Hakkin Da ('ya'ya)

Hakkin Da ('ya'ya)
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alheirnsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa, sai ka yi aiki cikin umarninsa da aikin wanda ya san za a saka masa da kyautata masa, wanda kuma za a yi wa azaba kan musguna masa".
'Ya'ya ni'ima ce daga cikin ni'imomin Allah ga iyaye, kuma da nagari yana daga cikin arzutar mutum, kuma yana daga cikin abubuwan da ake saka wa mutum lada a kansu yana daga kabarinsa. Sannan yana daga cikin rabautar mutum ya samu da nagari mai taimaka masa yayin da ya tsufa ya yi rauni.
Daga nasihohi tattararru da suke cikin wasu hadisai su ne; Kada ka fusata danka ba tare da hakkin shari'a ba, wannan yana iya sanya masa jin haushi, da son barna, da daukar fansa, da nisantar gida ta hanyar kusantar mutanen banza. Haka nan an yi wa uba da yake tura dansa cikin biyayyar iyaye saboda kyawawan dabi'unsa rahama .
Game da tausasawa cikin mu'amala kuwa ya zo cewa, sauki shi ne yake kawata komai , tsanantawa ita ce take bata komai, haka nan mata da 'ya'ya ana son a biyar da su daidai yadda zasu iya gwargwadon karfinsu, kuma a yarda da dan kadan da zasu iya ba tare da kausasawa ko tsanantawa.
Game da girmama 'ya'ya a mu'amala ya zo cewa; Manzon Rahama (s.a.w) idan Fadima (a.s) ta shigo gida yakan tashi daga wajansa, ya kama hannunta, ya sumbance ta, ya zaunar da ita kan shimfidarsa .
A daidaita tsakanin 'ya'ya hatta a kallo: Da uba zai rika yi wa wannan kallon wulakanci ba dalili, amma wancan kuma ana lallashinsa to ba abin da wannan zai haifar sai kaiwa ga tarwatsawa da rarraba tsakanin 'ya'yan .
Annabi Ya'akub (a.s) ya kasance a aikace ba ya rabawa tsakanin 'ya'yansa, ba ya fifita wani a kan wani a aiki da mu'amala, amma ya kasance yana nuna wa Yusuf (a.s) soyayya domin Allah ya zabe shi, Sannan shi ne salihi a cikinsu da shi da dan'uwansa, kuma shi ne karami yana da hakkin soyayya da akan nuna wa yara.
Amma da yake 'yanuwansa mujrimai ne sai wannan ya sanya haushi ya rike su suka nemi kashe Annabin Allah su huta saboda soyayyar da yake da ita ta musamman wajan Annabin Allah Ya'akub (a.s), Sannan suka zo suka yi karya da kyarkeci don cimma mugun kaidinsu. Wannan mun kawo shi ne domin kare Annabi Ya'akub (a.s) da barrantar da shi daga zunubi da wasu suke jingina masa.
Kyautata sunan 'ya'ya da sanya musu sunan Annabawa da wasiyyansu; kamar Muhammad da Ibrahim da Ali, ko kuma sunan da aka danganta zuwa ga Allah kamar Abdullahi da AbdurRahman, ko sunan salihan bayi kamar Fadima da Maryam da Khadija ko Lukman, haka nan tarbiyyar 'ya'ya tana daga wajibi na farko a kan iyaye.
Duk da da yana da hakki kan iyayensa, sai dai hakkin nasa yana cakude ne da kyawawan halaye, don haka ne aka umarci 'ya'ya da runtse ido da kau da kai daga abin da suka mallaka yayin da iyayensu suka bukata daga garesu. Musulunci ya karfafi hakkin Allah ne a kan hakkin 'ya'ya sabanin yammacin duniyada suka karfafa hakkin 'ya'ya a kan na Allah. A kan wannan lamarin muna da kyakkyawan misali ga Annabi Isma'ila (a.s) da ya yi hakuri lokacin da babansa ya ce zai yanka shi bisa umarnin Allah, sai ya gaya masa da ya yi abin da aka umarce shi, bai yi maganar hakkinsa na rayuwa ba a matsayin hakkin dan Adam!.
'Ya'ya amana ce hannun iyaye, kuma Allah zai tambaye su yadda suka kiyaye wannan amanar; Fadinsa madaukaki cewa: Ya ku wadanda kuka yi imani ku kiyaye kawukanku da iyalanku daga wuta…" , ya isa matukar isa wurin gargadi da kiyaye wannan amanar a hannayen iyaye. Kuma babu wanda ya fi kowa ribatar wannan lamarin sai wadanda suka ba su tarbiyya kafin al'ummar da suke ciki, domin idan suka ba su tarbiyya to zasu kasance farkon wadadan zasu girbi alherin kyawawan wadannan 'ya'ya nasu.
Sannan akwai ruwayoyi masu muhimmanci wadanda suka yi nuni da marhalolin yadda za a ba wa yaro tarbiyya wadanda suka yi umarni da wasa da yaro shekaru bakwai, da yi masa ladabi shekaru bakwai, sannan sai a yi abota da shi shekaru bakwai . Wannan fomula ce mai kyau matuka da tasiri wurin ganin an samu tarbiyyar yaro mai kyau, da gina shi domin ya kasance namiji nagari.
Sai dai a batun tarbiyyanatar da shi akan samu matakai da yanayi da zamuna masu sassabawa, don haka sai a kiyaye nasa zamani. Kada iyaye su dora yaro kan irin al'adun nasu zamani matukar zamanin ya canja, sai su kiyaye canjin da aka samu bisa kiyaye kyawawan halaye. Imam Ali (a.s) yana cewa: Kada ku takura yara a bisa naku halaye (wato yanayin zamani) domin su an halicce su ga wani zamanin da ba zamaninku ba ne. Tayiwu irin wannan lamarin yana nuni da nau'in al'adu kamar na tufafi da sauran kayan more rayuwa, da kuma canjin halaye da al'adu da suke faruwa a zamuna mabanbanta .
Sannan akwai abubuwa masu yawa da suke taimakawa wurin samar da tarbiyya ta gari ga yara da suka hada da:
1- Tsaftar jiki da tufafi da wuri
2- Saba wa yaro da cin halal
3- Karfafa hankali da tunani yaro ta hanyar:
- Koya musu rubutu da karatu
- Tunani da lura cikin lamurransu
- Yawo da shakatawa da motsa jiki
4- Da karfafa ruhin yara ta hanyar:
- Bayyanar musu da abubuwan sadaukarwa masu kima a rayuwa
- Munana musu munanan halaye da guje musu
- Iyaye su aikata ayyukan alheri don su kasance koyi
- Lakkana wa 'ya'ya ibadoji da saba musu da su kamar salla
- Yin mu'amala da su da tausasawa da tausayawa
- Samar musu abokai salihai na gari, da nisanta su daga gurbatattu
5- Sai kuma takain kafa musu akida sahihiya, kamar son Manzon Allah (s.a.w) da alayensa tsatsonsa, musamman wasiyyansa goma sha biyu, da 'yarsa sayyida Zahara (s.a), da nuna musu wajabcin biyayya garesu, da sanar da su rayuwarsu.
Iyaye su ne wadanda suke da nauyi mai girma da muhimmanci a fagen tarbiyyar 'ya'yansu manyan gobe da ya hau kansu, suna iya cimma wannan buri da dan Adam yake bukatarsa matuka ta hanyar kiyaye dokokin da Ubangiji ya gindaya. Kuma kiyaye haka zai iya bayar da wata gudummuwa maras misali ga duniyar dan Adam, kuma su ma 'ya'ya da wannan ne zasu koma masu girmama iyaye da suke kawo ci gaba ga dan Adam.
Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Kamar yadda iyaye zasu take hakkin 'ya'ya, haka ma 'ya'ya zasu take hakkin iyaye . Wannan al'amari ya sanya muka ga karancin biyayya ga iyaye sakamakon karancin kiyaye hakkokin 'ya'yansu da yake faruwa ne.
