Tattaunawa 2
Tattaunawa Ta Biyu
Zan fara da maganar da kai mai musun wilayar jagoranci da tafarkin Ahlul Baiti (a.s) ka yi ta Gadir Khum a inda Annabi (SAW) yake cewa "man kuntu mawlahu, fa Aliyu maulahu". Kana mai cewa; Ai wannan bai nuna khalifanci ga Imam Ali a ba, kana mai kari da musun ma'anar karshen hadisin da yake cewa: "Allahumma wali man walahu wa adi man adahu" da cewa duk bai nuna halifanci ba!.
Game da al’amarin Gadir Khum, ka sani hannun Annabi a bude yake a kan ya yi amfani da wannan kalma ta "wali", don haka babu mai iya iyakance masa irin kalmar da zai yi amfani da ita, kuma shi ne shugaban masu hikima. Kuma a sarari tana nuna wajabcin biyayya gareshi hada da wajabcin soyayya kamar yadda ka kawo. Kuma wannan yana nuna halifancin Ali (a.s) kai tsaye ko tantama babu, saboda abubuwa kamar haka:
Na daya: Shin in tambaye ka Ya kai mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s): Kana ganin Annabi (s.a.w) zai tara mutane dubu hamsin zuwa dubu dari (bisa sabanin tarihi kan adadin) a wuri har ya sanya a dawo da wadanda suka yi gaba, a kuma tsaya har na baya su iso a wannan hanya mai zafi da suke cire rawunansu suna sanyawa kasan takalmansu, ga wahalar tafiya…! Domin kawai ya ce musu “Duk wanda nake abin sonsa ne to Ali (a.s) ma abin son sa ne. ko kuma duk wanda nake abokinsa ko mai taimakonsa Ali ma abokinsa ne ko mai taimakonsa ne”. (Sai ya zama ke nan wato; Duk wani sahabi ko aboki ko abin taimako, ko mai son Annabi (s.a.w) ya zama ke nan sahabi ga Ali (a.s) ko abokinsa ko abin taimakonsa, ko mai sonsa, alhalin tarihi ya nuna mana wadanda suka yi zamani da Manzo (s.a.w) suka nuna masa so, amma bayan wafatinsa suka ki Ali (a.s), sai ya zama ke nan wannan bayanin na Manzo (s.a.w) ya zama labari ba insha’i ba, alhalin Manzo (s.a.w) ya barranta daga wasa)
A hankalinka wani mai hankali zai yi hakan balle Annabi (s.a.w) da ya fi kowa kamala; Ashe yana bukatar haka bayan ya riga ya gaya wa musulmi gaba daya da cewa su abokai ne masoya juna mataimaka juna, kai har ma ya ce idan daya ya koka yana gabas ko yamma daya kuma yana gabas ko yamma bai taimaka masa to shi ba musulmi ba ne. ashe duk bayan wannan sai Annabi ya tara mutane domin kawai ya gaya musu hakan game da Ali (a.s)!
Na biyu: sannan kuma har Annabi ya yi addu’a da Allah ya taimaki wanda ya taimaka masa, ya tabar da wanda ya ki taimaka masa, kuma ya kebance shi da wannan banda sauran musulmi. A yanzu kana ganin wannan idan yana nufin so kawai zai kebanta da shi a cikin dukkan sahabbai! Don haka sai ya kasance sauran sahabbai bai wajabta son su ba ke nan, don haka ba laifi idan mutum ya ki su, kai yanzu ka yarda da hakan!.
Na uku: Bai’ar da aka yi masa, kuma hatta da halifofi sun yi masa bai’a a wannan wuri ba ta nuna so kawai, ta hada har da mika wuya ga jagorancinsa.
Na hudu: Murnar da Abubakar da Umar suka yi masa suka ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Talib, ka zama shugabana kuma shugaban kowane musulmi. Ban sani ba ko kana nufin Umar bn khattab ko Abubakar ba su fahimta ba ne, da su da sauran sahabbai da suka yi wa Imam Ali (a.s) murnar zama jagoransu. Ko kuma kana nufin ka ce suna taya shi murnar cewa dole ne su so shi, alhalin soyayya abu ne wanda yake na tarayya tsakanin musulmi, wanda da yadda kake nufi ne da ba su taya shi wata murna ba. Ko kuwa bai'ar da suka yi masa a wannan sahara mai zafi tana nufin soyayya da kauna kawai!, kuma idan haka ne wannan bai kebanta da shi ba, sai a yi wa kowane musulmi bai'a domin nuna soyayya da kauna gareshi. Sannan kuwa idan an yi masa bai'a domin nuna soyayya da kauna ne to yaushe ne aka nuna masa kauna da soyayya bayan wafatin Annabi (s.a.w) yayin da aka kewaye gidansa da wuta aka doki matarsa har ta yi bari da sauran munanan abubuwan da tarihi ya ruwaito.
Duba littattafai kamar: Shawahidittanzil na kanduzi bahanife: 1/ 175. Yana bi’il mawadda: juzi 1, shafi: 30 -31. Tarikhi bagdad: 8/ 290. Kuma Ahmad da ibn majah sun kawo haka daga Barra’. Kamar yadda Tirmizi da nisa’I daga Zaid. Ka duba littafin Gadir, zaka ga daruruwan masdarori da suka kawo wannan al’amarin. Haka nan dabari ya kawo wannan magana ta taya murna gareshi.
Na biyar: Gabatarwar da manzon Allah (s.a.w) ya yi a farkon hadisin yayin da yake cewa da su: “Shin ba ni ne shugaban kowane mumini da mumina ba?! A fili yake cewa ba komai ne karshe yake nufi sai abin da farko yake nufi.
Na shida: Maganar da ya rufe da ita na cewa Allah ka shaida bayan ya gama da kuma shaidawarsu. Ka ga ke nan sun shaida kan wannan al’amari mai girma ne da ya kebance shi a cikin sauran musulmi na wannan lokaci.
Na bakwai: Idan muka yi kokwanto kan tana nufin masoyi ko shugaba, to sai mu yi hukunci da duka ne da ya hada da wajabcin sonsa da kuma mika jagoranci gareshi; domin ka’idan nan ta ilimin Usul ta komawa ga ma’ana gamammiyya “amma” idan an rasa komawa ga kebantacciyar ma’ana “khas”. Don haka wannan ya tabbatar da ma’anar shugabancinsa da jagorancinsa kan duk wani mutum bayan Manzo (s.a.w), domin umarnin Allah bai kebanta da musulmi ba.
Na takwas: Akwai ayoyin Kur’ani da hadisai masu yawa da suke karfafar ma’anar jagora. Kamar ayar “kawai shugabanku … da muka kawo a bayanin da ya gabata wanda a karara take nufin jagora saboda karinar ayar da ta gabace ta, da wacce ta biyo baya da kuma tafsiran masu tafsirai.
Na tara: Daga hannunsa da Manzo (s.a.w) ya yi a wannan wuri da kuma nuna shi ga al’ummarsa.
Ya kai mai jayayya da akwai abubuwa masu yawa da lokaci ba zai ishe mu kawo su ba, amma Sheikh dan fodio yana cewa: Masu hikima sun ce: Nuni ya isar wa yin magana ga mai hankali. "الإشارة تغنى عن المقالة للعاقل"
Na goma: saukar azaba kan Nu’uman yayin da ya ki yarda da shugabancin Ali (a.s) nan take, da musun da ya yi wa Annabi (s.a.w) da cewa yaya zai ce su bi dan amminsa bayansa (s.a.w), da saukar azaba kansa wanda yake nuna dalilin saukar da ayoyin farko na surar Ma’arij. Ka duba tafsirin Durrul Mansur, da asbabun nuzul na Suyudi, da littattafai kamar Nurul absar na shiblanji basha’fi’e.
Na sha daya: Ya tabbata a ilimi mantik da palsapa cewa; Ma’ana gamammiya “amm” fuska ce ta “khas”, don haka wilaya a nan tana nufin ma’anar jagoranci, musamman da yake khas ana kawo shakku kansa, domin ka sani har abada ba yadda za a yi khas ya kasance fuskar amm.
Ka sani wannan kalma ta wilaya kalma ce da tana daga cikin kalmomin da aka yi wa tawili kamar yadda aka yi tawili ga watanta da wasu umarnin Annabi don son rai ko kuma saboda rashin yarda da wannan abin. Wasu sukan yi kokarin tawilin wasu abubuwa ne domin gyara barnar da aka yi wa addini wanda wannan cin amanar Allah da manzonsa ne.
Kuma wannan ba sabon abu ba ne, domin ba kawai tawili domin rashin yarda ba, hatta da zamanin Annabi (s.a.w) da yawa ya bayar da umarni amma ba a bi umarninsa ba.
Ya kai mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s), Amma maganar da ka yi ta cewa sauran mazhabobi zasu dawwama a wuta ba haka na ce ba, abin da na ce shi ne: Tunda ka kawo bahasin kasuwar al’umma gida saba’in da uku, don haka ne na tabbatar maka cewa Ahlul Bait (a.s) su ne suke kan tafarkin jama’a mai tsira; wato wannan guda daya. Kuma na kawo dalilai a kan hakan.
Amma batun Annabi (s.a.w) ya rayu akan tafarki da shi da mabiyansa ba bisa mazhaba ba; ai ba komai muka tabbatar maka ba da wannan maganganun bayan da muka kawo game da kasuwar jama’a 73 sai wannan, wato: cewa wannan jama’ar da take kan abin da Annabi (s.a.w) ya bari su ne mabiya Ahlul Bait (a.s). Ai wasiyyar da Annabi (s.a.w) ya yi ta bin Littafin Allah (S.W.T) da Ahlul Bait (a.s) yana nuni da hakan. Kuma bin su shi ne dawwama kan tafarkin Annabi yardajje gun Allah (S.W.T).
Ka sani Annabi (s.a.w) shi ne shugaban masu hikima da hankali, sannan kuma ya san babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani wahayi bayan nasa, don haka ya dauki matakai da zasu hana bacewar al’umma da karkacewarta. Idan kuwa ka ga al’umma ta ki to wannan ita tajiyo wa kanta. Don haka wahalhalun da kake gani da rarraba duk ya faru ne tun farko saboda barin wasiyyoyinsa. Kuma abin da ya faru ga yahudawa da Kirista shi ne ainihin abin da ya faru ga musulmi kwabo da kwabo, sai dai mu musulmi muna da ludufin Allah (S.W.T) na cewar muna iya bugun kirji mu ce: Duk wanda yake son ya ga sakon manzon Allah (s.a.w) ba tare da wani jurwaye ba to ga shi nan a tare da Ahlin gidansa (a.s).
Ya kai mai musu; Ka sani Maliku a Muwatta’ da Baihaki su ne kawai suka ce Littafi da Sunna aka bari, amma sauran ingantattun littattafai gaba daya sun ce an bar Littafin Allah ne da Ahlin gidan Annabi da aka fi sani da Alayensa. (Kuma wannan ba matsala ba ce, saboda ruwayoyin ba suna kore juna ba ne, suna fassara juna ne: wato; Littafin Allah da Sunnarsa da ta zo ta hannun Ahlul Bait (a.s)) Ba Litttafin Allah da ingantattun hadisai ba kamar yadda ka ce. Hada da cewa Littafin Allah da Sunnata yana da rauni sai ka koma ka duba. Ka sani sanin ingantattun littattafai zai yi maka wahala musamman da yake an kona hadisan manzon Allah (s.a.w) da sahabbai suka rubuta bayan wafatinsa, aka tattara su aka banka musu wuta, kuma aka kira su da cewa tatsuniyoyi ne irin tatsuniyoyin Ahlul Kitab! wayyo Allah!!
Kuma aka hana rubuta duk wani abu da aka ji daga Annabi (s.a.w) (ibn Kutaiba ya so ya kare wannan mummunan abu da ya faru a tarihi da tawiloli amma ya kasa!) sannan aka hana sahabbai yaduwa garuruwa domin kada hadisan su yadu. Idan an bar hadisai ne ingattattu, kai ya zaka san ingantacce bayan an fara hada su ne da wafatin manzon da wucewar (kusan) karni guda!, alhalin a lokacin siyasa ta shiga kowane loko. Duba ka gani a misali: Maliku bai yarda da Usman da Ali ba, kuma ya rubuta Muwatta. Buhari bai yarda da Imam Sadik ba, kuma ya rubuta Sahih Buhari. Banu Umayya suna la’antar Imam Ali har shekara 80 kuma an hana rawaito hadisansa. To kai irin wannan yanayi yaya kake tsammanin ka samu sahihi kamar yadda yake lokacin Manzo (s.a.w). hada da cewa Muslim ya tabbatar da cewa suna ruwaito ma’ana ne ba lafazin Annabi (s.a.w) ba! (Ka san kuwa cewa; da lafazin Annabi (s.a.w) ne da ta yiwu masu tunani su fahimci wani abu da shi mai ruwayar ba haka ya fahimta ba!!!) to ka sanin nan ne sirrin barin Ahlul Bait (a.s) zai bayyana gareka, kuma munin nisantar su yake futowa a fili.
Amma batun abin da Allah ya saukar, to yana cikin sakon Annabi ne gaba daya. Domin duk abin da ya fada Allah ya zartar da shi da cewa duk abin da ya zo da shi to mu karba Kamar yadda Kur’ani ya tabbatar da hakan.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Haidar Center For Islamic Propagation
Kammala gyarawa: 01 /July/ 2009
Ƙara sabon ra'ayi