jinta da ganinta, hannunta da kafarta, gashinta da fuskarta, da dukkan gabobinta, tana mai murna da farin ciki, tana mai jure duk wani abin kinta, da zoginta, da nauyinta, da bakin cikinta, har dai hannun kudura ya cire ka daga gareta, kuma ta fitar da kai zuwa duniya, sai ta yarda da koshinka ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai ita kuwa ta yi kishi, ta sanya ka inuwa ita kuwa ta sha rana, ta ni'imantar da kai da wahalarta, da jiyar da kai dadin bacci da rashin baccinta, cikinta ya kasance wurin zama gareka, dakinta ya zamanto matattara gareka, kuma nononta ya zama salkar sha gunka, ranta kuma kariya ne gareka, tana shan zafin duniya da sanyinta don kare ka, to sai ka gode mata a kan wannan sai dai ba zaka iya ba sai da taimakon Allah da dacewarsa".

Hakkin Uba: "Kuma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan, babu karfi sai da Allah".

Hakkin Da: "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alherinsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa ga Allah game da kai da kanka, to kai abin ba wa lada ne kan hakan kuma abin yi wa ukuba (idan ka cutar da shi ko ka yi sakacin tarbiyyarsa). To sai ka yi aiki cikin umarninsa irin aikin mai kawata aikinsa ta hanyar kyautata tarbiyyarsa tun a nan duniya, aikin mai yanke uzuri wurin ubangijinsa da abin da yake tsakaninsa da shi ta hanyar kyautata kula da shi da karba masa daga gareshi, kuma babu karfi sai da Allah".

Hakkin Dan'uwa: "Kuma Hakkin Dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi ne hannunka da kake shimfidawa, kuma bayanka da kake jingina da shi, kuma daukakarka da kake dogaro da ita, kuma karfinka da kake ijewa da shi, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko ka sanya shi tanadi domin zaluntar halittar Allah, kuma kada ka bar taimakonsa da agaza masa kan makiyinsa, da shiga tsakaninsa da shaidancinsa, da ba shi nasiha, da fuskantuwa zuwa gareshi a tafarkin Allah, to idan ya karkatu zuwa ga ubangijinsa, (Ubangijin) ya kyautata amsa masa, in kuwa ba haka ba, to Allah ya kasance shi ne ya fi zabuwa gunka, kuma mafi girma gareka fiye da shi".

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011

Ƙara sabon ra'ayi