Tattaunawa 6
Tattaunawa Ta Shida
Ina ganin dakatar da wannan tattaunawa domin:
Kana ganin hadisi zai iya inganta sannan sai kuma ya sabawa kur’nai mai girma, wannan abu ne mai ban mamaki daga gareka, ba ka san mutlak da mukayyad da amm da khas da sauransu na Kur’ani ba, amma kai tsaye kana ta kawo ayoyi kana fitar da hukunci, kada ka manta na sha nuna maka wannan inda ka kawo ayoyi ba a mahallinsu ba, sannan kuma mafi mamaki kana ganin hadisi ya inganta amma sai a rushe shi da ayoyin Kur’ani, alhalin babu karo tsakaninsu, sai dai kai ne saboda sanin wasu ‘yan kalmomi na larabci sai ka yi tsammanin sun yi karo da juna. Wannan kuwa al’amari ne mai hatsari da ya sami duniyar musulmi, kuma abin takaici da ‘yan ustazai suka dauka suka dora wa kansu a kasashenmu, sannan kuma wai haka ne addini yake, na gaya maka Annabi (s.a.w) ya fassara wannan addini da ya kawo, bai bar mu da ra’ayoyinmu ba, kuma wanda ya fassara da ra’ayinsa to ya tanadi wajen zamansa a wuta kamar yadda ruwayoyi suka zo da shi.
Sannan kuma muna bahasi kan wasu mas’aloli daban amma kai kuma kai tsaye kana kawo wasu daban, misali ka kawo maganar sahabbai a wannan fayaloli uku na karshe da ka aiko, alhalin bahasin namu ba akan sahabbai yake ba. Bahasinmu ya riga ya tabbatar mana da cewa; Shi'a suna kan gaskiya bisa abin da suke bi ga wasiyyar Annabi (s.a.w) ta halifofinsa sha biyu, kuma wannan wani abu ne da akan shi wasu masu kiyayya da wannan biyayya suke gaba da su, da yi musu sharri iri-iri, saboda kawai sun gabatar da wanda Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) suka gabatar da jinkirtar da wanda suka jinkirtar, ba su yarda da bin son rai ba da ake neman kiransu a kai har abada. Kuma akan haka ne suka sha wahala a tarihin rayuwar Ahlul Bait (a.s) da mabiyansu.
Ka yi mana kagen zagi ko la’ana ko sukan sahabbai kamar dai yadda kuka saba yi wa mabiya Ahlul Bait (a.s), wannan kage ko sharri ko kazafi kamar yadda bahaushe yake kiransa, an dade ana yi wa mabiya Ahlul Baiti (a.s) shi, sai dai kai a matsayinka na dan’uwana a musulunci ni mai yafe maka ne. Da fatan zaka daina yi wa mabiya Ahlul Bait (a.s) irin wadannan kage-kage. Idan ka san cewa; ba zaka iya yarda da dalili ba, to babu amfanin wannan muhawarori.
Hada ni da wasu mutane daban kamar Parisawa da kiran su mayaudara, alhalin bahasinmu ba shi da alaka da Parisawa, ba ni da wata alaka da su sai wacce kake da ita ta cewa; ‘yan’uwanka ne musulmi, kuma su ma wasu shekaru da suka gabata ba da dadewa ba, su ma ahlussunna ne kamarka (sai dai su ba wahabiyawa ba ne) suka fahimci mazhabar Ahlul Bait (a.s), idan kana jin haushinsu kan haka sai ka fara sukar larabawa da suka kawo musu wannan koyarwar ta Annabi (s.a.w), sannan kuma sai ka fara da Imam Ali (a.s) da sahabban Annabi mabiyansa da suka kawo wa larabawa wannan koyarwa, ka ga ke nan sai ka fara sukan daga tushe, kai kana ma iya kaiwa ga wanda ya kawo wajabcin biyayya ga Ahlul Baiti (a.s) da Ubangijin da ya aiko shi, wal’iyazu bil-Lah.Wannan kuwa ba ina yi maka fatan ka kasance haka sai dai nuna maka cewa; jin haushin biyayya ga Ahlul Bait (a.s) zai koma wa abin da na kawo maka ne. Domin wanda ya kawo wannan addinin ba bahaushe ba ne, kuma su ma Imam Ali (a.s) da sahabban da suka bi shi kan wasiyyar Annabi (s.a.w) ba hausawa ba ne, kuma addinin nan na musulunci ba bahaushe ba ne, kuma kabilanci a wannan addini haramun ne. Kuma ina godewa Allah da na san addini na fahimci Ahlul Bait (a.s) da wajabcin riko da tafarkinsu tun kafin ganin wani bafarise a idanuwana, balle ka kawo mini irin wannan tsammani. Sai dai ka sani shiriya idan ta zo ko tahannun waye kodakuwa bafarise ne da kake zagi, to sai a karbe ta, domin koyarwar addini ta umarce mu da neman ilimi koda kuwa a kasar Sin ne.
