Hakkokin Al'umma
Hakkokin Al'umma
Hakkin Jama'a: "Amma hakkin jama'ar da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda karfinka a kansu, kuma ba komai ba ne ya sanya ka mahallin matsayin mai kula da su sai rauninsu da kaskantuwarsu. Babu wani abu da ya cancanci wanda rauninsa da kaskancinsa ya mayar da shi jama'arka, hukuncinka ya kasance mai zartuwa ne a kansa, ya kasance ba ya iya kare kansa daga gareka da wani karfi ko dubara, kuma ba ya iya samun mai taimako kan abin da ya fi karfinsa daga gareka sai Allah, in ban da ka yi masa tausayi da rahama da kariya da tausasawa. Kuma babu wani abu da ya fi cancanta gunka idan ka san abin da Allah ya ba ka na buwaya da karfi da ka yi rinjaye da shi, in ba ka kasance mai godiya ga Allah ba, wanda kuwa ya gode wa Allah, to zai ba shi wata baiwar abin da ya yi masa ni'imarsa da shi, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ilimin Jama'a: "Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, wanda ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba ka na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa, mai hakuri mai neman lada, (kamar ubangida ne mai dukiyar bayi a hannunsa) wanda idan ya ga wata bukata sai ya biya masa ita daga dukiyar da take hannunsa, to (idan kai ma ka biya bukatun masu neman ilimi) ka kasance mai shiryarwa, kuma ka kasance abin buri da yarda. Idan kuwa ba haka ba, to sai ka zama mai ha'inci gareshi, kuma mai zalunci ga bayinsa, da keta huruminsa da na waninsa".
Hakkin Ilimin Jama'a: (Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, wanda ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa, mai hakuri mai neman lada, (kamar ubangida ne mai dukiyar bayi hannunsa) wanda idan ya ga wata bukata sai ya biya masu ita daga dukiyar da take hannunsa, to (idan kai ma ka biya bukatun masu neman ilimi) ka kasance mai shiryarwa, kuma ka kasance abin buri da yarda. Idan kuwa ba haka ba, to sai ka zama mai ha'inci gareshi -Allah- kuma mai zalunci ga bayinsa, kuma ya hau kan Allah ya cire maka ilimi da kwarjininsa, ya shafe sonka daga zukata).
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
www.hikima.org
Saturday, June 04, 2011
Ƙara sabon ra'ayi