Musulunci da Kiristanci - 2

Tattaunawar Musulunci da Kiristanci - 2

Maryam (a.s) ta kasance mai matsayi mai daraja wurin Allah ta yadda Allah (s.w.t) ya kasance yana aika mala’ikansa ya yi magana da ita, ta kasance daga cikin bayin Allah zababbu da ake yi wa ilhama tsira da amincin Allah ya tabbata gare ta da danta. A nan ne zamu ga wasu siffofi da sayyida maryam da sayyida Zahra (a.s) suka yi tarayya a ciki, sai mala’ika Jibril ya kasance yana zo wa Fatima (a.s) yana yi mata magana har aka tara wannan bayani da aka kira su da Mushafin Fatima (a.s).
Haka nan dan maryam annabi Isa (a.s) ya yi magana yana cikin zanin reno yana jariri, amma ita Fatima ‘yar Khadiza (a.s) ta kasance tana magana da babarta tun tana ciki, wannan mu’ujiza mai girma ta Khadiza da ‘yarta ce ta sanya annabin rahama (s.a.w) yana tambayarta da waye kike magana? Sai ta amsa masa cewa da abin da yake cikina. Kusan muna iya cewa: Karamar mu’ujizar ta dara wacce aka yi magana a jaririntaka, domin abin da yake cikin cikin mahaifa ya fi nesanta da iya yin magana.
Ubangiji yana kawo wa maryam (a.s) abinci da ‘ya’yan itaciya daga aljanna, har annabi Zakariyya (a.s) yakan tambaye ta: Daga ina kika samu wannan?. Sai ta ce masa: Daga Allah ne!. Haka nan Allah madaukaki yake kawo wa sayyida Zahra (a.s) ‘ya’yan itaciya daga aljanna sai Imam Ali (a.s) ya tambaye ta daga ina kika samu wannan? Sai ta ce masa: Daga Allah ne!. Allah (s.w.t) yana arzuta wanda ya so ba tare da wata wahala ba.
Annabi Isa (a.s) ya kasance mai yawan mu’ujizozi da yawa da suka hada da tayar da matattu, warkar da makafi da kutare da duk wani mai cuta mummuna mai nakasarwa, yin tsuntsaye na kasa da ba su rai. Amma musulunci bai yarda da cewar ya yi giya ba kamar yadda littafi mai tsarki yake kawowa, kamar yadda ita kanta Attaura ta haramta giya.
Ya kasance ya kira mutane zuwa ga gaskiya da kyawawan halaye da rike amana, da yin adalci, da cika alkawari, ya samu taimako daga mabiyansa don isar da sakonsa, sai dai ya samu wahala mai tsanani daga munafukai daga cikin sahabbansa har wasu suka karbi kudi suka taimaka don halaka shi. Wasun ma sun hada kai da azzalumai mahukuntan Isra’ilawa da na Gwamnatin Rum mai mulkin mallaka don a gama da shi.
A lokacin da gwamnatin Rumawa ta yardar wa Yahudawa kashe annabi Isa (a.s) ko kuma ta zare hannunta da nufin cewa wannan lamarin matsala ce tsakanin yahudawa sai yahudawa suka dauki niyyar ganin bayansa da kashe shi. Munafuki daga sahabban annabi Isa (a.s) da aka fi sani da Yahuda (Yahuza) ya ba su hadin kai don shirya yadda za a kashe shi da nuna wa makisan inda yake.
Lokacin da suka zo sai Yahuda (Yahuza) ya ce: Bari in dubo muku shi. Sai ya shiga don ya duba Isa (a.s). sai Allah madaukake ya dauke Isa (a.s) daga cikin sahabbansa suna gani yana mai yi musu wasiyya, kuma nan take ya jefa wa Yahuda (Yahuza) siffar annabi Isa (a.s). sai suka kama Yahuda (Yahuza) suka tsire shi yana rataye har kwanaki uku. Wannan shi ne abin da Musulunci yake cewa sabanin Kiristoci da suka tafi a kan cewa annabi Isa (a.s) ne aka tsire.
Annabi Isa (a.s) ya tafi yana mai kokawa da halin al’ummarsa, yana mai yi musu wasiyya da zuwan fiyayyen halitta wanda shi ne zai zo da tsarin da ya fi kowanne a tarihin dan Adam, yana mai gaya musu zuwa fiyayyen halitta wanda dukkan annabawa suka yi albishir da zuwansa daga zuriyar ‘ya’yan ‘yan uwansu wato Isma’il (a.s). Wannan lamarin ne ya sanya da yawan Yahudawa suka yi hijira zuwa yankin larabawa don a haife shi a cikinsu sakamakon sanin siffar yankin da za a haife shi ya yi kama da yankin Madina da Makka.
Bayan wucewar annabi Isa (a.s) sai jama’arsa ta kasu gida daban-daban, wasu suka bi wasiyyarsa suna masu riko da wasiyyan da ya yi wasiyya da su har wasiyyai goma sha biyu kamar dai zababbun Banu Isra’ila na Musa (a.s). Wasu kuwa suka yi wa wannan wasiyya tawaye har sai da Bulus masanin falsafar Indiyawa da Rumawa da Iraniyawa da ya dade yana kashe Kiristoci ya mika wuya ga kiristanci ya zo ya yi da’awar shi ne ya fi sanin addinin Isa (a.s).
Daga karshe Bulus ya ci galaba kan Musulmi (Nasarawan wannan zamanin) mabiya addinin Isa (a.s), ya raba kawukan mutanen, ya shigo da batun cewa Isa (a.s) dan Allah ne. Ya zo da fomular ubangizai uku kamar yadda yake a falsafar Indiyawa da Rumawa da Iraniyawa. Sai aka rabu gidaje daban-daban har zuwan sarkin Rum bayan Bulus da shekara 200 da ya karbi kiristanci yana mai goyon bayan wannan ra’ayi da Bulus ya soko shi cikin kiristanci.
Amma game da zunubin asali wani abu ne da musulunci ya yi kakkausan suka kansa, domin Allah madaukaki a bisa koyarwar musulunci yana karfafa cewar; Wata rai ba ta daukar zunubin wata rai. Don haka yaro ko babba wanda bai yi wani sabo ba a rayuwarsa ba a iya jifan sa da sabon da iyayensa suka yi balle kuma a dora masa shi. Don haka muna iya cewa: Zunubin asali da kiristanci yake ganin cewa; Zunubin da Adam da Hauwa (a.s) suka yi na cin itaciya da aka hana su, ya hau kan zuriyarsu ta mutane. Lamari ne da musulunci bai yarda da shi ba.
Sannan muna iya cewa zunubin da suka yi zunubi ne na barin abin da ya fi dacewa kamar yadda koyarwar Ahlul-baiti (a.s) ta yi nuni da hakan. Idan ma mun kaddara cewa zunubi ne babba to muna iya cewa; musulunci ya sanar da sakon Allah kan cewa sun yi addu’a da neman gafara zuwa ga Allah madaukaki sai ya yafe musu zunubansu. Kuma duk wani wanda ya yi sabo idan ya koma ga Allah madaukaki ya nemi gafara ya tuba ya kame ga barin yin sabon to Allah (s.w.t) zai gafarta masa zunubansa. Wannan ita ce dokar musulunci kan wanda ya yi sabo.

Idan muka waiwayi rahbaniyanci da zaman rashin aure da malama coci suke yi a yau tun farko zamu ga musulunci bai yarda da shi ba, kuma abin da yake faruwa a yau na fasikanci a coci-coci da ‘yan mata da kananan yara yana nuna gaskiyar ra’ayin musulunci kan wadannan mas’alolin, domin wadanda suke yin wannan danyen aikin zamu ga sun fake da addini ne suka fada cikin fasikanci sakamakon lalacewa da gurbacewar koyarwar da suka doru a kanta. Abubuwan kunya da suke faruwa a majami’ai musamman a kasashen turai ya isa abin kunya da ya kamata coci ta gane cewa ba ta nufi hanya ta gari mai inganci kan wannan mas’alar ba.
Haka nan idan muka waiwayi batun yafe zunubi da sabo da zamu ga yana faruwa bisa koyarwar coci shi ma ya zama hanyar kasuwanci da gyara wa mai yin laifi laifinsa, ta yadda muka ga mutane suna yin sabo sai su kawo kudi wurin malaman coci don su samu afuwa, kuma su malaman ne kawai zasu iya nema masa afuwa wurin Allah, don haka duk sabon da ya yi ana iya yin ciniki domin wanda ya kawo kudi mai yawa yana iya zunubi mai yawa kuma ya samu gafara sakamakon wannan kudi da ya kawo.
Haka nan batun abincin daren Ubangiji da aka yi shi ma ya saba wa addini sahihi da koyarwa ta gari, da girman da Allah yake da shi. Yanzu a ce idan aka ci gurasa da giya an ci naman Allah da jininsa ne, wannan kuwa ba zai kasance wulakanci ga ubangijin da aka yi wa hakan ba. kuma yaushe ne giya ta kasance halal a Attaura, ko masu wannan tunanin suna ganin cewa Isa (a.s) bai san cewa giya haram ba ce a Attaura har zai yi giya a sha.
Don haka ne zamu ga koyarwar musulunci ta kasance daidai da dabi’ar halittar dan Adam, kuma wannan koyarwar ce kawai zata iya samar wa mutum mafita a duniya da lahira. Musulunci ya umarni da yin aure da karfafar akidu na hankali da tunani sahihi ingantacce, rashin wannan ne koyarwar a coci ta sanya malaman coci suna ta fasikanci a cikin majami’unsu. Idan suna son koma wa ga tafarki na gari, to kuwa ya zama musu dole su kalli koyarwar musulunci da kyau su yi tunani su ga kyakkyawar koyarwar da Allah ya aiko annabinsa na karshe da ita.

Laccar: Sheikh Bahrami

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi