Siffofin Imamai

Siffofin Imamai

Mun yi imani cewa imami kamar yadda annabi yake, wajibi ne shi ma ya zama mafificin mutane a siffofin kamala, kamar jarumtaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al’amura, da hankali, da hikima, da kuma kyawon dabi’u, dalilinmu na wajabcin samuwar wadannan siffofi ga Annabi shi ne dalilinmu na wajabcin siffantuwa da wadannan siffofi ga imami.
Amma game da iliminsa kuwa, shi yana samun ilmi da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukkan saninsa ta gurin Annabi ne, ko kuma daga Imamin da ya gabace shi, Idan kuwa aka sami wani sabon abu, to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhama da karfin kwakwalwar da Allah ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al’amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure, kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka ko koyarwar malamai, duk da yake iliminsa yana iya karuwa, shi ya sa Annabi (S.A.W) a addu’arsa yake cewa: “Ubangiji ka kara mini ilimi”[2].
Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowane mutum yana da wata sa’a ayyananniya ko wasu awowi a rayuwarsa da yakan san wani abu da kansa ta hanyar kaifin fahimta wanda shi a kan kansa wannan reshe ne na ilhami, saboda abin da Allah ya sanya masa na karfin yin haka. Wannan karfi yana sassabawa da sabawar mutane a karfinsa da rauninsa, da yawansa da karancinsa. Sai kwakwalwar mutum ta kai ga sani da ilimi ba tare da ya bukaci wani tunani ba, ko kawo mukaddima da hujjoji na hankali, ko kuma koyawar malamai ba, kuma saudayawa mutum yakan sami irin haka a kan kansa a rayuwarsa, Idan kuwa al’amarin haka yake to ya halatta mutum ya kai ga kololuwar daraja da kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami, wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da, da na yanzu suka tabbatar da shi.
Karfin ilhama a gun imami ana cewa da ita “kuwwa kudsiyya” wato karfi daga Allah, da take mafi kamalar kololuwar darajar ilhama, sai mai wannan siffa a kowane lokaci a kuma kowane hali ya so ya san wani abu sai ya san shi ba tare da mukaddima ba ko koyarwar wani malami, sai ya koma wa wannan abin jahiltar domin saninsa sai ya san shi tare da taimakon wannan karfi da Allah ya ba shi, sai ilimi da wannan abu ya bayyana gareshi tamkar yadda bayyanar surar abu take bayyana a tsaftataccen madubi.
Wannan kuwa abu ne bayyananne a tarihim Imamai (A.S), su a wannan fage kamar Annabi suke ba su taba yin tarbiyya ko neman ilmi a hannun kowa ba, ba su koyi karatu a gurin wani malami ba tun daga farkon rayuwarsu har zuwansu shekarun balaga, karatu ne ko kuwa rubutu, bai tabbata ba cewa daya daga cikinsu ya shiga gurin koyon rubutu ko ya yi almajiranci a hannun wani malami a kan wani abu, duk kuwa da cewa suna da matsayin ilimi da ba a iya kintatawa, kuma ba a taba tambayar su wani abu ba face sun ba da amsarsa a lokacin da aka tambaya, ba a taba jin kalmar ban sani ba daga bakinsu, ko kuma jinkirta ba da amsa har sai sun yi nazari ko tunani ko makamancinsu, alhali kuwa ba zaka taba samun wani daga cikin manyan malaman fikihu ba sai ka ji an ambaci wanda ya tabiyyatar da shi ya koyar da shi, da kuma wadanda ya karbi ruywaya ko ilimi a hannunsu, da kuma dakatawarsu a wasu mas’aloli ko kokwantosu a mafi yawa daga ilimomi, kamar yadda yake a kowane zamani da kowane guri.Biyayya Ga Imamai
Mun yi imani da cewa Imamai su ne “Ulul’amri” Shugabannin da Allah ya yi umarni a yi musu biyayya, kuma su masu ba da shaida ne a kan mutane, kuma su ne kofofin Allah kuma tafarki zuwa gareshi, masu shiryarwa zuwa gare shi, su ne taskar iliminsa, masu fassara wahayinSa, rukunan TauhidinSa, ma’ajiyar saninSa, don haka suka kasance aminci ga mazauna bayan kasa, kamar yadda taurari suke aminci ga mazauna sama kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S.A.W).
A wani hadisin yana fada: “Misalinsu a cikin wannan al’umma tamkar jirgin Annabi Nuhu (AS) ne wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya dakata ya bar shi to ya nutse ya halaka. Kuma ya zo a Kur’ani mai girma “Su sai dai bayin Allah ne ababan girmamawa, ba sa rigonsa da magana, kuma su da umarninsa masu aiki ne”. Surar Anbiya: 26-27. Kuma su ne wadanda Allah ya tafiyar masu da dauda ya tsarkake su tsarkakewa.

Wallafar: Allama Muzaffar
Fassarar: Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi