Duniyar Barzahu
Duniyar Barzahu
Barzahu duniya ce mai cike da kamanni da wannan duniya, ita ba a wannan duniya ba, kuma ba lahira ba, sai dai ta wani bangare tana cikin wannan duniyar, kuma tana wani bangare ba ta cikinta. "Allah yana da wani mala'ika da yake kira kowace rana cewa; Ku haifa domin mutuwa, ku tara domin karewa, ku gina domin rushewa". Nahajul-balaga: Hikima: 127.
Don haka duniya wuri ne na wucewa ba na wanzuwa ba, "Duniya gidan wucewa ne zuwa gidan tabbatuwa, mutane a ciki iri biyu ne: Mutumin da ya sayar da ransa sai ya halaka ta, da mutumi da ya sayi ransa sai ya 'yanta ta". Nahajul-balaga: Hikima: 128. Sannan duk wani abu yana wucewa da sauri kamar wulkawar ido, duniya gidan gaggawa ce ba gidan jinkiri ba: "Duk wani abu mai zuwa yana da komawa, kuma abin da ya koma ya juya baya kai ka ce bai kasance ba". Nahajul-balaga: Hikima: 144.
Sannan babu wani wanda ya isa ya ki tafiay, mutuwa riga ce wacce ba ta fita, kai ta fi riga, domin ana iya kwabe riga, amma ita mutuwa fatar jiki ce da ba a iya yage ta a jefar, kuma wannan karshen yana iya kasacnewa mai daci ko mai zaki, mai wahala ko mai dadi. "Kowane mutum yana da karshe mai zaki ko mai daci". Nahajul-balaga: Hikima: 143.
Don haka kada a dauki duniya da zafi sosai, a bi ta a sannu, gida ne mai dadi da wahala, mafi munin wahalarta shi ne talauci, idan talauci ya mamaye al’umma ba ta iya samun nutsuwa balle ta yi tunani. "Talauci shi ne mafi girman mutuwa". Nahajul-balaga: Hikima: 153.
Idan mutum ya yi zari sosai to zai tara wa kansa wahalar da wani zai sha dadin sakamakonta, don haka gajiyar da kai domin tarin da ya wuce kima wahala ce. "Ya kai dan Adam, duk abin da ka nema sama da karfinka, to kana tara shi ga waninka ne". Nahajul-balaga: Hikima: 182. Don haka sai a zo wa wannan duniya a sannu, kada a bi bayanta duk inda ta yi, a yi gaba da kanta zata zo. "Hkika wannan zukata suna da sha'awa da gaba da baya, ko zo musu ta gaba". Nahajul-balaga: Hikima: 183.
Idan muka ketare bangon wannan katangar duniya sai mu fada wacca duniyar da ake kira barzahu, mutanen barzahu suna rayuwa kamarmu, suna jin dadi, wasu kuwa suna shan bakar wahala, wasu ma jibgar su ake yi kamar yadda Kur’ani ya gaya mana game da Fir’auna da mutanensa.
Wata rana -a lokacin da Imam Ali (a.s) ya dawo daga yakin Siffain, sai ya yi nuni ga kaburburan bayan birnin Kufa ya ce:- "Ya ku mutanen gidaje masu dimautarwa, masaukan talauci, kaburbura masu duhu. Ya ku ma'abota turbaya, ya ma'abota bakunci, ya ma'abota kadaitaka, ya ma'abota dimuwa, ku ne masu rigo masu wucewa gaba, mu masu biyo sawunku ne. Amma gidaje dai an zauna su, kuma mata an aure su, kuma dukiyoyi an raba su. Wannan shi ne labarinmu ku kuma meye labarinku. Sannan sai ya juya wurin sahabbansa sai ya ce: Amma da an yi musu izinin yin magana da sun ba ku labarin cewa "Hakika Takawa ita ce mafificin abu.". Nahajul-balaga: Hikima: 125.
Idan mun duba wannan magana ta Imam Ali (a.s) zamu ga ta kunshi bangarori masu muhimmanci da zamu yi nuni da su. Na farko kiran sa ga wadannan mutane da cewa; "Ya ku mutanen gidaje masu dimautarwa, masaukan talauci, kaburbura masu duhu", wadannan kalmomi ba wasa ba ne daga gareshi mai aminci, sai dai magana ce zuwa ga masu fahimtar abin da masu rayuwa a wannan duniyar ba sa ganewa.
Sannan Imam Ali (a.s) ya kira wadancan gidajen masu dimautarwa imma dai saboda farkon zuwa wadannan gidaje na barjahu firgici yakan samu mutum kamar yadda firgici yakan samu mutanen da suke zuwa wannan gidan duniya yayin fitowa daga cikin mahaifiyarsu, ko kuma bisa la'akari da cewa yawancin mutane ba su da aiki na kwarai, shi kuwa gidan barzahu gida ne na shan wahala ga dukkan wanda bai yi mai kyau ba.
Kuma wannan lamarin yana iya bayyana a fili idan muka yi la'akari da wasu bayanai da ruwayoyi da suke nunin rashin ceto a duniyar barzahu. Sai dai muna iya sake tambayar cewa; shin wahalar duniyar barzahu ta shafi marasa imani ne ta yadda duk wanda bai yi imani ba zai kasance cikin wahala da azabar barzahu ko kuwa ta ta'allaka da rashin ayyuka na gari ne ta yadda musulmi da kafiri wadanda suka yi ayyuka mummuna zasu sha wahala, musulmi da kafirai wadanda suka yi aikin alheri zasu samu jin dadi.
Sai dai idan muka duba zamu ga wasu ruwayoyin suna nuni da cewa samuwar duniya biyu wato; wadussalam da kuma barhut , kuma rayukan muminai yana zuwa wadussalam ne na kafirai kuwa yana zuwa barhut ne, don haka duk musulmi zai ji dadi a barzahu, duk wanda ba musulmi ba zai sha wahala a barzahu.
Sai dai idan muka duba cewa duniyar barzahu ba ta takaita da wadannan gidaje biyu ba zamu gane cewa wannan amsar ba daidai ba ce. Domin wasu a barzahu zasu kasance a cikin yanayin bacci ne kuma ba zasu farka ba sai ranar kiyama, wannan ne ma ya sanya wadannan sukan ce ai ba mu zauna ba sai rana daya ko rabin wuni.
Amma wadanda suke iya farkawa su rayu a barzahu mutane biyu ne; masu tsananin sabo wadanda za a kai su barhut, kamar yadda aka yi wa Fir'auna da mutanensa, da kuma masu imani mai karfi da za a kai su Wadussalam kamar yadda manzon Allah (s.a.w) da sakatarensa Imam Ali (a.s) da umarnin Allah suke kai mutane wurin bayar mutuwarsu da sauran mabiyansa masu imani domin su ci gaba da ilimi a tantunan da ake kafawa a can, da dausayoyi masu ni'ima, da koramu masu dadi, ko kuma yara da ake kai su gun annabi Ibrahim (a.s) a wannan duniyar ta barzahu domin su koyar da su ilimi kafin ranar tashin kiyama.
Amma da Imam Ali (a.s) yake siffanta wannan duniya ta barzahu da cewa; "masaukan talauci", yana nuni ne da talauci da dukkan nau'insa. Rashin duk wani abu na alatun duniya da muke gani a makabartu wannan shi ne talauci na zahiri, don haka ne ma idan mutum ba shi da abin da zai biya bukatunsa na duniya, ta yadda ba zai iya mallakar abin da yake bukata kamar yadda ya dace da sha'anin rayuwar al'umma sai a kira shi talaka. Amma a duniyar barzahu akwai talaucin mafaka babu wani abu da mutum zai samu sai abin da ya aiwatar mummuna ko kyakkyawa, don haka idan ya rasa taimako to a nan shi ne talaka. Sai dai akwai talauci da ma'anarsa mai zurfi, wannan shi ne talaucin da yake zatin samammu da halittun Allah gaba daya ne. wato dukkan halittu talakawan Allah ne, domin zatinsu ne su bukace shi, ba su da samuwa sai idan ya ba su, kuma ba su da komai sai abin da ya samar musu, gaba dayan samuwarsu da rayuwarsu talaci ne zuwa ga Allah, Allah shi kadai ne mawadaci. Wannan ne yake nuni da fadin Allah madaukaki: "Ya ku mutane ku masu bukata ne gun Allah, Allah shi ne mawadaci abin godewa" (Fadir: 15).