Zubo ayoyin Kur’ani ba tare da yi wa Littafin Allah (S.W.T) adalcin fassara shi ba, domin yana da ayoyi mutlakat kamar yadda kake kawo su babu tadabburi kana mai fassara su kamar yadda ka gina akidarka da mazhabarka a kai, kana kuma tsayawa a matsayin Allah a fahimtarka, ta yadda kake kiran fahimtarka a matsayin abin da Allah yake nufi, ra’ayin wani da fahimtarsa kuma shi ne abin da ya sabawa Allah da manzonsa. Me zai hana ka ka tambayi masana marasa bin son zuciya, koda kuwa ya sabawa mazhabarsu, me ya sa ba zaka komawa mukayyadat ba, kamar “faman nakasa fa’innama yankus ala nafsihi” da gomomin irin wadannan mukayyadat da Allah ya saukar a littafinsa mai girma.
Sannan kuma wanda ya ce: hadisin wane ba daidai ba ne, shi kuma a wa? Yaushe ne wata ruwaya ta zo tana cewa; idan wane ya ce hadisi kaza ba ingantacce ba ne ta zauna, kai ba ka sani cewa kowa yana da mazhaba ba a wannan kwamacalar da ake ta tafkawa ana jingina ta ga addini. A ina ka samu wata ruwaya ta cewa abi malaminka wajen tace hadisai, wani abin mamaki kana magana kana warwara, ka ce: hadisai Allah ya kare su, kana kuma cewa; akwai masu tacewa; kuma ka kira tacewar da kariyar Allah, wato; ke nan Allah ne ya ce; wane zai zo ya tace sai ku bi shi, wal’iyazu bil-Lah idan dai haka addini yake a hannun ma’abotansa. Ka sani babu wani wanda Allah ya wajabta binsa sai manzon Allah (s.a.w) da halifofinsa goma sha biyu. Sai ka koma wa addininka ka bincika.
Kafin ka zargi malaman Shi'a da zagin sahabbai sai ka fara da Buhari da ya ce: wadanda zasu shiga cikin aljanna daga cikinsu kamar wani garken rakuma ne marasa makiyaye. Buhari: fatahul bari; j11, shafi 333. ya ce: Manzon rahama a wannar ranar lahira zai ce a yi nesa da su, kuma ya kawo dalilin hakan da cewa; tun da Manzo ya yi wafati suka yi ridda! Kuma aka gaya wa Annabi cewa; ba ka san abin da suka yi a bayanka ba. Sannan kana iya sukan Maliku da yake fada a muwatta: manzon rahama ya ki nema wa Abubakar gafara, duk da kuwa ya gaya masa muma munsulunta kamar yadda wadannan shahidai suka musulunta, kuma mun yi yaki kamarsu. Amma duk da hakan manzon rahama ya ce masa: Ban san abin da zaku yi bayana ba”.
Kai kana iya fara sukan ma sahabban kansu, domin uwar muminai Allah ya kara mata yarda ta ce wa usman “ku kashe Na’asal hakika ya kafirta” tarihin Dabari: j 3, shafi: 477. Kuma ibn Mas'ud yana cewa: “katalani ibn zami’atal kafir, bi amri usmanil kafir”, sharhi nahajul balaga, j 3, shafi: 44. Ko kuma mugira da yake cewa; game da Mu'awiya; “ji’itukm min indi akfarin nasi” kamar yadda ya zo a murujuzZahab na mas’udi, kuma ya fadi haka lokacin da Mu'awiya ya so cire ash’hadu anna muhammadar rasulul-Lah daga kiran salla yana mai sukan Annabi (s.a.w) kan ya sanya wannan a kiran salla, don sunansa ya wanzu!
Don haka kafin ka zagi malaman Shi'a kana sukansu da zagin sahabbai, sai ka fara da sahabban kansu ke nan da suka zagi sahabbai, ko ma neman kawar da sunan Annabi (s.a.w) da mugira ya fada game da Mu'awiya. Idan kuwa ba ka yi haka ba, to dole ka sani ba ka yi adalci a cikin mazhabinka ba, da kake ganin laifin wasu kana boye naka, idan kuwa ba ka sani ba ne, to wannan musiba ce gareka cewa; ba ka san mazhabinka ba. Idan kuwa ka sani amma kana ganin kuskure ne sahabbai suka yi sai dai ka boye, to ka daina sukan wasu akan wannan, kuma su ma sai ka ba su uzurin cewa; kuskure ne suka yi kamar yadda kake ganin sahabbai sun yi ka ba su uzuri. Domin babu adalci kuskuren da ka yarda da shi ka ba shi uzuri ya kasance daidai, amma na wasu ba daidai ba ne!
Duk wani dalili duk karfinsa a wajenka matukar yana karfafar biyayya ko falala ga Ahlul Bait (a.s) ba dalili ba ne a wajenka, ka ga ke nan a irin wannan babu amfanin wata muhawara a kai. Domin indai haka ne fagen addini da ilimi zai koma, to ba shi da bambanci da magana a bakin titi, da kowa ya ga dama sai ya fadi abin da ya so.
Wani lokaci ka nuna sukanka ga manyan malaman ahlussunna kamar Hakim, saboda sun yi laifin ruwaito abin da yake iya tabbatar da ko karfafa biyayya ga Ahlul Bait (a.s), ina ganin dukkan dalilai a wajenka komai karfinsu, sai ka yi musu hukunci da cewa; sun yi karo da Kur’ani, kai ka ce: kai ne Kur’ani kuma fahimtarka ita ce fadin Allah (S.W.T). kai mafi muni ma da kake nuna cewa Annabi (s.a.w) yana iya kuskure wal’iyazu bil-Lah! Kana ganin ko ya fadi magan to ai Allah ma ya fadi wata sabanin haka a Kur’ani, kana mai dogaro da ganinka da ra’ayinka na cewa; Annabi (s.a.w) bai san gaibi ba, wato; kai ka fi shi sanin abin da zai zo nan gaba ke nan, kuma kai ka fi shi fahimtar Kur’ani ke nan! Wal’iyazu bil-Lah! To malam abdussalam a irin wannan yanayi ka ga ke nan babu wani abu da zan iya cewa; sai dai kowa ya yi wa kansa hisabi kan addininsa tun kafin haduwa da Allah madaukaki, ya kuma shiryar da wanda ya kauce hanya kowaye shi daga cikinmu.
Karancin saninka da mustalzamatil akaliyya a muhawararmu yana sanyawa ba ka ma fahimtar wasu abubuwan da kake fada balle kuma ka fahimci ni abubuwan da nake fada, ka ga ke nan muna magana alhalin ajujuwan maganarmu sun saba, don haka babu yadda za a yi a samu dan furamare kuma a yi masa laccar da ake yi wa masu yin digiri, ka ga ke nan babu wani amfani gareshi. Ka sani tumu ba a hawansa da ci, sai an cashe an surfe an nike an yi kari… an yi masa miya sannan sai ya zama a shirye yake domin a ci. Ba haka kawai ake watsa masa ruwan kuka ba sai a hau cinsa.!
Yawan tanakudin maganarka kamar yadda na nuna a sama; misali; ka kore matan Annabi (s.a.w) daga kasancewa daga Ahlul Bait ne, a lokaci guda kuma ka sanya su, da cewa; ya ce; “anti minni bikhair” ban san yadda wannan maganar zaka iya amfani da ita ba, wajen sanya su cikin Ahlul Bait. Maganarka a lokaci guda tana nuna kamar fitar da su daga ciki suka ne kuma garesu, abin da nake gaya maka ke nan, cewa ba ka san lawazimul akaliyya ba, tayiwu kyamarka ga mabiya Ahlul Bait (a.s) da kuma mummunar fahimta da ka yi musu ta sanya ka yi musu tawilin duk wata magana tasu kamar suka ce ga wani.
Saba wa dukkan malaman musulmi gaba daya a cikin maganganunka, domin kana ganin hadisi mutawatiri komai adadin masu ruwaito shi matukar ya sabawa taka fassarar ga Kur’ani to bai inganta ba, wato; dukkan masana malamai na musulmi kai ka fi su sanin Kur’ani da sanin ingantaccen ra’ayi ke nan.
Umar ya fada a cikin sahihul bukhari cewa bai’ar da suka yi wa Abubakar fitina ce da Allah ya kare musulmi sharrinta: Buhari; j8, sh26. Amma kai kuma kana nuna kafi Umar sanin bai’ar da aka yi wa Abubakar kana mai cewa; Allah ya ba wa abubakar. Yayin da kake cewa da ni: “Na ji ka ce manzon Allah (s.a.w) ya bar aliyyu RA a mtasyin halifansa. Allah kuma ya bada shi ga Abubakar RA” A irin wannan yanayi da hatta wadanda suka yi bai’a kamar Umar dan Khaddab kai ka fi su sanin yadda abin ya wakana, to yaya kake son ni in gamsar da kai alhalin fadin Umar bai isa ya zama hujja ba a gun ka. Haka nan Umar bn Khaddab ya fadi cewa: “Akdhana Ali” da ta shahara gunsa da littattafai masu yawa sun ruwaito shi, amma kai kana musun kasancewar Imam Ali (a.s) mafi ilimin sahabbai. To yaya kake zaton zan cigaba da ba ka dalili, idan na Umar ba shi da amfani a wajenka ni kuma nawa yaya zai zama mai hujja.
Karancin sanin tarihi da kake da shi, da musun duk wani abu da al’ummar musulmi ta yi ittifaki a kan faruwarsa, idan kuwa haka ne sai ka yi musun sauran abubuwan da musulmi suka yi ittafaki a rayuwarsa, kamar ka yi musun dukkan samuwar musulmin farko ke nan. Kana mai musun la’antar Imam Ali (a.s) da Mu'awiya ya kafa, to sai ka yi musun yakarsa da sauran abubuwan da suka faru a tarihin musulmi. Ni da ni ne a makwafinka, ban gamsu da abin da nake a kai ba, da ban tsaya ina yaudarar kaina ba. Maimakon ka yi musun faruwar abun da al’umma ta kafu a kai idan ruhinka ya kasa dauka sai ka san wani abu da zaka yi wanda zaka samu nutsuwa da shi wajen Ubangijinka!
Kana ganin aikin Annabi (s.a.w) yana iya sabawa fikihu kamar misalin da ka bayar a can baya na fikihu da sha a azumi wanda shi ne na yi tir da shi. Ka dauka addini kamar ramuwar gayya ce ba dalili ba, sai kai kuma ka yi tir da alwala da sallar da ta inganta daga Annabi (s.a.w). Allah ya sauwake!
Idan mutumin da ba ma’asumi ba ne ya yi sabo, ba yadda zaka kafa hujja da shi akan hakan. Idan kuwa haka ne to sai mu halatta bautar gumaka domin su ma sun yi kafin musulunci ke nan. Ko kuma mu ya bi abinda aka yi wa Annabi (s.a.w) na tawaye a sulhun hudaibiyya, ko kuma mu ya bi kin biyayya gareshi a cikin bin rundunar Usama da hatta ta kai ga ya yi la’ana yana mai cewa: ‘la’anal-Lahu man takhallafa an jaisu Usama”. Kai ya nemi a bari ya rubuta wasiyyarsa ma amma aka ki, kuma aka hana shi abin rubutu, wanda ibn Abbas yana kuka idan ya tuna wannan. Don haka ka koma wa musulunci da kyau, ka kalle shi da idanuwan basira, ba kallon bangare na mazhabanci ba, wallahi ina rantse maka da Allah madaukaki da ya halicci dukkan samammu da nine nake da shakku kan wajabcin biyayya ga Ahlul Bait (a.s) kiftawar ido da na bar su gaba daya na yi riko da abin da na gamsu da shi a hujja, sai dai ban samu wani abu da ya fi shi inganci ba, don haka idan kana ganin ka nutsu da abin da kake a kai to ka tabbata a kai, amma idan kana kokwanto kamar yadda maganganunka suke nunawa kana mai warwarar abubuwan da kake cewa; ko kuma ka yi musun abin da ya inganta a gunku, to ka sake komawa ka yi tunani a kanka.
