Hakkin Jama'ar Kasa na Ilimi
Hakkin Jama'ar Kasa na Ilimi
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, kuma ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa, mai hakuri mai neman lada, wanda idan ya ga wata bukata sai ya biya masa ita daga dukiyar da take hannunsa, to ka kasance mai shiryarwa, kuma ka kasance abin buri da yarda. Idan kuwa ba haka ba, to sai ka zama mai ha'inci gareshi -Allah- kuma mai zalunci ga bayinsa, kuma ya hau kan Allah ya cire maka ilimi da kwarjininsa, ya shafe sonka daga zukata".
Hikima ta 139.
Bahasin ilimi ya fi dukiya daga nahujul balaga:
Al'umma maras ilimi ba yadda za a yi ta ci gaba har abada, don haka ne al'ummar da take da karancin ilimi sai ta kasance wawiyar al'umma maras wayewa, ta yadda kowane abu sai ya zama mai ban tsoro gunta.
Sai dai kada mu manta cewa; al'ummarmu tana fama da mafi yawan talauci ne saboda ba da yarenta take yin ilimi ba, neman kwarewa kan wasu yarurruka kamar larabci ko turanci kawai ya isa ya cinye kusan rabin rayuwar al'ummarmu domin ta samu wasilar da zata samu ilimi da shi. Da al'ummarmu zata yarda ta yi juyin ilimi ta yadda iliminta zai kasance da yarenta da ta samu ci gaban mai ban mamaki cikin lokaci kankani, kuma turai sun kai ga ilimi ne yayin da suka samu yin hakan!.
Da yawa matsalolin da ake fama da su na rashin daidaito tsakanin al'ummar kasa, da arziki zai ko rashin tsarin albashi da ya sanya ma'aikata zama marasa gaskiya masu karbar cin hanci, ko satar dukiyar al'umma, ko rashin tsafta da gyaran hanya, da kwatami, da hanyar ruwa, da hakkin kotu, da asibiti (lafiya), da rashin tsaro, da na magani, da batun fagen 'yancin hakkin namiji ko mace, duk ana iya warware su da ilimi da tunani mai kyau.
Wannan duniyar da lahira duka sun tsayu kan ginshikai muhimmai ne wanda mafi muhimmancinsu shi ne ilimi: Imam Ali (a.s) ya ce da Jabir dan Abdullahi Al'ansari: "Ya kai Jabir! Addini ya tsayu kan abubuwa hudu ne: Malami mai aiki da iliminsa, da jahilin da ya dage wurin neman sani, da mai kyauta da ba ya rowa da dukiyarsa, da talakan da ba ya sanar da lahirarsa da duniyarsa, idan malami ya tozarta iliminsa, sai jahili ya kame ya ki neman sani, idan mai kudi ya yi rowa da dukiyarsa sai talaka ya sayar da lahirarsa da duniyarsa".
Ya Jabiru, wanda ni'imomin Allah suka yawaita gareshi bukatun mutane zasu yawaita gunsa, kuma duk wanda ya yi abin da Allah yake so da ita, to zai sanya ta mai wanzuwa da dawwama, amma duk wanda bai tsayar da abin da Allah yake so da ita ba, to zai sanya ta mai gushewa da karewa .
Da ilimin ne za a samu canji gun dan Adam: Mutum halitta ce mai samun canje-canje da Allah madaukaki ya samar a cikin samammu, shi halitta ne da yake iya kasancewa mafi kamalar samammu, ko kuma ya zamanto mafi muninsu.
Wannan murdadden samamme mai wuyar sha'ani yakan samu canje-canje a cikin rayuwar duniya, sai wannan canjin da yake haifarwa ya samar da sauyi mai ba da mamaki a cikin hukunce-hukuncen mahaliccinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa a cikin daidaikun mutane ko kuma a cikin jama'a gaba daya a dunkule. Don haka ne ma sunnar Allah ta samar da canji a cikin bayinsa take sauyawa daidai gwargwadon samun canjin da ake samu a cikin dan Adam da halayensa. Wannan sunnar ta Allah ba ta canjawa har abada a nau'in yanayi guda a kowane zamani, amma tana canjawa da canjawar yanayin zamani ne. "Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake garesu…". Ra'ad: 11. "Wannan domin Allah bai kasance mai canja wata ni'ima da ya yi wa wasu mutane ba har sai sun canja abin da yake garesu…". Amfal: 53. Sai a samu rahama idan mutane suka kiyaye lamarin Allah na riko da dokokin sabuban halittu da abubuwan da ya hore masu, sai kuma a samu azaba idan aka yi sakaci da abin da Allah madaukaki ya huwace wa bayinsa.
Idan mutane a bisa misali; suka yi riko da ni'imar da Allah ya ba su ta kasa mai kyau, da ruwa mai dadi, da iska mai lafiya, suka yi riko da kayan aiki da ya hore musu kamar fatanya ko kuma garma, ko kuma kayan noma na zamani, suka yi amfani da taki ko na gargajiya ko na zamani, sannan kuma suka yi amfani da karfin dan Adam da ya ba shi na iya yin aiki, da kuma lokacin da ya fi dacewa a yi noma kamar damina, ko kuma amfani da tabki wurin noman rani, sannan sai suka yi amfani da iri, ko dashen shuka domin samar da abinci da 'ya'yan itaciya da sauran kayan marmari. Sannan suka himmantu wurin ganin sun kula da shukan nan da ba ta kariya daga duk wani abu da zai kawo mata hari mai hadari gareta kamar ciyayi da dabbobi, da ma mutane masu kiwo da sukan iya lalata ta, da kuma barayi da sukan iya satar kayan gona!
To wadannan sun yi riko da sabuban ilimi a rayuwa da Allah (s.w.t) ya hore musu, kuma sunnar Allah a nan ta wajabta musu samun nasara kan abin da suka sanya gaba, sai yalwa da abinci su samu a cikin wannan al'umma, babu wata yunwa da zata kunno musu kai, babu wani bala'in rashin abin sawa a baka ko sha da zai durfafe su. Sai dai idan akwai wani bangare na wani lamari kamar na alfahasha da ba su kiyaye ba, kuma Allah ya so ya jarrabe su da wannan, sai ya saukar musu da bala'i kamar na fari (rashin ruwan sama da bushewar kasa), ko kuma fari (kwarin fari masu kai hari kan shuka). Amma shi ma wannan yana magani; idan abin ya shafi mummunan halaye ne to sai su yi ta yin istigfari, idan kuwa ya shafi kamar kwari ne sai su hada biyu; suna istigfari suna kuma feshin maganin kwari, ta jirgin sama ne ko kuwa!?
A kowane fage wannan sunnar ta Allah tana da muhimmanci matuka, domin ita ce take gudana kuma take iko da kowane karfi, babu wani karfi da yake sama da ita, babu wani iko da ya isa ya shallake ta, babu wani wayo da ya isa ketare ta, babu wata dubara da ta isa ta kauce mata. Abin da ya rage abu guda ne, samar da yanayi da zai iya samar da sunna ta faru daidai gwargwadon yanayin, sai yanayin rahama ya samu idan an yi riko da sabubban rayuwa a daidai, sai kuma yanayin bala'i ya faru idan aka yi riko da su ba daidai ba.
Muhammad Bello yana gaya min cewa; akwai wani lokaci tsakanin 1996-1998 idan ban manta ba, da Jami'ar A.B.U Zaria ta kasance kamar wani dausayi mani'imci, aka hana kazanta da zubar da datti, aka sanya dokoki mai tsanani, sannan aka kyautata kayan rayuwa. Ya ce: Sai ga Jami'a ta koma kamar wani dausayin ni'ima mai dadi, da walwala da shakatawa, iskar ni'ima kamar ta sanyin safiya tana ratsawa! Wurin ya kasance wurin hutu ne ga masu son shakatawa da hole rayuwarsu! Kamar dai ka ce ba a Nigeria wurin yake ba!
Dan Adam ke nan! haka Allah ya gindaya masa, idan ya yi daidai sai ya ga daidai, idan ya saba sai ga ba dadi! Idan ya yi tsafta sai ya ga lafiya, idan ya yi kazanta sai ya ga cuta! Idan ya yi ilimi sai ya mallaki duniya ma, idan ya yi jahilci ko jaki sai dai ya yi masa gori! Wannan mutunci da Allah ya yi mana shi an wulakanta shi a wasu wurare, yayin da zaka ga mutum yana halaye kamar na dabba!. Wannan mutumin mai daraja da zai shiga aljanna, shi ne dai yake kuma fadowa kasa warwas ya gangara wuta!
Idan ba mu yi nisa ba; ba na tsammanin a cikinmu babu wanda bai san labarin mutumin da ya ga wata mata mai kyau ba, sai ya rika cewa da abokinsa kai! Allah ya hore mana mu karo aure! Amma da ta iso kusa da shi sai suka ga ashe matarsa ce! Ahe sai idan zata fita unguwa ne take cin ado!
Babu wanda bai san yadda idan faransawa sun dibi fulanin daji sun kai su Faransa sun dawo da su ake manta cewa; wadannan matan ne da ake kyamar irinsu saboda sun rayu a wadannan yankuna namu!
Babu wanda yake rashin takaici idan ya ji labarin wasu Yorubawa da aka kai Tehran a babban birnin Iran 1997-8 suka rika bude wandunansu a fili suna fitar da azzakarinsu suna yin fitsari a kan fulawowin da ake takama da su alhalin ga ban daki da ruwa da komai!
Babu wanda ba zai ji haushi ba idan ya ji labarin yadda wasu 'yan Afrika su biyu suka zaro al'aurarsu a bakin Titin Bajak da yake birin Kum a gaban Jami'ar Imam Khomain a 2007, suna yin fitsari a cikin ruwan da yake gudana! Ihun da mutanen da suke wucewa suke yi domin ba su taba ganin hakan ba a rayuwarsu wai sai ma ya ba su haushi, wai suna gaya wa wani dalibi daga Ghana cewa; wai don muna fitsari a nan sai kawai mutane suna yi mana kuwwa-kuwwa!
Kuma babu wani wanda ba zai ji haushi ba idan ya ga yadda mai gadi ya hana wani wanda ya matsu da bayan gida shiga bandaki saboda kawai ba dan makarantar ba ne!. Domin wannan yana nuna karancin mutunta dan Adam a fili!.
Haka dan Adam yake! Idan ya mutunta kansa sai Allah ya mutunta shi, idan kuwa ya ki sai ya ga ba daidai ba! wannan ciwo ne da ya yi mana yawa har ya kashe al'ummunmu, sai muka taso al'umma mai yawan jahiltar kawukanmu, mai yawan munanan halaye, mai yawan son kanta, mai yawan neman ta kai abin da ba ta shirya masa ba, mai yawan kazanta da rashin tsafta!.
A wani bangaren kuma mai matacciyar zuciya, da take ganin ba zata iya ba wa kanta mafita ba, har ma da yawa sun sallama wa abin da suka kira da kaddara! Sai dai mafi munin duka da aka sha, shi ne ganin da wasu suke yi wa wannan yanayi a matsayin daidai!. Jama'a ya kamata mu san cewa; Kur'ani da sunnar manzon Allah babban abin koyi ne, ma'aikin Allah da Ahlul Bati (a.s) sun yi a aikace, sun nuna mana misalin da ya kamata ya kasance ga dan Adam a rayuwa.
Yaya duniya zata kasance da manzon Allah (s.a.w) bai zo da canji ba?! ko kuwa ya ya kake tsammanin halin da ba Banu Isra'ila zasu kasance da Musa (a.s) bai kwace su daga hannun Fir'auna ba!? Yaya halin Banu Isra'il zai kasance da Isa dan Maryam bai halarto ba? yaya kuwa kake tsammanin yammacin duniya a yau ba don Sabuwar haihuwa (juyin kasahen Turai) ba, sakamakon canjin nan na juyin juya halin da ya faru cikinsu bugu da kari kuma ga na Faransa! Yaya kake tsammanin daulolin Afurka ba don zuwan turawa ba! yaya kake tsammanin wanzuwar masarautun da Gurguzu ya mamaye ba don zuwansa ba? yaya kasar Sin zata kasance ba don motsin jagora Moi ba? yaya kuwa yankunan Nijeria zasu kasance a yau ba don mamayar mallaka da hade kudancinta da arawacinta ba?!
Wadannan duk wasu misalai ne da zasu iya nuni a fili yake cewa; Dan Adam wani halitta ne da idan ya canja sai a canja masa yanayin da ya zaba! Daidai canjin da ya yi daidai sakamakon da zai faru a duniya, wannan kuwa yana iya kasance na kwarai ko maras kyau da amfani, yana iya kasance na ilimi ko jahilci.
Muna iya ganin yadda ilimin dan Adam a yau ya canja komai na duniya, da ya yarda da jahilcinsa da bai kai wannan matsayin ba, a nan muna iya ganin canji yana iya kasancewa mai kyau ko maras kyau. A matsayinka na dan Adam mai wannan baiwar ta Allah wane tunani ka yi domin samar da canji mai kyau cikin al'ummarka!? Wane yakin ne ka yi da ranka domin samun canji a halayenka? Wane kokari kake yi domin ganin sauyi a cikin gidanku, da unguwarku, ko garinku? Ka yi tunani kai mutum cewa; kana da ikon canja komai, kada lalacin tunani ya sanya ka yanke kauna!.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Saturday, April 30, 2011
Ƙara sabon ra'ayi