Don haka akwai wasu bayanai muhimmai da zamu kawo kanunsu a nan ne kawai, mai son fadadawa yana iya koma wa littafinmu mai suna "Hakkin iyaye da 'ya'yansu".
Abu na farko shi ne zaba wa 'ya'ya uba na gari da uwa zata yi, da kuma zaba musu uwa ta gari da uba zai yi, sannan sai su duka biyun su yi fafutukan ganin sun cimma lamarinsu na tarbiyyar yaran gaba daya.
Sannan sai su girmama junansu domin yaran su rika ganin kimarsu duka gaba daya ta yadda zasu ga kowannen daga cikinsu yana da daraja don hakan ne zai sanya su yarda da kalaman kowanne daga cikin iyayen. Sannan sai su samar da yanayin da ya dace da tarbiyyar yara, kamar wuri mai tsafta, abinci mai tsafta na halal, kula da karatun Kur'ani ga yaran, son Manzon Allah (s.a.w) da alayensa (a.s), da abokai na gari.
A takaice zamu kawo wadannan abubuwan kamar haka:
1. Sanya sunaye masu kyau kamar masu nuna bauta ga Allah, da annabawa da na wasiyyansu:
2. Karfafa Izzar Rai
3. Bukatar Tausasawa Da Nuna Kauna
4. Sakin Fuska Da Nuna Kauna ,
5. Daidaito Cikin Kauna Da Kyauta
6. Tanadin Arzikin Halal
7. Samar Da Wani Yanayi Mai Sanya Nishadi
8. Muhimmancin Wasan Yara
9. Tsammani Da Buri Marasa Amfani
10. Kula Da Lafiyar Yaro
11. Wajebcin Tarbiyya
12. Kula Da Mutuncin Yaro
13. Karfafa Alakar Tattaunawa
14. Habbaka Yanayin Yara
15. Amsa Wa Yara Tambayoyi
16. Yada Jin Kunya
17. Koyon Ilimi Da Ladabi ,
18. Gaskiya Da Rikon Amana
19. Koyar Da Kur'ani
20. Soyayyar Alayen Annabi (s.a.w) ,
21. Motsa Jiki Da Yawon Shakatawa
22. Zabar Aiki Mai Dacewa
23. Taimakawa Don Yin Aure
24. Yin Wa'azi D a Shiryarwa
Don haka hakkokin 'ya'ya a kan iyaye suna da muhimmanci matuka, Imam Ali (a.s) yana cewa: "Da yana da hakki kan uba, kuma uba yana da hakki kan da, daga hakkin uba a kan da, ya bi shi a komai sai dai cikin sabon Allah, kuma hakkin da a kan uba shi ne ya kyautata sunansa, ya kyautata ladabinsa da koyar da shi Kur'ani" .
Sannan mun riga mun yi nuni da cewa hanyar soyayya hanya ce da take kusanto da yara ga iyayensu, har su samu nutsuwa da iyayensu su karkata zuwa garesu, ta haka ne iyayen zasu samu bayar da tarbiyya ta gari ga 'ya'yansu. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Soyayya tsakanin iyaye, kusanci ne tsakanin 'ya'ya, kusanci ya fi bukatar soyayya fiye da yadda soyayya take bukatar kusanci" .
Daga karshe muna son mu yi nasiha ga uba cewa kada ya sanya tsoron yadda zai tafiyar da rayuwar yaransa da yawa a ransa, domin matukar ya dauki matakan da suka da ce wurin tafiyar da rayuwarsa, to Allah zai zo masa da nasa taimakon, kuma zai arzuta shi da su 'ya'yan. A kan haka ne zamu Imam Ali (a.s) yana cewa da wani sahabinsa: "Kada ka sanya mafi yawan shugulin zuciyarka ya kasance na iyalinka da 'ya'yanka: Idan iyalinka da 'ya'yanka sun kasance daga masoya Allah, to Allah ba zai tozarta masoyansa ba, idan kuwa sun kasance daga makiya Allah ne, to me ye naka na bakin cikinka da shagaltuwarka da makiya Allah?!" .

www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Thursday, June 16, 2011

Ƙara sabon ra'ayi