Tafarkin Ahlul Baiti (a.s)
Tafarkin Ahlul Baiti (a.s)
Babu shakka cewa hadisai masu yawa sun zo suna nuni da wasiyyar da manzon Allah (s.a.w) ya bar wa al’ummarsa ta biyayya ga littafin Allah da riko da ahlin gidansa, kuma ya kawo su waye su, domin babu ma’ana manzon rahama (s.a.w) wanda ya fi kowa kamalar hankali da tunani ya zo ya ce wa mutane akwai littafin Allah da ahlin gidana da zaku bi bayana, kuma ba zasu taba rabuwa da littafin Allah (s.w.t) ba, sannan kuma bai ayyana littafin Allah ba, kuma bai ayyana mutanen da yake nufi ba.
Hadisai masu yawa sun zo a littattafan Shi'a da Sunna kan cewa: manzon rahama ya yi umarni da biyayya ga ahlinsa bayansa, mafi shahararsa shi ne hadisin manyan nauyayan alkawura biyu da aka dora su a kan wannan al’umma, wanda sahabbai masu yawa suka ruwaito shi, kamar: Jabir dan Abdullah, da Zaid dan Arkam, da Abu Sa’id al’Khudri, da Zaid dan Sabit, da sahabbai wasunsu masu yawa.
Hadisin ya zo da sigogi daban-daban, kuma dukkaninsu suna nuni da abu guda ne da yake nuna wajabcin riko da littafin Allah da Ahlin gidan Annabi (s.a.w)
Amma mu a nan zamu wadatu da kawo siga daya daga cikinsu, sannan sai mu yi nuni da inda za a samu sauran, domin duk suna nuni da abu guda ne. Muslim ya ruwaito wani hadisi mai tsawo daga Zaid dan Arkam, daga cikin hadisin yana cewa; manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Amma bayan haka, ku sani ya ku mutane cewa ni mutum ne, dan sakon ubangijina ya kusa zuwa sai in amsa, kuma ni na bar muku nauyayan alkawura biyu: Na farko; Littafin Allah, a cikinsa akwai shiriya da haske, to ku yi riko da littafin Allah, ku yi riko da shi, sai ya kwadaitar da riko da littafin Allah, ya karfafa kwadaitarwa, sannnan sai ya ce: Da kuma ahlin gidana, ina hada ku da Allah kan ahlin gidana, ina hada ku da Allah kan ahlin gidana, ina hada ku da Allah kan ahlin gidana!
A cikin Kur’ani mai girma madaukaki yana cewa: “Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa” . Amma a cikin hadisi mai tsarki kuwa ya zo cewa: "Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su" .
Wadannan ruwayoyi suna da tawaturanci daga manyan maruwaita kamar haka: sahih Muslim: 4/1873, sunan Tirmizi: 5/622-3, masnad Ahmad: 3/14; 26, mustadrak: 3/148, 109-10, majama'uz zawa'id: 9/162, da gomomin littattafai wadanda ba mu kawo su ba.
Sannan kuma dukkan malaman hadisai sun tafi a kan ingancin sanadinsa, kuma yana daga hadisai mutawatirai (wato; hadisin da babu yadda za a yi ya kasance mai rauni, saboda yawan malamai amintattu masu ruwaito shi).
Duba: assawa'ikul muhrika: 145, 228, 9/162, tafsirul Kur'anil Azim: 4/113.
A cikin wannan hadisin zamu ga yadda manzon Allah ya muhimmantar da wasiyyarsa, ya kira ta nauyi da Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) suka dora wa al’umma, kuma matukar ta yi riko da su ba zata taba bata ba har abada. Wannan shi ne gadon da Annabi (s.a.w) ya bar wa al’ummarsa, domin annabwa ba su bar wa al’ummarsu gadon dukiya ba, sun bar musu gadon ilimi ne da shiriya. Sannan sai ya kira su da abubuwa biyu masu daraja da nauyi, saboda nauyin kiyaye su da yake kan al’umma.
Duba: buhari: 1/27, tirmizi: 5/49, ibn Majah: 1/81, darumi: 1/98, ibn Hambal: 5/196. da wasunsu masu yawa.
Sannan kuma ya yi nuni da su waye alayensa, wato ahlin gidansa a cikin ruwayoyi masu yawa. Da manzon rahama (s.a.w) bai yi nuni da su waye ba, da an samu karon maganganu tsakanin al’ummarsa. Sai dai Allah da ludufinsa mai girma duk sa’adda ya yi bayanin shari’a yakan kawo bayanin wadanda ake nufi da ita. Muna iya ganin misalin ayar mubahala, da ayar ciyarwa, da ayar tsarkakewa, dukkan wadannan ayoyi bayan saukarsu manzon rahama (s.a.w) ya yi bayanin cewa; alayensa ake nufi da wadannan falaloli, sannan kuma ya ambaci sunayensu wato; Ali, Fadima, Hasan, da Husain (a.s), da kuma tara daga zuriyar Husain (a.s), wanda na karshensu shi ne Imam Mahadi (a.s) da zai bayyana karshen duniya, kamar yadda na farkonsu shi ne Imam Ali (a.s).
Duba: Muslim: 4/1871, masnad ibn Hambal: 1/185, Tirmizi: 5/225.
Sannan muna ganin yadda manzon rahama (s.a.w) ya yi nuni ga wannan al’ummar da cewa su duba su gani me zasu yi game da wadannan nauyayan alkawura biyu, wannan kuwa saboda ya san al’ummarsa zata kasance ta bi sawun yahudawa da kiristoci ne, ba zata bi wannan sakon da ya zo da shi ba kamar yadda su ma ba su bi na annabawan da suka gabata ba. Don haka ne ma ya yi musu gargadi a karshen wannan hadisin.
Sannan kada wani ya yi tsammanin ya fadi hadisin a lokaci guda ne, domin akwai karinoni masu yawa da suka nuna yin wasiyya da alayensa da Kur’ani a wurare masu yawa, wannan ne ma ya sanya al’umma a wannan zamanin na saukar Kur’ani ta san wasiyyarsa ba tare da jahiltar ta ba.
Sai dai al’umma ta kasance kamar al’ummar Musa (a.s) ne, kamar yadda yahudawa suka yi watsi da Haruna (a.s) suka bauta wa dan maraki, ko kiristoci da suka yi watsi da Sham’unus Safa, suka riki waninsa, to haka ma wannan al’ummar ta yi watsi da wasiyyan Annabi (s.a.w) ta yi riko da wasunsu. Sannan wani abin mamaki, kamar yadda wasiyyan Annabi Musa (a.s) da Isa (a.s) kowannensu suke guda goma sha biyu, haka ma na manzon Allah Muhammad (s.a.w) suke su goma sha biyu!.
Don haka ne muka ga Imam Ali (a.s) yana da siffofin Haruna (a.s) da Yusha’u bin Nun, (a.s) wadanda suke wasiyyan Annabi Musa (a.s) kafin da bayan mutuwarsa. Kamar yadda aka kin bin Harun (a.s), haka aka ki bin sa, kamar yadda matar Musa (a.s) ta yaki Annabi Yusha’u bin Nun (a.s) wasiyyin Musa (a.s) bayan mutuwarsa, haka ma, matar manzon Allah (s.a.w) ta ya ki wasiyyinsa Ali (a.s), kamar yadda harun (a.s) yake da ‘ya’ya masu suna kusan iri daya, shabar, shubair, haka ma Imam Ali (a.s) yake da ‘ya’ya Hasan, Husain.
Kamar yadda Yusha’u bin Nun ya yi shekaru talatin bayan Musa (a.s), haka ma shi ma Ali (a.s) ya yi shekaru talatin bayan Muhammad (s.a.w), kuma kamar yadda mutane uku suka yi jagorancin al’umma bayan Musa (a.s) kafin Yusha’u (a.s), haka ma mutane uku suka yi halifanci bayan Muhammad (s.a.w) kafin Ali (a.s).
