Bayana Imamanci

Bayana Imamanci

Imamanci yana daga cikin Usuluddin wadanda imani ba ya cika sai da kudurcewa da su, kuma bai halatta a yi koyi da iyaye da dangi da malamai a cikinta ba komai girmansu da darajarsu kuwa, abin da yake wajibi shi ne, a nemi sani, a yi bincike game da shi, kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.
A takaice, sauke nauyin da yake kan baligi da aka wajabta masa, ya dogara ne a kan imani da imamanci tabbatarwa ko korewa, koda mun kaddara cewa imamanci ba ya cikin shika-shikan addini da ba ya halatta a yi koyi a cikinsu, duk da haka ya wajaba a yi imani da ita ta fuskacin cewa; sauke nauyin da Allah ya dora wa baligi ya wajaba a hankalce, kuma dukkaninsu ba sanannu ba ne a yanke, saboda haka wajibi ne mu koma wa wanda muka san mun sauke nauyin da yake kanmu ta hanyar biyayya gareshi, ko ya zamanto imami (A.S) a mazhabar imamiyya, ko waninsa a wasu mazhabobin.
Kamar yadda muka yi imani da cewa annabci tausasawa ce daga Allah, kuma ba makawa a kowane zamani ya kasance akwai imami mai shiryarwa da zai maye gurbin annabi a ayyukansa na shiryar da ‘yan Adam, da dora su a kan abin da yake maslaha a Sa’adar Duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancance ta, domin tafi da al’amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da ketare iya daga cikinsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da yake wajabta aiko da annabawa da manzanni shi ne yake wajabta sanya Imami bayan Manzo (S.A.W).
Saboda haka ne muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi, ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. Imamanci ba zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al’amarinsu ba ne da idan suka so zasu nada wanda suke son nadawa, ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan ba tare da Imami ba. Ya zo cewa: “Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu mutuwa irin ta jahiliyya” kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a hadisi ingantacce.
A kan haka bai halatta ba wani zamani daga zamanoni ya kasance ba tare da imami da yake wajibi a yi masa biyayya ba, wanda yake ayyananne daga Allah (S.W.T), shin mutane sun ki ko ba su ki ba, sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, yana rayuwa a cikinsu ne ko kuwa yana boye ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya boyu daga ganin mutane kamar yadda ya boyu a cikin kogo da shinge, haka nan yake game da imami (A.S), kuma a hankalce babu bambanci tsakanin gajeriyar boyuwa ko mai tsawo[1].
Madaukaki ya ce: “Kuma ga kowace a’lumma akwai mai shiryarwa”. Surar Ra’ad: 8. Da kuma fadinsa: “Kuma babu wata al’umma face sai mai gargadi ya zamanto a cikinta”. Surar Fadir: 22.Ismar Imamai
Mun yi Imani da cewa wajibi ne ga Imami ya zama katangagge daga dukkan munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da gangan ko da rafkanwa, kamar yadda annabi yake. Haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga rafkanwa, da kuskure, da mantuwa, domin Imamai su ne masu kare shari’a, masu tsayar da ita, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin da ya hukunta mana imani da ismar annabawa kuwa, shi ne ainihin dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba.
Ba wani abu ba ne a wajan Allah   Ya sanya duniya a cikin abu daya

Wallafar Allama Muzaffar
Fassarar Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi