Jahilci a Addini
Jahilci a Addini
Babu wani abu da ya fi "Jahilci" ko "Mummunar Fahimta" muni a cikin dukkan ciwowwukan da suka yi wa duniya k'awanya, kuma dai shi wannan jahilcin yana nan ya yi katutu a kowane fage, sannan kuma duk wani kuskure da d'an Adam yake cikinsa, ko kuma wani bala'i da yake damunsa ya kasance sakamakon wannan ciwon ne, wannan bala'in ko ciwon, ko kuma mu kira shi da matsala, yakan iya kasancewa a fagen addini, ko wayewa, ko siyasa, ko rayuwar al'umma, ko kuma tattalin arziki da makamantansu: sai dai a nan zamu so a kawo wasu bayanai da misaloli a fagen Addini:
Wasu mutanen sun d'auka kowa yana kan b'ata sai dai su ne a daidai, wasu sun wuce gona da iri da har sun d'aukar wa kawukansu cewa duk wani wanda ba su ba, to kafiri ne; wannan tunanin ya taso tun daga k'arni na 8 hijira, sannan sai ya kafu a gabas ta tsakiya, sannan ya watsu duniya a cikin shekaru 40 na k'arshe, kuma ya watsu har a Nigeria. A wasu k'asashen kamar Afganistan, da Somali, da Pakistan, da Ceceniya, da Thailand, da Philippine, d.s.s wannan ak'ida ta yi k'amari matuk'a musamman da yake ma'abota wannan ak'ida suna da makami a hannyensu. Sai kashe mutanen da ba su yarda da su ba! sai sanya musu bamabamai a cikin masallatai! Sai d'aukar mutane musulmi masu shaidawa da kalmar shahada, suna salla, suna azumi, suna hajji, suna zakka, da dukkan ayyukan da aka d'ora wa musulmi wajabcin yinsa, a matsayin kafirai. Yak'ok'in gwamnatin Pakista da masu irin wannan ak'ida ya fito a fili yayin da sukan sanya wa k'ananan yara bamabamai su aika su wani wuri domin su sayo musu wani abu, amma sai su tashi bom d'in bayan yaran sun isa wannan shagon da ake son tarwatsawa. Sannan mafi muni haramta makarantun boko, da karatun boko da wad'annan ma'abota ak'idoji suke da shi, muna gani a Pakistan bayan sun kame makarantar 'yan mata ta boko sai aka raba wa masu jihadi su a matsayin k'wark'warori. Ganin da wannan ak'ida take da shi na rashin alfarma ga kowa babu yaro ko babba, mace ne ko namiji, shi ne babban bala'i, don haka duk wanda yake ba ya ganin nasa ne, to ya halatta komai nasa, ya halatta jini, da dukiya, da mutunci!.
Wannan tunanin yana ganin "Tauhidi" kamar yadda ya fahimce shi ne asalin lamari, sannan kuma yana ganin tauhidin da mushrikai suka rasa a lokacin manzon Allah na Uluhiyya (shirka a Ibada) ne. Kuma duk wanda yake yin shirka a ibada kafiri ne, don haka jininsa, da dukiyarsa, da mutuncinsa ya halatta. Sannan kuma yana ganin duk wani tsani da mutum ya rik'a zuwa ga Allah shirka ne, wannan tsanin ya had'a da annabawa, da manzanni, da wasiyyansu, da sauran duk waliyyan Allah, don haka duk wani wanda yake yin tawassuli yake neman ceto a wurin wad'annan bayin Allah masu daraja a gun Allah mad'aukaki shi ma yana shiga cikin mushrikai koda kuwa ya fi kowa tsoron Allah a duniya!
Ba wannan ne duka bala'in ba, sai dai babbar musiba ita ce ta yi wa duk wani musulmi mai fahimtar da ta sab'a da wannan tunanin kan ma'anar Tauhidi hukuncin Kafirci! kuma kafircinsa ya fi na Abu Jahal da Abu lahab da sauran kafiran K'uraihawa! Kuma ya kasance an halatta duk abin da ya shafe shi! Don haka ne ma, masu irin wad'annan tunanin duk inda suka dira suka nemi kafa wata daula, to sai wurin ya yi kaca-kaca da yak'i, sannan kuma babu wani wanda ake kiyaye alfarmarsa, da jininsa, ko dukiyarsa, da mutuncinsa. Tarihin wannan ak'ida tun lokacin kafa ta da yadda ta ribace matan musulmi, da yadda aka hana musulmi zuwa hajji, da yadda aka takura wa da damansu a hajji, har ma da kisa saboda kawai sun yi wani abu da ya sab'a wa wannan fahimtar ba b'oyayye ba ne!.
Wannan tunanin yana ganin addu'a a matsayin fami girman lamari, kuma yana ganin dukkan na baya sun yi kuskuren fahimtar ma'anar ibada, sannan yana ganin laifin manyan malaman lugga a kan yadda suka fassara ma'anar addu'a bai yi daidai da yadda shi yake gani ba, sannan kuma yana da sab'ani kan cewa wanda ya rik'i tsani zuwa ga Allah mushriki ne ko kuwa sai ya yi addu'a wato kira sunan wannan tsanin da ya rik'a kamar annabi ko wani waliyyi!? Ko ma dai me ye, wannan tunanin yana da nasa nazari kan Tauhidi kuma ya yi aiki da shi a aikace; don haka ne ma muka samu yanayin gwamnatoci da aka kafa k'ark'ashin wannan tunanin sun zubar da jinin musulmi mai yawa da sunan kawar da shirka ko bidi'a daga cikin addini. Ina ma dai wannan tunanin zai d'auki ra'ayinsa a matsayin bambancin fahimta ta yadda kowa zai yi nasa, ina ma dai wannan tunanin bai rushe kayan tarihi da k'aburburan bayin Allah salihai ba! Ina ma dai ya kiyaye mana tarihin musulunci bai rushe shi ba!
