Hakkin Ji

Hakkin Ji
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi daga giba -yi da
wani-, da jin abin da bai halatta a ji ba, da tsarkake shi daga sanya shi hanyar zuwa ga
zuciya, sai dai idan wata magana ce mai kima da zata farar da wani alheri a cikin zuciyarka,
ko kuma zaka samu wata dabi'a mai daraja da girma da ita, domin shi ji shi ne kofar magana
zuwa ga zuciya wanda yake kaiwa ga fahimtar abubuwa daban-daban na alheri da na sharri. Babu
kuma karfi sai da Allah".
Mariskai su ne mafi muhimmancin hanyoyin da mutum yake samun alaka da wajensa, kuma da su ne
yake iya fahimtar da waninsa abin da ya kudurce ko kuma ya san abin da waninsa ya kudurce,
don haka idan aka toshe su daga mutum wannan yana nufin an toshe masa hanyoyin samuwar
ilimi. Sai dai duk da haka da wannan muhimmancin da suke da shi, zamu iya ganin suna da
shugaba wanda suke rusana masa gaba daya, wanda idan babu shi to zasu rasa kimarsu, wanna
kuwa shi ne hankali da Allah madaukaki ya ba wa mutum.
Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da wannan lamarin mai muhimmanci yayin da Disani (shi wani mutum
ne da bai yi imani da samuwar Ubangiji ba) ya ce masa: Nuna mini abin bautata? Sai imam
Sadik (a.s) ya riki wani kwai, sai ya ce: Wannan wata katanga ce rufaffiya tana da fata mai
kauri, kuma a karshita akwai wata fata siririya, kuma akwai wani ruwan azurfa karkashi
siririyar fatar, da kuwa wani ruwan zinariya, sannan wannan ruwan zinariyar ba ya cakuda da
ruwan azurfar, kuma waccan ba ta cakuda da wannan, wani abu bai shiga cikinta ba, kuwa babu
wani abu da ya fita daga cikinta, ba a sani ba cewa namiji aka halitta ko mace, sannan sai
ta tsage ga -tsuntsu- kamar Dawisu, shin kana ganin akwai wanda ya shirya hakan?
Sai Disani ya ce: Mu ba ma imani sai da abin da muka riska da idonmu, ko ji, ko shaka, ko
dandano, ko tabawa. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Ka ambaci mariskai, su kuwa ba sa
amfanar komai sai da hankali. (Sharhin Risalatul Hukuk: s; 35).
Da wannan lamarin muna iya fahimtar kimar hankali ga wadannan mariskai, domin idan sun yi
kuskure sukan koma wa hankali domin su tantance, idan kuwa babu hankali to ba su da kima sai
riskar abubuwa, don haka dan Adam zai kasance a cikin toshewar ilimi da rashin sanin
gaskiya, da kuma kasa tantancewa.
Wannan yana iya tuna mana yadda Amru dan Ubaid ya kasance tare da Hisham, yayin da Hisham
dalibin imam Sadik (a.s) ya yi masa kakat game da cewa wadannan gabobin da muke da su ba su
da kima sai da hankali. Asalin wannan tattaunawar ta kasance ne yayin da Amru dan Ubaid ya
yi musun wajabcin jagora ga al'umma, shi kuwa Hisham ya kawo tilascin samar da jagora ga
al'umma daga Allah wanda zai daidaita al'umma idan ta karkace.
Hisham ya ce da Amru: Ina da tambaya. Sai ya ce: Kawo ta. Sai na ce: Kana da idanu? Ya ce:
I. Na ce: Me kake gani da shi? Sai ya ce: Launuka da mutane. Sai na ce: Kana da hanci? Ya
ce: I. Na ce: Me kake da shi? Ya ce: Ina shaka da shi. Sai ya ce: Kana da baki? Ya ce: I.
Sai na ce: Me kake da shi? Sai ya ce: Ina dandana abinci. Sai ya ce: Kana da zuciya? Sai ya
ce: I. Sai na ce: Me kake da ita? Sai ya ce: Ina tantance dukkan abin da ya zo wa gabobi ne
don sanin gaskiya da shi. Sai na ce: Shin ba sa wadatuwa daga zuciya? Sai ya ce: I. Sai na
ce: Yaya haka bayan lafiyarsu lau? Sai ya ce: Ya kai dana! Gabobi -mariskai- idan suka yi
kokwanto cikin wani abu da suka shaka, ko suka gani, ko suka dandana, sai su mayar da shi
zuwa ga zuciya, sai su samu yakini, sai kokwanto ya lalace. Sai ya ce: Ke nan Allah ya sanya
zuciya ne domin -maganin- kokwanton gabobi? Sai ya ce: I. sai na ce: Ke nan dole ne a samu
zuciya domin idan ba haka ba gabobi ba zasu samu yakini ba? Ya ce: I.
Sai na ce: Ya kai Marwan Allah bai bar wata gaba ba sai da ya sanya mata jagora da zai gyara
mai kyau, ya kore shakkun da take da shi, sannan sai ya bar halitta dukkansu cikin dimuwa,
da kokwantonsu, da sabaninsu, bai sanya musu wani Imami jagora ba da zasu koma masa yayin
shakkunnsu dimuwarsu, amma sai ya sanya wa gabobinka Imami makoma jagora da zasu koma masa
yayin dimuwarka da kokwantonka!. (Nahajul Iman: Ibn Jubair, s 161. Amali: Saduk, s 472.
