Adalcin Allah

Adalcin Allah
Adalcin Allah yana daga siffofin Allah mad'aukaki tabbatattu na kamala cewa shi adali ne ba azzalumi ba, ba ya take hak'k'i a shari’arsa ba ya zalunci a hukuncinsa, yana saka wa masu biyayya kuma yana da hak'k'in hukunta masu sab'o, ba ya kallafawa bayinsa abin da ba zasu iya ba, kuma ba ya yi musu uk'uba fiye da abin da suka cancanta.
Kuma mun yi imani cewa Ubangiji ba ya barin aikata abu mai kyau matuk'ar ba wani abin da zai hana aikata shi, kuma ba ya aikata mummuna saboda Shi mai k'udura ne a kan ya aikata kyakkyawa ko ya bar mummuna, tare da cewa yana da sani game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna, da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan, babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balle ya bar shi, babu kuma wani mugun aiki da yake buk'atarsa balle ya aikata shi, tare da cewa shi mai hikima ne ba makawa aikinsa ya kasance ya dace da hikima kuma a bisa tsari mafi kamala.
Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki to da al’amarin hakan ba zai rabu da d'aya daga cikin surorin nan hud'u ba:
1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma gajiya ga barin aikata shi.
3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma gajiya ga barin sa ba, sai dai yana buk'atar aikatawa.
4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma buk'ata gareshi, sai al’amarin ya tak'aita ke nan a kan cewa aikisa ya zama bisa sha’awa da wasa.
Dukkan wad'annan siffofi sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna.
Sai dai kuma wasu sashen musulmi sun halatta wa Allah (s.w.t) aikata mummuna, suka halatta cewa zai iya azabtar da masu biyayya, ya kuma shigar da masu sab'o aljanna kai hatta kafirai ma, kuma suka halatta cewa yana iya d'ora wa bayinsa abin da ya fi k'arfinsu da abin da ba zasu iya ba, tare da haka kuma ya azabtar da su a kan ba su aikata ba. Kuma suka halatta zalunci da danne hak'k'i, da k'arya da yaudara ga Allah mad'aukaki, da kuma aikata aikin da babu wata hikima, da manufa, da maslaha, da fa’ida, da hujjar cewa shi: “Ba a tambayar sa a kan abin da yake aikatawa amma su ana tambayar su”. Surar Anbiya: 23.
Da yawa daga cikin irin wad'annan da suka suranta Shi a kan wannan Ak'ida tasu b'atacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, Ja’iri, mai wauta, mai wasa, mak'aryaci, mai yaudara, da yake aikata mummunan aiki yana barin kyakkyawa, Allah ya d'aukaka ga aikata wad'annan abubuwa d'aukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa[1].
Kuma Allah Mad'aukaki yana cewa: “Kuma Allah ba ya nufin zalunci ga bayi”. Surar Mumin: 23. “Kuma Allah ba ya son b'arna”. Surar Bak'ara: 31. “Kuma ba mu halitta sammai da k'asa da abin da ke tsakaninsu muna masu wasa ba”. Surar Dukhan: 205. “Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini”. Surar Zariyat: 56. Da sauran ayoyi masu girma, tsarki ya tabbata gareka ba ka halicci wannan don b'arna -rashin manufa- ba.

Fassarar Littafin Muzaffar
[1] - A sani masu wannan ra’ayi suna magana ne a matakin yiwuwa a hankalce saboda musunsu ga rawar da hankali zai iya takawa a wannan fage, amma a aikce ba su siffanta shi da wannan miyagun siffofi ba sai da lazimin maganarsu, wato sakamakon abin da suke fad'a suka kuma tafi a kai zai kai ga siffanta Allah da miyagun siffofin tawaya irin wad'annan a hankalce.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation

Ƙara sabon ra'ayi