Idan ka gajiya kan wasu abubuwan to ka ce; ka gajiya, domin ka kasa ayyana jagoranka babu bukatar sai ka yi abin da duk wanda ya ji ya san ka kasa ne, sai ka koma ka yi tunani. Ka sani Annabi (s.a.w) ya bar mutane 12 da su ne jagororin al’umma har alkiyama ta tashi kowane zamani akwai dayansu kuma shi ne jagoran al’ummarsa. Idan ka ki yarda da su, to sai ka kawo naka ababan biyayya ba ka amsa da cewa; Annabi (s.a.w) ne. wannan ba ya nuna komai sai gajiyawarka.
Ka nuna ka fi kowa sanin Kur’ani a cikin al’ummar Annabi (s.a.w), hatta da mutanen da kake takama da su, abin da suka kawo maka ba shi da kima. Kana yi wa ayoyin Kur’ani hawan da ka dama, ina yi maka nasiha da ka bar hakan, ka bari sai ka nuna, ba tun kana iri ba ka kai matsayin tofo ba ka ce zaka fara yin ‘ya’ya. Kana cewa Allah ya ce: ruhama’u bainahum, kana kafa hujja da wannan da cewa ba zasu yi sabani ba, kana kuma ayyana wa Allah su waye ruhama’u bainahum, sannan kuma kana sabawa duniyar musulmi da ba ta tafi akan abin da ka ce ba. Duba ka gani Buhari ya kawo cewa: Fatima (a.s) ta yi fushi da Abubakar wata shida har ta mutu ba ta yi masa magana ba, kuma ba ta yarda ma ya halarci janazarta ba: Buhari, j5, sh:82. ko sh:139. sannan ga daruruwan sabani da yakoki da la’ance-la’ance da suka gudana da kashe-kashe duk tsakaninsu da dukkan al’umma ta yi ittifaki akan faruwarsu, amma sai ka kawo ayar Kur’ani kawai ka fitar da hukunci ka wautar da hankulan dukkan musulmi kana mai musun abin da suka samu tun daga wancan zamani da suka gani kuma suka ji har ya kawo ga wannan al’ummar.
Ka koma wa tunaninka, idan kuma a bisa sani ne kake wa Littafin Allah tawilin da ka ga dama, to wannan kuma yana komawa tsakaninka da Ubangijinka ne.
Ilimi yana da zurfin da ba ka tsammani, kuma Allah da manzonsa su ne suka fi kowa sani, sannan kuma Allah ya sanar da manzonsa abin da zai faru, kuma Manzo (s.a.w) ya dauki dukkan wani mataki akan hakan, don haka ya rage wa al’umma ta yi riko da abin da ya bari ko kuwa. Kuma duk wanda ya kauce bai cutar da Allah komai ba sai kansa. Allah ya wadatu gabarinmu, ba lallashinmu yake yi ba, kuma ba wani amfani zamu yi masa ba, sannan kuma ya wadatu gabarinmu, ba kuma gori muke yi masa ba cewa; mun yi imani, shi ne zai yi mana akan cewa ya shiryar da mu. Don haka ne ma ya hana annabinsa damun kansa da bakin ciki domin wani bai yi imani da abin da ya zo da shi ba!.
Don haka ne ma nake ganin bahasi da wannan yanayi ba shi da wata kima sai bata lokaci, kuma muna fatan Allah ya shiryar da mu, ya kara mana fahimtar juna.
Idan ka sake kawo maganar sahabbai ka fita daga maganarmu ta asali ba zaka sake ganin amsata ba, har abada. Haka nan idan na sake ganin sharri da kage.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Haidar Center For Islamic Propagation
Kammala gyarawa: July 1, 2009
Ƙara sabon ra'ayi