Gyaran Rai Na Biyu

Gyaran Rai Na Biyu

Rai shi ne bangaren badini na dan Adam wanda ba a ganin sa amma ana riskarsa da mariskai na badini, don haka ne kowane mai rai yana riskar samuwarsa da cewa yana da samuwa.

Ran Mutum
Rai shi ne bangaren badini na dan Adam wanda ba a ganin sa amma ana riskarsa da mariskai na badini, don haka ne kowane mai rai yana riskar samuwarsa da cewa yana da samuwa. Amma jiki shi ne bangaren zahiri na dan Adam wanda yake ana riskarsa da mariskai na zahiri, kamar gani, ji, shaka, dandano, da sauransu. Da wannan ne zamu kai ga natijar cewa mutum yana da bangarori biyu ne na badini da zahiri, kuma asalinsa shi ne badininsa, amma a fili muna iya fahimtar asalinsa wato badininsa ta hanyar zahirinsa ne.
Ran mutum tana da rassa da bangarori kamar yadda jikinsa yake da gabobi, wadannan bangarori sun hada da zuciya, da hankali, da Saken tunani (Khayal), da Saken zuciya (Waham), sai kuma Rundunar Sha'awa, da Rundunar Fushi.
Zuciya: Ita ce bangaren samuwar mutum mai juya shi wacce idan ta samu haskaka da hasken shiriya babu wani abu da yake bubbugowa daga gareta sai umarnin alheri. Amma idan ta cika da duhun bata to sai ta lalace, sai ta kasance babu wani abu da zai zo daga wurinta sai umarni da sabo. Don haka ne ma ruwaya ta zo cewa a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuwa ta baci dukkan jiki ya baci, ita ce zuciya .
Kuma ita wannan zuciya ita ce gidan ubangiji a cikin duniya da bai yarda a sanya kowa a ciki ba sai shi, don haka ne wanda ya yarda ya sanya wanin Allah a cikinta to sai ya tabe. Sai dai sanya wanin Allah ba yana nufin babu wani a ciki ba, abin nufi shi ne idan akwai wani abu a cikinta to ya kasance don Allah, kamar dai son annabawa, da waliyyai, da bayin Allah saboda Allah.
Hankali: Shi ne bangaren rayukan bayi mai riskar sanin abubuwa kamar yadda suke ko sabanin hakan, ana son cika wannnan bangaren da hasken ilimi da sanin Allah madaukaki da siffofinsa, da annabawansa da wasiyyansu.
Idan wannan bangare ya samu hasken ilmi to babu wani abu da zai yi sai kokarin haskakawa sauran gabobi da abin da ya dace da wanda bai dace ba, sai ya rika nuna hanya ga mutum domin ya kai shi zuwa ga rabautarsa. Shi fitila ce ta sauran bangarori da idan suka fada duhu zai haskaka musu, kuma shi zai bayar da mafita ta gari da nuni zuwa ga hanyar kwarai.
Amma idan ya jahilci ubangijinsa, da siffofinsa, da sakonsa, ya kasa tantance gaskiya da karya, sai ya rude ya shiga dimuwa, rundunar jahilci ta mamaye shi, sai wauta ta durfafe shi, duhun rashin sani ya lullube shi, sai ya jagoranci bangarorin sha'awa da fushi zuwa ga hanyar lalaci da bata, domin shi makahon jagora ne wanda bai san mafita ba.
Hankali shi ne jagoran tafiyar a dukkan wadannan bangarori na rai, kuma shi ne yake tantance mai kyau da maras kyau sai ya yi umarni da kyakkyawa, ya hana yin mummuna, kuma ya tace ya auna guda biyun sai ya ware mai amfanarwa da mai cutarwa domin ya yi umarni da da rinjayar da amfanuwa daga na farko, da kuma nisantar na biyu.
Saken Tunani (Khayal): Shi ne bangaren rai wanda yake tuna abubuwan da suke da surarsu da hotonsu a cikin tunani, wasu sun faru wasu kuwa ba su faru ba, yana iya haifar da wata sura ta wani abu mai kyau ko mai tsananin muni. Wannan bangare yana daga cikin bangaren da ya fi komai hadari domin yana sanya waswasi, da firgici, da tsoro, misali idan mutum yana shi kadai, ko yana cikin duhu musamman yara wannan bangaren yana iya azabtar da su har su fita da gudu.