Ihtijaj: Dabarasi, s 367).
Muhimmancin ji ba karamin abu ba ne, hatta da 'yan wuta suna cewa: "… da mun kasance muna
ji, ko muna hankaltuwa da ba mu kasnace daga cikin 'yan Sa'ira ba". (Mulk: ). Sai suka yi
furuci da cewa rashin kiyaye ji shi ne ya kai su wuta, domin sun mika jin su ga dukkan
shirme da sabon Allah, sai suka mika shi ga masu bautar wani Allah, suka cika musu
kwakwalensu da shirka da bautar waninsa.
Da sun saurari manzanni da annabawan Allah madaukaki, da ba su fada cikin wannan halakar ba,
amma sai suka ki, suka toshe kunnuwansu, suka ki saurara. Wannan lamarin kamar yadda ya faru
a lokacin da Annabi (s.a.w) yake kira, da can kafinsa ya faru ga mutanen Annabi Nuhu (a.s)
yayin da yake kiran su zuwa ga Allah (s.w.t), amma sai su sanya tufafinsu su rufe
kunnuwansu, su yi girman kai ga barin jin sa.
Ji yana da cikin ni'imomin da Allah madaukaki ya yi mana a matsayin bayinsa, ya sanya shi
kofa ce ta kaiwa zuwa ga cuciya, don haka ne da ji ne ake hankaltar abubuwa a fahimce su, da
ji ne muke samun ilimi, sai dai da hankali ne muke tacewa. Duk wata magana zata bi ta cikin
kunne, amma ba dukkan magana ba ce karbabbiya sai sahihiya, don haka ne ya hau kanmu mu yi
wa dukkan wata magana tankade da rairaya, idan mun ga sahihiya ce sai mu karba, idan kuwa ba
haka ba sai mu ajiye ta.
Ya wajaba a kiyaye ji daga sauraron haram da jita-jita musamman ga mai maganar da an san ba
ta da tushe, da yawa mutanen da aka saurare su maganarsu ta zama bala'i ga al'umma da mai
sauraron. Haka nan ana son sauraron magana mai amfani kamar ta Ilimi da sauraron karatun
Kur'ani (musamman ga mai ciki), kuma mai magana da kai yana da hakkin ka saurare shi idan ya
gama maganarsa sai ka yi taka.
Domin amfani da kunne amfani mai inganci sai mu yi kokarin kiyaye abin da zamu ji, sai mu
himmatu da jin karatun Kur'ani da hadisan Annabi (s.a.w), wasu sukan mance da cewa akwai
Kur'ani a rayuwarsu. Mu kare kanmu daga jin mummuna kamar yadda muke kare kanmu daga furta
mummuna, domin jin mummuna yana shiga hankali sai ya yi masa mummunan tasiri.
Mu kiyayi satar jin maganar mutane ta bayan bango da garu, da kofofi ko taga, wannan yana
daga cikin ha'inci da mummunan ladabi, kuma yana cikin leken sirrin mutane da yake haram.
Idan muka ji wani yana yin zancen wani to kada mu yi tarayya da shi a cikin wannan, sai dai
idan ya kasance wani abu ne na maslahar al'umma da ta kama sai an yi wannan maganar, ko kuma
ya kasance laifin da shi wancan mutumin yake yi a fili yake yin sa.
Kada mutum ya kasance shi ne mabudin sharri ta hanyar dauko maganganun wasu mutane yana gaya
wa wasu domin haifar da fitina da Allah ya hana ta. Sannan ba ya daga cikin ladabi mutum ya
yi ihu a cikin kunnen wani, ko ya hura masa kunne, ko ya doke shi a kunne, ko ya ja masa
kunne, sai dai babu laifi a huda kunnen 'yan mata domin sanya kayan ado kamar dan kunne.
Mu nisanci kade-kade da jin su, domin koda ya kasance yana yi mana amfani ta wani bangaren,
amma yana sanya shagaltuwa daga tunani, da bata lokaci, da kashe karfinmu, da daidaita mana
tunani, da raba mana hankali, da karanta mana lafiya ta hanyar dukan kwakwalmu da sauti daya
mai maimaici da yawa yake yi, sannan wani lokaci yana sosa mana rai ta hanyoyi daban-daban,
kamar sanya sha'awa, ko sanya bakin ciki, da sauransu.
Mu gode wa Allah kowace rana a kan ni'imar ji da ta gani da ya yi mana ita, wannan ni'ima ce
wacce ba don ita ba da ba mu san komai ba a rayuwarmu ta duniya, da ba mu amfana daga jin
makomarmu da abin da zai amfane mu a cikinta ba. Allah madaukaki yana cewa: "… Allah ne ya
fito da ku daga cikin uwayenku alhalin ba ku san komai ba. Kuma ya sanya muku ji da gani da
zuciya ko kwa gode".
Don haka kunne ni'imar Allah ce mai daraja, don haka ya hau kanmu kada mu yi amfani da shi
wurin saba masa, sai mu yi amfani da shi wurin ji da sauraron zancen Allah mai hikima, da
hadisan annabinsa masu daraja, maimakon mu rika sauraron zancen masu giba, da yana
annamimanci, da hana yin alheri. Mu yi amfani da shi wurin samun ilimi, da aiki da shi,
sanin duk wani abu da muka jahilta, sai sauraron wadannan abubuwan ya zama bautar Allah.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Saturday, June 19, 2010

Ƙara sabon ra'ayi