Amma fadinsa mai daraja da yake siffanta su da "kaburbura masu duhu", ga dukkan alamu wasu zasu yi tsammanin duhun duniya zai kasance shi ne ake nufi, da ya kasance haka ne kuwa da babu wani wanda zai tsira daga wannan duhun. Don haka ne zamu iya tabbatar da cewa ba duhu ne irin na duniya ba, sai dai ya kasance duhu irin na barzahu kamar yadda rayuwarsu take ta barzahu.
Da wannan ne zamu iya gani a fili cewa rayuwar barzahu ba abin da ya dace da ita sai talauci irin na barzahu, domin babu wata ma'ana wanda yake barzahu ya zama talaucinsa shi ne rashin kudi, yunwarsa ta kasance ita ce rashin abinci, kishirwarsa ta kasance rashin ruwan sha, tsaraicinsa ya kasance rashin tufafin sawa, domin da ya yi shekaru miliyoyi babu wadannan abubuwa da bai bukace su ba.
Haka nan yanayin rayuwa kamar wurin kwana da wurin tafiya kamar kasuwa, da filin hira, da makaranta, da gidan hutawa da shakatawa da kurkuku, da 'yan sanda da jagorori, a wancan gida na barzahu duk sun saba da na wannan duniya, don haka duk wani kwatance da za a yi mutane a wannan duniya game da barzahu sai dai ya kasance domin su fahimciwani abu da zai kasance hanyar shiriyarsu.
A nan ne zamu fahimci hatta da ilimin da ake kwasa a waccan duniya ta barzahu yana da na shi bayani sabanin na wannan duniya, sai dai duk yadda aka juya zai kasance bude shafukan abubuwan da aka jahilta ne domin saninsu da yaye duk wani hijabi da shamaki daga ma'abota rashin sani, ta yadda zasu dadani gaskiya kamar yadda take. Wannan lamarin yana da girma matuka, domin makaranta ce ta mutanen da ba su da jiki irin namu na wannan duniyar, bukatunsu sun saba, halayen mutanen wannan duniya.
Don haka zamu fahimci duhun duniya ba duhu ba ne wanda idan aka dauke fitila sai mu daina ganin komai, idan aka kawo wuta sai mu ga haske, ba wuri ba ne wanda yake da dare da rana balle a ce rana ta kule don haka sai duhu ya bayyana, sai dai shi duhu ne na barzahu wanda yake mamaye samuwar mutum da rayuwarsa ta barzahu.
Sannan sai fadin Imam Ali (a.s) cewa: "Ya ku ma'abota turbaya, ya ma'abota bakunci, ya ma'abota kadaitaka, ya ma'abota dimuwa", idan mun duba zamu ga kalmar turbaya tana nuna rashi da talauci wato rashin kayan more rayuwa da suke makabarta, amma idan turbaya ce ta barzahu to sai ta saba da wannan turbaya, sai dai wannan turbayar ta duniya ita ce zahirin waccen turbayar ta barzahu, kamar yadda kuma turbayar barzahu ita ce zahirin ta lahira, ta lahira kuwa badinita.
Sannan Imam ya ambaci kalmar "bakunci" wanda zamu iya gani a fili cewa ma'abota barzahu baki ne, a waccan duniya, kamar yadda mutumin da ake haifa a wannan duniya yake zama bako har ya bar ta, don haka ne zamu gane cewa gidan gaskiya da hakika shi ne gidan lahira inda kowa zai dawwama.
Ya kuma kira su "ma'abota kadaitaka, saboda a kowane gida a barzahu mutum daya ne, duniyar barzahu ba ta ma'anar gida da wani yaek da shi da 'ya'yansa, domin ba a haihuwa, ba a aure, ba a kafa gari, babu gida, babu gari, babu sarki, babu komai sai mutum da ubangijinsa.
A nan ne maganar Sadrul Muta'allihin zata tabbata cewa mutum jinsi ne da yake da nau'oi mabanbanta a cikinsa, kowanne yana da nasa nau'in da ya saba da na waninsa. "Kuma kowannen yana da fuskar da yake jibinta, to fa sai ku yi rigen alheri…" (Bakara: 148).
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya kira ma'abota barzahu da "ya ma'abota dimuwa", domin halin da suke cike na mayen abubuwan da suka gabata, suna cikin mayen turbaya, da mayen talauci, da mayen kadaici. Mu sawwala wani mutum ya fada cikin irin wadannan halayen a duniya yaya zamu ga dimaucewarsa, haka nan mutumin da ya fada irin wannan a barzahu yake fuskantar dimaucewa.
Sannan Imam Ali (a.s) ya yi nuni da cewa "ku ne masu rigo masu wucewa gaba, mu masu biyo sawunku ne", haka nan duniyar barzahu take, ta yi kama da duniya, girmar wani da rigon sa zuwa wannan duniya ba falala ba ce, haka nan girmar wani da rigon sa zuwa duniyar barzahu ba falala ba ce. Don haka wannan gabatar ba gabatar falala ba ce, sai dai gabata ce irin ta samuwar da ta dogara da zamani.
Sannan sai Imam (a.s) ya yi musu magana yana mai lurasshe da wadanda suke tare da shi da sunan yana yi wa na kabari magana yana cewa: "Amma gidaje dai an zauna su, kuma mata an aure su, kuma dukiyoyi an raba su". Dan Adam ba shi da wani buri da ya fi ya samu gida, da mata, da dukiya, don haka ne Imam (a.s) bai yi amfani da wani abu a wannan bayani ba sai su. Sai ya nuna musu duk wannan abubuwan da kuke hankoron samu to ku sani wata rana zai koma hannun waninku, idan gidan ne zaka bar shi wasu su gaje, idan mata ce zaku bar ta wasu su aure, idan dukiya ce wasu zasu maye ta, sai hisabinta ya hau kanku, wasu kuwa su amfana da ita, don haka mai hankali sai ya samu abin lura da tunani.
Sannan sai Imam ya nemi su yi magana, sai dai koda sun yi magana babu mai ji sai shi. Manzon rahama (s.a.w) ya yi magana da na rijiyar kulaib, har sai da wani daga sahabbansa ya yi mamaki cewa; yaya kake yi wa matattu magana, yana mai jahiltar cewa manzon rahama (s.a.w) yana da kashafin badinin samammu. Don haka ne wadannan matattun da sun amsa wa wasiyyin manzon rahama (a.s) da babu wanda zai fahimta sai shi, kamar yadda manzo ya fahimta sabanin sauran mutane. Don haka ne ma Imam Ali (a.s) ya ce: "Wannan shi ne labarinmu ku kuma meye labarinku".
Sannan sai ya juya wurin sahabbansa sai ya ce: Amma da an yi musu izinin yin magana da sun ba ku labarin cewa "Hakika Takawa ita ce mafificin abu", a fili yake cewa ba a izini da jiyar da sahabbasa ba sabanin shi.
Shi yana dauke da suna mafi girma, don haka babu wani abu da zai buya gareshi game da barinsu sabanin mutane. Sannan mafi muhimmancin lamari a cikin wannan bayanai shi ne lamarin jin tsoron Allah madaukaki, domin duk wani tsoro, ko talauci, ko dimuwa, ko kadaici, da dan Adam yake fuskanta a barzahu, ko wani duhu da yake mamaye shi, duk ana iya kauce musu du tsoron Allah da aka fi sani da Takawa.
Sannan duk mutum mai tafiya ne da gaggawa, domin shekaru 60 zuwa 100 da mutum yake yi a wannan duniya suna kama da awa daya ne, don hak ane zamu ga yadda gaggawar halartowar barzahu take Imam Ali (a.s) yana cewa: "Tafiya ta kusa". Nahajul-balaga: Hikima: 177.
Don haka duk wani abu da zamu yi na zaluntar kawukanmu ko zaluntar waninmu mu kiyaye mu nisance shi. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Mai fara zalunci a gobe zai ciji tafinsa". Wato Ranar kiyama zai ciji yatsansa don nadama. Nahajul-balaga: Hikima: 176.
Idan mun duba zamu ga ranar kiyama tana farawa daga barzahu ne, don haka wanda bai kiyaye ba zai ciji yatsansa a barzahu. Allah ka sanya mana aiki domin kai bisa takawa, ka sanya mu cikin daliban Imam Ali (a.s) a barzahu.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Saturday, 31 July 2010
Duniyar Ba
Ƙara sabon ra'ayi