Daga cikin ayyukansa yakan iya daukar surar abubuwan da ya riska sai ya hada su, kamar ya sawwala wani dokin zinare mai fika-fikai, da kaho. Da wannan ne zamu fahimci hadarin wannan bangare na Saken tunani, da cututtukan rai da yake jefa mutane kamar waswasi.
Saken Zuciya (Waham): Shi kuwa wani bangare ne na rai wanda yake da hadarin gaske, wanda yake tafiyar da Bangaren Sha'awa da Bangaren Fushi da suke bangarori ne na rai, yana da son holewa da kece raini, da son hutu da annashuwa, da tunkude duk wani abu da bai yarda da shi ba ga kansa. Bangare ne da yawanci yakan yi umarni da abin da ya fi sauki ne, misali yakan sawwala wa mutun hutawa da yin bacci yayin da ya ji kiran salla, ko ya sawwala masa son kallo ko jin wani abu wanda yake na haram. Idan aka yi sakaci ya fada hannun rundunonin jahilci wadanda suka fi kusa da shi domin abin da suke so ya fi sauki gareshi, to sai mutum ya fada cikin halaka, ya dulmiya cikin bata.
Wannan bangaren na Saken zuciya shi ne mai bayar da umarni da hanin da yawanci karkatacce ne domin abin da rai ta so shi take yi, abin da ta ki shi take bari, kuma yawanci takan bi mai dadi ne ta bar mai wahala, don haka sai ta koma wa hankali domin tantancewa. Idan wannan bangaren ya yi wa hankali tawaye to a lokacin ne halaka take zuwa, sai mutum ya fada cikin duk wani ashararanci da lalacewa, da holewa da kece raini.
Bangaren Sha'awa: Shi ne bangaren da yake neman jawo wa rai wani amfani da duk wani abu da take sha'awa, wannan abin kuwa ya hada da na badini ne kamar abin da ya shafi ruhi kamar son ilimi, ko son kai, jin dadin rai. Ko kuma abin da ya shafi zahirin rayuwa wanda ya shafi bukatun jiki, kamar son jima'i da son mata, da son kyau, da son ci da shan mai dadi, da hutawa, da son bacci.
Wannan bangaren yana bin abin da Saken Zuci ya ba shi umarni ne, kuma yakan motsa matuka domin cimma burinsa idan ya tashi, har ma ya gusar da hankali, kamar mutum mai tsananin sha'awa da ya kebe da matar da yake sha'awa gabansa, idan wannan sha'awar ta kai kashi 100 ta yadda ta gusar da hankali to yana iya rungumar ta ko ya auka mata.
Bangaren Fushi: Wannan bangaren shi ma yana bin abin da Saken Zuci ya ba shi umarni ne, kuma yana kunshe da kyamar duk wani abu da bai yi wa rai dadi ba. Yana gudun aibi, yana kyamatar duk wata tawaya ta badini kamar jahilci, da tawayar rai, da jin rashin kamala, da isar rai. Kamar yadda yana motsawa matuka idan ya fahimci aka yi masa wulakanci na zahiri, kamar renin wayo, da keta mutunci, ko izgili da akidarsa, ko ubangijinsa, ko iyayensa, ko kansa, don haka ne ma yake tashi da karfinsa duk sa'adda rai ta fahimci ba a yi mata daidai ba.
Hadarinsa yana da girma matuka, domin idan ya tashi ya kai wani mikdari mai tsanani kamar kashi 100 yana iya yin kisa, ko sata, ko hari kan duk abin da yake so ya kai wa hari, don haka ne aka yi umarni da nisarta fushi matuka a addinin musulunci. Sai dai larura ne ga mutum ya motsar da shi yayin da ake bukatar hakan, kamar ya fusata don kare mutuncinsa da na iyayesa, ko ya motsa don kare wani abu mai daraja gunsa kamar idan aka ci mutuncin addininsa.

www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Tuesday, May 25, 2010

Ƙara sabon ra'ayi