Ma’anar Shi’anci

Ma’anar Shi’anci
Wallafar Allam Muzaffar
Fassarar Hafiz Muhammad

Ma’anar Shi’anci Wurin Ahlul Baiti
Ahlul Baiti (AS) ba su da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga garesu. Don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su, kuma suka aminta da shi a kan sirrinsu, suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa, da kuma wanda yake kansa.
Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu ne kuma shi’arsu sai idan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa, mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin sha’awece-sha’awece da son ransu wadanda ke neman hanyar fandare wa bin Allah. Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana, da tsentseni da tsoron Allah.
“Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa” .
Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku” .
A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:
1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi : “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi”.
“Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.
2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan :
Abu Ja’afar (AS) “ Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?
Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.
Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan.
Sa’id: To halaka ke nan.
Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.
3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Alkinani .
Alkinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
Abu Abdullah: Menene abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?.
Alkinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu.
Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?
Alkinani: E mana.
Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
4- Abu Abdullahi (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da zamu kawo wasu kamar haka:
A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.
B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.
C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma, a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni, shi ba ya daga cikin masoyanmu”.
D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa, kokarinsa ya tsananta, kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa, ya kaunaci ladansa, ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi