Samun Canji Ga D'an Adam

Canza Wa Mutane
 

Samun Canji Ga D'an Adam

Mutum halitta ce mai samun canje-canje da Allah mad'aukaki ya samar a cikin samammu, shi halitta ne da yake iya kasancewa mafi kamalara samammu, ko kuma ya zamanto mafi munin samammu.
Wannan murd'ad'd'en samamme mai wuyar sha'ani yakan sanya samun canje-canje a cikin rayuwar duniya, sai wannan canjin da yake haifarwa ya samar da sauyi mai bam mamaki a cikin hukunce-hukuncen mahaliccinsa, wannan kuwa yana iya kasancewa a cikin d'aid'aikun mutane ko kuma a cikin jama'a gaba d'aya a dunk'ule. Don haka ne ma sunnar Allah ta samar da canji a cikin bayinsa take sauyawa daidai gwargwadon samun canjin da ake samu a cikin d'an Adam da halayensa. Wannan sunnar ta Allah ba ta canjawa har abada a nau'in yanayi guda a kowane zamani, amma tana canjawa da canjawar yanayin zamani ne. "Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake garesu…". Ra'ad: 11. "Wannan domin Allah bai kasance mai canja wata ni'ima da ya yi wa wasu mutane ba har sai sun canja abin da yake garesu…". Amfal: 53. Sai a samu rahama idan mutane suka kiyaye lamarin Allah na rik'o da dokokin sabuban halittu da abubuwan da ya hore masu, sai kuma a samu azaba idan aka yi sakaci da abin da Allah mad'aukaki ya huwace wa bayinsa.
Idan mutane a bisa misali; suka yi rok'o da ni'imar da Allah ya ba su ta k'asa mai kyau, da ruwa mai dad'i, da iska mai lafiya, suka yi rik'o da kayan aiki da ya hore musu kamar fatanya ko kuma garma, ko kuma kayan noma na zamani, suka yi amfani da taki ko na gargajiya ko na zamani, sannan kuma suka yi amfani da k'arfin d'an Adam da ya ba shi na iya yin aiki, da kuma lokacin da ya fi dacewa a yi noma kamar damina, ko kuma amfani da tabki wurin noman rani, sannan sai suka yi amfani da iri, ko dashen shuka domin samar da abinci da 'ya'yan itaciya da sauran kayan marmari. Sannan suka himmantu wurin ganin sun kula da shukan nan da ba ta kariya daga duk wani abu da zai kawo mata hari mai had'ari gareta kamar ciyayi da dabbobi, da ma mutane masu kiwo da sukan iya lalata ta, da kuma b'arayi da sukan iya satar kayan gona!
To wad'annan sun yi rik'o da sabuban rayuwa da Allah (s.w.t) ya hore musu, kuma sunnar Allah a nan ta wajabta musu samun nasara kan abin da suka sanya gaba, sai yalwa da abinci su samu a cikin wannan al'umma, babu wata yunwa da zata kunno musu kai, babu wani bala'in rashin abin sawa a baka ko sha da zai durfafe su. Sai dai idan akwai wani b'angare na wani lamari kamar na alfahasha da ba su kiyaye ba, kuma Allah ya so ya jarrabe su da wannan, sai ya saukar musu da bala'i kamar na fari (rashin ruwan sama da bushewar k'asa), ko kuma fari (k'warin fari masu kai hari kan shuka). Amma shi ma wannan yana magani; idan abin ya shafi mummunan halaye ne to sai su yi ta yin istigfari, idan kuwa ya shafi kamar k'wari ne sai su had'a biyu; suna istigfari suna kuma feshin maganin k'wari, ta jirgin sama ne ko kuwa!?
A kowane fage wannan sunnar ta Allah tana da muhimmanci matuk'a, domin ita ce take gudana kuma take iko da kowane k'arfi, babu wani k'arfi da yake sama da ita, babu wani iko da ya isa ya shallake ta, babu wani wayo da ya isa k'etare ta, babu wata dubara da ta isa ta kauce mata. Abin da ya rage abu guda ne, samar da yanayi da zai iya samar da sunna ta faru daidai gwargwadon yanayin, sai yanayin rahama ya samu idan an yi rik'o da sabubban rayuwa a daidai, sai kuma yanayin bala'i ya faru idan aka yi rik'o da su ba daidai ba. Muhammad Bello yana gaya min cewa; akwai wani lokaci tsakanin 1995-1998 idan ban manta ba, da Jami'ar A.B.U zaria ta kasance kamar wani dausayi mani'imci, aka hana k'azanta da zubar da datti, aka sanya dokoki mai tsanani, sannan aka kyautata kayan rayuwa. Ya ce: Sai ga Jami'a ta koma kamar wani dausayin ni'ima mai dad'i, da walwala da shak'atawa, iskar ni'ima kamar ta sanyin safiya tana ratsawa! Wurin ya kasance wurin hutu ne ga masu son shak'atawa da hole rayuwarsu! Kamar dai ka ce ba a Nigeria wurin yake ba!
D'an Adam ke nan! haka Allah ya gindaya masa, idan ya yi daidai sai ya ga daidai, idan ya sab'a sai ga ba dad'i! Idan ya yi tsafta sai ya ga lafiya, idan ya yi k'azanta sai ya ga daud'a! Idan ya yi ilimi sai ya mallaki duniya ma, idan ya yi jahilci ko jaki sai dai ya yi masa gori! Wannan mutunci da Allah ya yi mana shi an wulak'anta shi a wasu wurare, yayin da zaka ga mutum yana halaye kamar na dabba!. Wannan mutumin mai daraja da zai shiga aljanna, shi ne dai yake kuma fad'owa k'asa warwas ya gangara wuta!
Idan ba mu yi nisa ba; ba na tsammanin a cikinmu babu wanda bai san labarin mutumin da ya ga wata mata mai kyau ba, sai ya rik'a cewa da abokinsa kai! Allah ya hore mana mu k'aro aure! Amma da ta iso kusa da shi sai suka ga ashe matarsa ce! Ahe sai idan zata fita unguwa ne take cin ado!
Babu wanda bai san yadda idan faransawa sun d'ibi fulanin daji sun kai su Faransa sun dawo da su ake manta cewa; wad'annan matan ne da ake k'yamar irinsu saboda sun rayu a wad'annan yankuna namu!
Babu wanda yake rashin takaici idan ya ji labarin wasu Yorubawa da aka kai Tehran a babban birnin Iran 1997-8 suka rik'a bud'e wandunansu a fili suna fitar da azzakarinsu suna yin fitsari a kan fulawowin da ake tak'ama da su alhalin ga ban d'aki da ruwa da komai!
Babu wanda ba zai ji haushi ba idan ya ji labarin yadda wasu 'yan k'asar Ghana su biyu suka zaro al'aurarsu a bakin Titin Bajak da yake birin K'um a gaban makarantar Jami'ar Imam Khomain a 2007, suna yin fitsari a cikin ruwan da yake gudana! Ihun da mutanen da suke wucewa suke yi domin ba su tab'a ganin hakan ba a rayuwarsu wai sai ma ya ba su haushi, wai suna gaya wa wani d'alibi daga Ghana cewa; wai don muna fitsari a nan sai kawai mutane suna yi mana kuwwa-kuwwa!
Kuma babu wani wanda ba zai ji haushi ba idan ya ga yadda mai gadi ya hana wani wanda ya matsu da bayan gida shiga band'aki saboda kawai ba d'an makarantar ba ne!.
Haka d'an Adam yake! Idan ya mutunta kansa sai Allah ya mutunta shi, idan kuwa ya k'i sai ya ga ba daidai ba! wannan ciwo ne da ya yi mana yawa har ya kashe al'ummunmu, sai muka taso al'umma mai yawan jahiltar kawukanmu, mai yawan munanan halaye, mai yawan son kanta, mai yawan neman ta kai abin da ba ta shirya masa ba, mai yawan k'azanta da rashin tsafta!. A wani b'angaren kuma mai matacciyar zuciya, da take ganin ba zata iya ba wa kanta mafita ba, har ma da yawa sun sallama wa abin da suka kira da k'addara! Sai dai mafi munin duka shi ne ganin da wasu suke yi wa wannan yanayi a matsayin daidai!. Jama'a ya kamata mu san cewa; Kur'ani da sunnar manzon Allah babban abin koyi ne, ma'aikin Allah da Ahlul Bati (a.s) sun yi a aikace, sun nuna mana misalin da ya kamata ya kasance ga d'an Adam a rayuwa.
Yaya duniya zata kasance da manzon Allah (s.a.w) bai zo da canji ba?! ko kuwa ya ya kake tsammanin halin da ba Banu Isra'ila zasu kasance da Musa (a.s) bai k'wace su daga hannun Fir'auna ba!? Yaya halin Banu Isra'il zai kasance da Isa d'an Maryam bai halarto ba? yaya kuwa kake tsammanin yammacin duniya a yau ba don Sabuwar haihuwa ba sakamakon canjin nan na juyin juya halin Faransa! Yaya kake tsammanin daulolin Afurka ba don zuwan turawa ba! yaya kake tsammanin wanzuwar masarautun da Gurguzu ya mamaye ba don zuwansa ba, yaya k'asar Sin zata kasance ba don motsin jagora Moi ba? yaya kuwa Nigeria take a yau ba don mamayar mallaka da had'e kudancinta da arawacinta ba?! Wad'annan duk wasu misalai ne da zasu iya nuni a fili yake cewa; D'an Adam wani halitta ne da idan ya canja sai a canja masa yanayin da ya zab'a! Daidai canjin da ya yi daidai sakamakon da zai faru a duniya, wannan kuwa yana iya kasance na k'warai ko maras kyau da amfani, yana iya kasance na ilimi ko jahilci.
Muna iya ganin yadda ilimin d'an Adam a yau ya canja komai na duniya, da ya yarda da jahilcinsa da bai kai wannan matsayin ba, a nan muna iya ganin canji yana iya kasancewa mai kyau ko maras kyau. A matsayinka na d'an Adam mai wannan baiwar ta Allah wane tunani ka yi domin samar da canji mai kyau cikin al'ummarka!? Wane yak'in ne ka yi da ranka domin samun canji a halayenka? Wane k'ok'ari kake yi domin ganin sauyi a cikin gidanku, da unguwarku, ko garinku? Ka yi tunani kai mutum cewa; kana da ikon canja komai, kada lalacin tunani ya sanya ka yank'e k'auna!.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi