Hakikanin Annabci

Hakikanin Annabci

Annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na Ubangiji (s.w.t) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zab'a daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daud'ar miyagun d'abi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan’adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta d'aukaka zuwa ga daraja mad'aukakiya a gidajen duniya da lahira.
Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai lud'ufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da d'an Adam, da kuma isar da sak'on kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah mad'aukaki bai ba wa mutane hak'k'in ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zab'ensa. Ba su da wani zab'i a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSa”. Surar An’am Aya ta 124.
Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargad'i, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a.
Annabci Tausasawa Ne
Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sark'afaffun gab'ob'i a halittarsa, da d'abi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane d'aya daga cikin mutane. D'abi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda d'abi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa[1][1], ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan d'abi’u[2][2] daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwad'ayin rayuwar dauniya, da adonta, da k'awarta, da tarkacenta, kamar yadda Mad'aukaki yake cewa:
“Hak'ik'a mutum yana cikin hasara”. Surar Asri: 2. “Hak'ik'a mutum yana d'agawa. Don kawai ganin ya wadata”. Surar Kalam:6-7. “Hak'ik'a rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wad'annan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake k'unshe da d'abi’u da kuma sha’awa.
A wani b'angaren, Ubangiji mad'aukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargad'i da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi.
Husumar cikin zuciya da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da d'abi’u, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan d'abi’arsa to yana daga cikin mafi k'ololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan’adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu. Amma wandanda kuwa d'abi’arsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu ci baya a ‘yan’adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi.
Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin b'ata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwad'ayin haka”. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wad'anda suke b'ullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya keb'antu da shi ne shi kad'ai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki d'aya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana k'ara jahilci ko kuma k'ara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na d'abi’a da sauran samammu na binciken ilimi ya k'aru ba.
Saboda haka mutum a tsananin buk'atarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana buk'atar wanda zai d'ora shi a kan hanya mik'ak'k'iya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta k'arfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa buk'atar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana k'ara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fand'arewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi ¬da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin wad'annan gwagwarmayar d'auki-ba-dad'i ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi.
Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya keb'ance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya had'a kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun had'u sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari.Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargad'i game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su.
Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai buk'atar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa.
Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah mad'aukaki ya bi shi, Allah ya d'aukaka ga haka d'aukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fad'inka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai tab'a yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.
[1] - “Da rai da abin da ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma tak'awarta”. Surar Shamsi: 7-8.
[2] - D'abi’a al’amura ne kamar k'i, so, fushi, yarda, da sauran halayen rai da zuciya.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Daga Littafin Muzaffar

Ƙara sabon ra'ayi