Annabcin Annabi Musa

Shin Annabcin Annabi Musa (A.S) Na Duk Duniya Ne Ko Kuwa?
Duba zuwa ga wannan maud’in yana bukatar bincike kan lamurra guda biyu; na farko: Kan da’awarsa zuwa ga tauhidi da kadaita Allah madaukaki. Na biyu: Kan batun shari’arsa da hukunce-hukuncen da ya zo da su daga ubangijinsa. Domin wadannan abubuwa ne guda biyu mabambanta; ta yiwu ya zo da kira ga tauhidi ga Banu Isra’il mutanensa kawai ko kuma ya kasance ya zo da kiran ga dukkan al’ummar duniya ne. Sannan yana iya yiwuwa ya zo da kiran tauhidi ga al’ummar kabilarsa kawai wato; Banu Isra’il, amma kuma ya kasance ya zo da shari’a ga dukkan mutanen duniya ne. Domin kasancewar kiransa zuwa ga tauhidi zuwa ga duniya ne gaba daya, ba ya tilasta kasancewar shari’arsa ta kasance ta duniya ce gaba daya, banda akasin hakan, wato; da shari’arsa ta kasance zuwa ga mutanen duniya ne gaba daya, to dole kiransa zuwa ga tauhidi na kadaita Allah ya kasance zuwa ga dukkan mutanen duniya ne. Don haka a nan muna da bincike guda biyu ke nan da zamu yi:
Na farko: Kiran Annabi Musa (a.s) zuwa ga kadaita Allah madaukaki;
Na biyu: Kasancewar shari’arsa ta game daukacin dukkan al’ummun duniya ne;
Wasu ayoyi masu yawa suna nuni da kasancewarsa an aiko shi ne zuwa ga Banu Isra’il, kamar ayar nan da take cewa: “Yayin da Musa yake cewa da mutanensa ya ku mutane….” Saffi: 5. Da ayar nan da take cewa: “Kuma hakika Musa ya zo muku da ayoyi (hujjoji) sannan sai kuka riki dan maraki…”. Bakara: 92. Da ayoyi masu yawa da suke nuni da aika Musa (a.s) zuwa ga mutanensa, sai dai wannan ba ya nuni a fili da cewa sakonsa bai shafi sauran al’umma ba, domin ga Annabi Shu’aibu (a.s) an aika shi zuwa ga mutanen “Madyana”, a lokaci guda kuma ga shi an aika shi zuwa ga mutanen garin “Aika”. Duba; surar A’arafi: 85, da kuma Shu’ara: 176-177.
Muna iya cewa da’awar Musa (a.s) ta kadaita Allah ta shafi Banu Isra’il da kibdawa ne, kuma muna iya fahimtar wannan daga surar nan ta A’arafi: 105, da 134, da surar Daha: 43, 44, 47, da surar Shu’ara: 16-17, 27, da surar Zukhuruf: 46, da surar Muzammil: 15-16, da surar Zariyat: 38. Da sauran ayoyin da suke nuna cewa an aika Musa zuwa ga Fir’auna da Banu Isra’il ne, kuma kiransa yana nuni da kawar da bautar gumaka, da tsafi, da sihirin Fir’auna da mutanensa, har ma aka yi kure tsakanin Annabi Musa (a.s) da masu sihiri kuma ya yi galaba a kansu. Wannan duk yana nuna mana yadda da’awarsa ta shafi wanin Banu Isra’ila na Kibdawa da makamantansu, sai dai duk da haka ba mu da wani dalili mai gamsarwa a kan cewa da’awarsa ta shafi duk duniya ne, kai har ma da Kibdawan.
Tana iya yiwuwa da’awarsa ta zo ne domin ta tseratar da Banu Isra’il, sai dai domin da’awarsa ta samu karbuwa to dole ne ya yi tattaunawa da fir’auna domin ya tabbatar masa cewa; daga Allah madaukaki yake, ta yadda za a ce; da tseratar da su zai yiwu ba tare da shan wannan wahalar ba, to da ya yi. Sannan muna ganin cewa; duk sa’adda ya tabbatar wa fir’auna cewa shi manzo ne daga ubangijinsa sai ya kara masa da cewa ka aika Banu Isra’il tare da ni. Daha: 47. Don haka ne ma zamu ga yayin da ya kasa tseratar da su ta hanyar tattaunawa da fir’auna sai ya dauki wata hanyar ta mu’ujiza domin ya tseratar da su. Ayoyin da suka zo kamar haka suna nuni da wannan: A’arafi: 134, Nazi’at: 17-19, Daha: 77, Yunus: 90, Dukhan: 24. Da kuma nuni da cewa; muhimmancin tattaunawa da fir’auna domin a samu tsiran Banu Isra’il ne. Hada da cewa wasu ayoyin sun nuna cewa bayan Nuhu (a.s) an aika annabawa (a.s) masu yawa zuwa ga mutanensu har zuwa kan Musa (a.s) zuwa ga fir’auna, kamar yadda muke iya gani a surar Yunus: 74-75.
A bisa zahiri ana iya cewa da’awar Annabi Musa (a.s) ba ta shafi wasu ba, in banda Banu Isra’il, kuma daya daga cikin dalilan da suke tabbatar da hakan shi ne; yayin da ya ga wasu mutane suna bautar gumaka bayan an tseratar da Banu Isra’il, sai mutanensa suka ce: Ka sanya mana ubangiji kamar yadda suke da shi, Annabi Musa (a.s) bai amsa wa mutanensa ba, sannan kuma ya kwabe su kan cewa abin da wadannan mutanen suke yi bata ne. Sannan kuma babu wani dalili da muka samu a kan cewa ya gargadi wadannan mutanen kan abin da suke yi na bautar gumaka kamar yadda ya gargadi mutanen fir’auna, domin su ba ya bukatar tseratar da Banu Isra’il daga hannunsu. Sai dai duk da hakan abin da muke kawo wa na rashin samun dalili a kan kwabar wadancan mutanen ba bisa yakini ba ne, domin tayiwu akwai dalili amma bai zo mana ba.
Sannan babu wani tarihi da ya zo da labarin cewa; Annabi Musa (a.s) ya kira wasu mutanen bayan halakar da fir’auna da mutanensa, abin da ya zo mana game da shi yana bayanin wahalhalun da ya sha ne bayan sun kubuta daga fir’auna, ta yadda mutanensa (a.s) suka ki biyayya gareshi ta shiga garin da aka umarce su, har sai da Harun (a.s) ya rasu, kuma Musa (a.s) ya rasu bayansa da shekara daya, sannan sai Annabi Yusha’u ragowar na gari kuma wasiyyin Musa (a.s) ya karbi jagorancin al’umma ya yaki mutane masu tsaurin kai, Allah ya yi musu budi a hannunsa. A cikin wannan halin na dimuwa da suka shiga a cikinsa ne Annabi Musa da Harun (a.s) suka rasu, kuma wannan halin na dimaucewa da suka yi, ya dauki shekaru arba’in ne kamar yadda Allah madaukaki ya yi musu alkawarin wannan dimuwa a cikin wannan muddar. Duba, Surar Ma’ida: 21-22.
Hada kuma da cewa babu kayan sadarwa cikin sauki a wannan zamanin, babu hanyoyin isar da sako kamar yadda ya kamata, don haka sanya annabcinsa ya kasance zuwa dukkan duniya lamari ne wanda yake ba mai yiwuwa ba. Hada da cewa; al’ummun wannan lokacin suna cikin tsananin makantar kabilanci da bangaranci, ta yadda zuwan wani bare a cikinsu da sunan sakon Allah, yanayinsu ba zai karbe shi ba, don haka ne hikimar Allah madaukaki ta fi dacewa da aiko kowane Annabi (a.s) zuwa ga mutanensa ne. A bisa zahiri wannan yana iya tabbata idan muka duba kissar Annabi Musa da Hidir (a.s) wanda aka hada tsakaninsu kuma Musa (a.s) ya amfana da ilimomi da sirrori daga tafiyarsu tare; Kahafi: 65-66. Wannan yana iya nuna yiwuwar samuwar annabawa da yawa a wurare mabambanta ko wuri daya a cikin zamani daya, kamar dai Annabi Ibrahim (a.s) da Annabi Lud (a.s); Ankabut: 31-32.

Amma bahasi na biyu mai cewa; shin shari’ar Musa (a.s) ta game dukkan mutane ne ko kuwa kawai ta hau kan Banu Isra’il na?
A nan ma wasu sun yi da’awar cewa; ta game dukkan al’ummar duniya ne, wannan kuwa bisa dogaro da zahirin cewa; an rubuta masa komai a cikin allunan da ya karbo. A’arafi: 145. Da kuma kasancewar littafinsa haske ne ga masu takawa; Anbiya: 48. Da shedar aljanu a kan cewa sun ji wani littafi da aka saukar bayan Musa (a.s); Ahkaf: 30. Da cewar wannan yana nuna saukarsa ga aljanu da mutane gaba daya.
Sai dai idan muka duba hujjoji masu yawa da suke cikin Kur’ani mai daraja zamu ga wannan da’awar da aka yi ba zata iya tabbata ba, musamman cewa; wani wanda ba daga cikin Banu Isra’il ba zai iya amfana daga littafin Musa (a.s) koda kuwa sakonsa bai game har da shi ba, ga shi mu ma yanzu musulmi amma muna amfana daga Attaura ta fuskacin wa’azozinta koda kuwa ba mu amfana ba ta fuskacin hukuncin da yake kunshe cikinta.
Sannan kuma idan mun duba zahirin ayoyi masu yawa karara sun nuna cewa wannan sakon ya kebanta a shar’ance ga Banu Isra’il ne; muna duba ayoyi kamar haka: mai nuna cewa shi shiriya ne ga Banu Isra’il; Gafiri: 53. Da mai nuna cewa; an saukar wa Banu Isra’il hukuncin kisasi; Ma’ida: 32, 44, 45. Da mai nuna an ba su littafi da hukunci; Jasiyat: 16. Da wasu masu yawa da suke nuna su aka saukar wa da littafin karara a fili kamar haka: bakara: 121, 144, An’am: 20, 114, Ra’ad: 36, Ankabut: 47.
Akwai mai nuna cewa an saukar wa da Banu Isra’il littafi amma ba a saukar ga mushrikai ba a yankin larabawa kamar haka; An’am: 156-7. Don haka hatta da ayoyin da suka yi maganar saukarsu ga mutane ana iya fassara su da abin nufi da su, su ne Banu Isra’il, domin wasu ayoyin suna fassara abin nufi da wasu ayoyin.
Don haka wannan yana iya tabbatar mana da cewa; shari’ar Annabi Musa (a.s) kamar sakonsa na kadaita Allah ne, wanda bai kasance ya shafi dukkan halittun mutanen duniya ba!.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Saturday, September 12, 2009

Ƙara sabon ra'ayi