Da manzon Allah (s.a.w) yake nuni ga wannan al’umma da cewa; Ku duba ku gani shin zaku kiyaye amanar wadannan abubuwa nauyaya biyu bayana kuwa ko zaku bi wasu daban ba tafarkinsu ba. A nan zamu ga yadda yake nuni da cewa mafi yawan al’umma ba zasu bi su ba, kamar yadda al’ummun farko mafi yawan al’ummarsu ba su bi wasiyyansu ba.
Wani abin mamaki shi ne; har yanzu mazhabin kowane mutum a cikin wannan al’umma ana samun nutsuwa da mai bin sa, da rashin tsangwamarsa, amma duk wani wanda ya riki tafarkin alayen manzon Allah (s.a.w), to wannan ya zama abin tsangwama.
Sannan kuma muna iya ganin yadda al’umma ta jahilce su, saboda tsananin gaba da aka yi da su, da boye hakikaninsu, da kawar da ambaton sunansu daga cikin al’umma sakamakon gaba da wannan gida mai daraja da sarakunan musulmi suka yi a tsawon tarihinsa.
Domin duba kamannin tarihin wannan al’umma da ta Annabi Musa (a.s), duba wadannan ayoyi da tafsiransu, da kuma wadannan hadisai kamar haka:
Yunus: 35, A’afari: 150, duba: Faidhul Gadir: 3/14.
Sannan bayan hadisin nauyayan alkawura biyu; akwai hadisai masu yawa da suka zo suna nuni da wajabcin riko da Ahlul Baiti (a.s) da tafarkinsu, hadisai kamar mai nuni da cewa; Ahlul Baiti (a.s) su ne amincin wannan al’umma, kuma duk wanda ya saba musu zai zama daga rundunar Ibilis zai halaka. Duba: alMustadrak: 3/149.
Da hadisin da yake nuni da cewa su aminci ne ga al’umma, idan babu su to al’umma zata halaka. Duba: alMustadrak: 3/457, 2/448, Faidhul Gadir: 6/298.
Da nuni da cewa su kamar jirgin Annabi Nuhu (a.s) suke ga al’umma, duk wanda ya shiga ya tsira, wanda ya ki kuwa ya halaka. Duba: alMustadrak: 2/343, 3/150, Kanzul Ummal: 12/94, da gomomin littattafai da ba mu kawo ba.
Wadannan abubuwan duk suna nuna mana cewa ba yadda al’umma zata fita daga bata, sai da biyayya ga Ahlul Baiti (a.s), kuma duk wanda bai yi riko da su ba, to ya kauce wa wasiyyar manzon Allah (s.a.w) da tafarkinsa. Sai dai hisabinsa yana ga Allah daidai gwargwadon saninsa ga wannan wasiyyar da kaucewarsa daga tafarkinsu da gangan.
Sannan kuma dole ne a rike su gaba daya, domin manzon rahama (s.a.w) ya yi umarni da cewa; riko da duka biyun ne kawai zai iya kubutarwa. Don haka duk wanda ya dauka riko da Kur’ani ba tare da su ba, ko riko da su ba tare da Kur’ani ba, zai kubutar daga bata, to babu gafalalle maras rabauta kamarsa, domin shiriya ba ta samuwa sai da biyun.
Kur’ani littafi ne mai fuskoki, akwai ayoyi masu sakakken bayani, akwai masu dabaibayi, akwai gamewa, akwai kaidi, akwai shafaffe da mai shafewa, akwai badini da zahiri, akwai bayyananne da dunkulalle duka a cikinsa. Don haka ne ma al’ummar ta sassaba sosai tsakaninta, amma sai manzon Allah (s.a.w) ya yi mata nuni da riko da mutanen da ba zasu taba barin Kur’ani bisa fahimtarsa kamar yadda yake ba, domin ya ba su wannan ilimin yana hannunsu. Don haka biyayya garesu ne kawai zata tseratar da al’umma daga kauce wa tafarkin gaskiya da ya bari.
Daular Banu Umayya da ta Abbasawa da suke tsananin gaba da Ahlul Baiti (a.s) sai suka ga bai kamata wannan falala ta kasance garesu ba, don haka ne suka kirkiro hadisai domin ya kalubalanci wannan ingantaccen. Amma dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, domin malamai sun tona asirinsu.
Duba hadisin da suka kirkiro mai cewa: Sahabbaina kamar taurari ne, duk wanda ka yi riko da shi, to ka shiriya. Amma sai ga manyan malaman Sunna da kansu sun tafi a kan cewa: Kage ne aka yi wa Annabi (s.a.w). Daga cikinsu akwai: Talkhisul Khabir: 4/191, A'alamul Muwakki'in: 2/242, da sauransu.
Ibn Hazam yana cewa: Da wannan hadisin ya inganta to da ya halatta a sayar da giya kuma a sha saboda koyi da Samura dan Jundub, da kuma haramcinta gun sauran sahabbai. Da barin wankan janaba saboda kasala ya halatta kamar yadda yake gun Usman da Dalha, kuma haramun gun A’isha da Ibn Umar. Ya ce: Yaya kuwa zai halatta a bi mutanen da suna sabo, kuma suna yin daidai?! Ya ce: Abin da yake wajibi mu bi shi ne abin da Allah ya zo da shi ta hannun manzonsa (s.a.w). Duba: Al'ihkam fi Usulul Ahkam: 6/244, 5/62, 6/239-240.
Haka nan idan sun ce: Ai an yi umarni da riko da sunnar halifofin manzon Allah (s.a.w), sai mu ce: Idan kuna nufin halifofinsa wadanda suka gaje shi ne, to shi ma ba zai yiwu ba, domin dukkaninsu idan ka cire Ali da dansa Hasan (a.s), sauran duka suna saba wa sunnar manzon Allah (s.a.w), sannan suna jahiltar da yawa daga hukuncinsa.
Duba ka gani Abubakar kansa yana saba wa addini, sannan ya yi nadama kan wasu abubuwa da ya yi, sannan yana furuci da jahiltar wasu hukunce-hukuncen. Ibn Kutaiba madogara gun Sunna da mai biye masa Dabari sun ruwaito cewa: Halifa na farko Abubakar dan Abi Kuhafa yana fada yayin da zai mutu ya yi nadama ina ma dai bai sanya an kai mamaye da samame gidan Sayyida Zahara (a.s) ba". Ina ma dai bai yi mulkin al'umma ba, ina ma dai bai …, da kin bin Usama saboda la'anar da aka yi wa wanda ya ki bi…, da kin tsayar da hakkin kisa da zina kan Khalid…" da sauransu. Ibn Kutaiba Addinuri a littafin Imama WasSiyasa yana mai cewa: Abubakar ya ce: Ya yi nadamar abubuwa uku; da ya sani da ya bar su bai yi ba. Da kuma wasu uku da ya bari; da ya sani da ya yi su. Uku kuma ina ma dai ya tambayi mazon Allah (s.a.w) game da su: sai ya ambaci ukun da ya yi nadamar yin su kamar haka:
Na daya: Mamaye gidan zahara (a.s) koda kuwa an kulle shi a kan yakar sa ne. Na biyu: Ina ma dai bai karbi shugabanci ba ya ba wa Umar ko Abu Ubaida ya huta. Na uku: Ina ma dai ya kashe Fuja'atus Salami ko ya sake shi bai yi masa ukubar da ya yi masa da wuta da kunyatawa. Sai kuma ya kawo wanda ya so a ce bai bari ba ya yi su kamar haka; Na daya: Ina ma dai ya kashe Ash'as dan Kais. Na biyu da na Uku: Ina ma dai da ya tura Khalid bn Walid Sham ya tura Umar Iraki. Amma ukun da ya
so a ce ya tambayi manzon Allah (s.a.w); Na daya: Ina ma dai ya tambaye shi waye shugaba bayansa don haka babu wani mai jayayya. Na biyu: Ina ma dai ya tambaya ko Ansar (mutanen Madina) suna da wani rabo a mulki. Na uku: Ina ma dai ya tambaya game da gadon 'Yar dan'uwa da Amma.
Haka nan ma Ibn Abil hadid bahanife ya kawo yana mai nakaltowa daga Mubarridu yana mai fadin wannan lamarin da muka kawo daga Ibn Kutaiba, har da karin cewa: Ina ma dai ya tambayi waye shugaba bayan Annabi (s.a.w), da haddi, da cin yankan Ahlul Kitabi. Kuma ina ma dai bai mamaye gidan Fadima ba, da nadamar kin bin rundunar Usama, da barin Ash'as. Da fadin: Ina ma dai ya yi wa Khalid bn Walid kisasin kashe Malik bn Nuwaira, da kuma ina ma dai ya kashe Uyaina dan Hasin da Dalha dan Khuwailid.
Umar da Usman kuwa an kawo abubuwa masu yawa da suka yi na saba wa sakon manzon Allah (s.a.w), wannan kuwa ba zai yiwu ba, domin manzon Allah ba zai zo da abu ba, sannan kuma sai ya sanya mai gadon kujerarsa ya shafe sakon Allah.
Misali: Umar ya kawo sallar asham, ya shafe auren mutu’a, ya canja wurin makamu Ibrahim, ya shafe wani bangare na kiran salla. Haka ma Usman ya hana hajjin tamattu’i, ya hana sallar kasaru, ya yi abubuwan da su kansu sahabbai suka kashe shi a kansu. Hada da cewa: Nana A’isha tana cewa: Ku kashe Na’asal (wato Usman) domin kafiri ne (al'imama wassiyasa: 1/51), muna ganin yadda lamari ya kai ga Nana A’isha ta kafirta shi. Sannan wadanda suka zo bayansu na Umayyawa, da Abbasawa, yawancinsu mashaya ne, da azzalumai wadanda ba abin da suka sanya gaba sai yakar zuriyar manzon Allah (s.a.w) da ganin bayanta.
Idan dai dukkan sunnar sahabi ko wadancan halifofi hujja ce: To ke nan da ya halatta duk abin da kowane sahabi ko halifa ya yi, mu ma sai mu yi. Alhalin bayan abubuwan da muka ambata, muna ganin wasu daga cikinsu sun kashe jikokin manzon Allah (s.a.w) da ‘ya’yansa. Mu’awiya ya sanya la’antar Imam Ali (a.s) a kan mimbari a karshen kowace huduba, kuma aka kira ta Sunna, daga nan ne ake cewa da masu la’antar Imam Ali (a.s) Ahlussunna. Tarihi ya zo cewa; Idan limami ya manta da la’anar Ali (a.s), sai mutane su yi ca a kansa cewa; Ka bar Sunna! Ka bar Sunna!, don haka sai ya yi la’anar sannan sai a yi salla. (Alkaulul Fasal: j 2; s: 384)
Idan dai dukkan sunnar sahabi ko wadancan halifofi hujja ce: To ke nan da ya halatta a kafirta Usman saboda koyi da A’isha, a yaki Imam Ali (a.s) wasiyyin annabin rahama (s.a.w) saboda koyi da ita, ko kuma shugaban kasa ya kwashe dukiyar kasa ya ba wa danginsa saboda koyi da Usman, ko ma ya kashe shi saboda koyi da sahabbai! Ko ya sha giya ya halatta ta, ko ma ya zina saboda koyi da wadanda suka yi!
Ko ya kwanta da matar wani kamar yadda Khalid ya yi da matar Malik bin Nuwaira mai suna Ummu Jamil bayan ya kashe shi, har ya jawo sabani tsakanin Abubakar da ya ki yi masa haddi, da Umar da ya ce: Sai an yi masa haddi. Don haka sai ka je gidan wani ka kashe shi don ana da sabani da shi da daula, ka kwanta da matarsa ta karfin tsiya! alhalin duk musulmi ba mu ga suna halatta haka ba.
Don haka ingantacciyar magana ita ce: Manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da riko da ahlin gidansa su sha biyu, kuma ya kira su da halifofinsa kamar yadda ya zo a duk littattafan Sunna da Shi'a. Cewa: Bayana akwai halifofina goma sha biyu, kuma dukkaninsu daga Kuraish. A wata ruwaya: daga "Banu Hashim". Da fadinsa: Kuma alkiyama ba zata tashi ba, sai na goma sha biyunsu ya tafi. Don haka umarni da riko da littafin Allah (s.w.t), da ahlin gidansa kuma halifofinsa goma sha biyu da ya yi wasiyya da su, shi ne ake nufi da riko da sunnar halifofinsa, ba sunnar duk wanda ya hau kan mulki ba. Domin wadanda ya yi wasiyya da su a matsayin halifofinsa biyu ne kawai daga cikinsu suka riki jagorancin al’umma, na farko Ali (a.s), na biyu Hasan (a.s), da aka tilasta wa yin sulhu da Mu’awiya ko ya fuskanci kisa!.
Hadisin “Shugabanni daga kuraishawa ne, kuma suna cikin Banu Hashim, ba na waninsu ba ne, kuma shugabanci ba ya yiwuwa ga waninsu” .
Muslim ya ruwaito daga Jabir daga Samura cewa ya ji Annabi (s.a.w) yana cewa: “Addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa har sai alkiyama ta tashi ko kuma an samu halifofi goma sha biyu a gareku dukkaninsu daga Kuraish”. A wata ruwaya sai Annabi ya fadi wata kalma da ban ji ba, sai na tambayi babana: mene ne manzon Allah ya ce: Sai ya ce: “Dukkaninsu daga Kuraishi suke” .
A wata ruwaya ya ce: “Dukkaninsu daga Banu Hashim” .
Ahmad da Hakim sun rawaito da lafazin Hakim daga Masruk ya ce: Mun kasance muna zaune a wani dare gun Abdullahi dan Mas’ud yana karanta mana Kur’ani sai wani mutum ya tambaye shi: ya Aba Abdurrahman shin kun tambayi Annabi (s.a.w) halifa nawa ne zai mallaki al’amarin wannan al’umma? Sai Abdullahi ya ce: Tun da na zo Iraki ba wanda ya tambaye ni wannan kafin kai! Sai ya ce: Mun tambaye shi sai ya ce: “Goma sha biyu ne, da adadin zababbun Banu Isra’il” .
Sannan duk wanda ya yi da’awar cewa; yana son Ahlul Baiti (a.s) da bakinsa, amma ba mu ga yana yin riko da tafarkinsu ba, kuma muka ga yana gaba da mabiyansu, to wannan mutumin karyar so yake, domin duk wanda yake son abu to zai kiyaye shi, ya yi riko da shi. Don haka masu tunanin son Ahlul Baiti (a.s), alhalin suna gaba da tafarkinsu da mazhabarsu, da mabiyansu, to suna yaudarar kawukansu, kuma su masu karyar so ne.
Da yawa zaka samu mutane suna karyar soyayya ga manzon Allah da alayensa, alhalin hatta da a salati sun cire sunan alayen manzon Allah (s.a.w), wadanda kuwa suka yarda su raba alayensa kamar yadda yake a salati, su kuma sai suka zo da bidi’a suka kara sahabbai domin kada falalar ta samu alayen manzon Allah (a.s) kawai.
Don haka duk wanda ya ce: Yana son Allah (s.w.t) ko annabinsa (s.a.w), ko alayen annabinsa (a.s), amma kuma muka ga yana saba musu, yana ma gaba da masu bin tafarkinsu, to wannan shi kansa ya san ba mai so ba ne, makaryaci ne, kuma shi kansa ya san yana yaudarar kansa ne.
Don haka gaskiya ta fito fili ga mai son riko da ita, babu wata mafita garemu al’ummar musulmi sai mu koma kan wasiyyar manzon Allah (s.a.w) da alayensa goma sha biyu (a.s), domin mu samu izza da tsiran duniya da na lahira.
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Wednesday, October 07, 2009
Ƙara sabon ra'ayi