Wannan ak'ida ta dogara da ayar: "Ku kashe kafirai duk inda kuka same su". Sannan sai ta fassara kafirai da cewa sun had'a da musulmin da ba fahimtarsu d'aya ba kan Tauhidi! a yau muna ganin yadda ya rikid'e ya kasance mai tsanin huce haushinsa kan musulmi! Bai bar yaro ba ko tsoho balle samari! Bai bar wani masallaci ba da yake son halakawa sai da ya sanya masa bom ya kashe duk masu sallar ciki! bai bar duk wani wuri da musulmi suke zuwa domin ziyartar k'aburburan bayin Allah ba, balle kuma wurin hutu da kasuwannin musulmi da suke zuwa domin neman halal! Bai bar alfarmar jini ba, da ta dukiya, balle mutuncin musulmi duk da sunan yak'i da kafirci. Don haka ne sai ya kasance duk inda ya dira ya yi k'arfi ya d'auki makami, farkon wanda yake d'and'ana kud'arsa shi ne musulmi! Irak'i babban hadafi ne da wannan ak'ida ta samun wurin ayyukanta!.
Babbar matsalar wannan tunanin sandarre da ya k'one mana kayan tarihi k'urmus, ya halatta jinanai masu yawa a duniya, ta taso ne daga k'in wasu ilimomin masu gina tunanin d'an Adam da lurasshe shi zuwa ga lud'ufin Allah da kamalar d'an Adam, da kuma fuskantar k'imar da Allah ya sanya ta ga bayinsa na gari kamar Annabawa (a.s). Wannan tunanin muna gani a fili ya k'yamaci ilimin Usul mai zurfi, ya kuma sanya d'amarar gaba da k'iyayya mai tsanani, da kafirta tunanin hankali, don haka sai ya kasance mafi girman mak'iyinsa shi ne; Ilimin Palsapa, da Irfani, da Mantik'. Sannan kuma yana tsananin rik'o da koyarwar gidan Umayyawa ta gaba da k'iyayya da gidan Banu Hashim da duk wata zuriyar manzon Allah (s.a.w).
Ahlul Baiti (a.s) a matsayinsu na wad'anda manzon Allah (s.a.w) ya bar mana su tare da Kur'ani kamar yadda ya inganta a hadisai masu yawa a Sihah na daga ingantattun Littattafai da sauransu ba su tab'a yarda da kafita musulumi ba. Su rahama ne ga dukkan talikai kamar kakansu (a.s), sannan kuma su k'ofa ce ta rangwame da k'auna, k'ofar tuba da kawar da kai daga kurakuran bayi, sannan kuma kullum suna yin addu'a ne ga bayin Allah. Kuma sun kasance masu tsananin tausayi da taimakon raunanan bayi, ga kuma ilimi da dukkan zamunnansu aka yi musu sheda da shi, amma ba su tab'a zuwa da irin wannan tunanin ba, haka ma sahabbai ba a tab'a samun wani daga cikinsu da irin wannan tunanin na kafirta musulmi ba, sai dai a wannan zamanin mun ga masu wannan tunanin sun nuna sun fi wad'annan bayin Allah sanin mene ne Tauhidi!.
Ta wani b'angare kuma da akwai sabon tunani da ya faru a k'arnin da ya gabata na wasu masu tunanin kafirta al'umma bisa la'akari da tsarin da take kai. Tunani ne da ba ya kafirta d'aid'aikun musulmi, amma sakamakon tsarin da suke bi, ko kuma yake tafiyar da su ba na musulunci ba ne, to suna ganin wannan yana sanya al'umma ta kasance ta kafirci. Wannan tunanin duk da ba shi ne wanda muka kawo a addini ba, domin shi wannan yana maganar siyasar addini ne ba kamar na farko ba da yake maganar tauhidin addini wanda yake asasin addini, sai dai shi ma yana iya kai wa ga ganin al'umma a matsayin kafira, koda kuwa bai kai ga ganin musulmi a matsayin kafirai ba.
Ahlul Baiti (a.s) a matsayinsu na wad'anda manzon Allah (s.a.w) ya bar mana su tare da kur'ani ba su koyar da irin wannan tunanin ba, don haka ne muka samu wad'anda suka yi koyi da su da aka fi sani da Shi'a ba su tab'a kafirta wata al'umma ba. Babban abin da suka sanya gaba a kowane zamani shi ne; tarbiyyantar da al'umma, da neman ci gabanta a kowane fage, da kare ta daga fad'awa b'ata, da d'amafara ta da wad'anda Allah ya ce a bi da ya had'a da Kur'ani da Sunnar Annabi, da kuma lurasshe da ita domin ta yi rik'o da wasiyyar manzon rahama (s.a.w) na yin rik'o da Kur'ani da Alayensa (a.s), don haka siyasar musulunci shi ne rik'on da wad'annan lamurra masu tsarki da daraja da bin wasiyyarsu!.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Ƙara sabon ra'ayi