Labarun Manoma da Makiyaya A Ivory-Coast

Labarun Manoma da Makiyaya A Ivory-Coast
Mutum Guda Ne Ya Rasa Ransa A Rikicin Makiyaya Da Manoma A Ivory-Coast
Rahotannin da suke fitowa daga arewacin kasar Ivory coast sun bayyana cewa mutun guda ne ya rasa ransa a yayinda wasu da dama suka ji rauni a wani rikici wanda ya barke tsakanin makiya da manoma a yankin Bako. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya bayyana cewa rikicin ya barke ne bayan da manoma a yankin Bako suka lura cewa dabbobin makiya sun lalata masu amfanin gonakinsu a jiya Alhamis. Sarafin Anbula Mataimakin shugaban lardin Bako ya bayyana bacin ransa da aukuwan wannan rikicin kuma ya yi fatan rikicin ba zai yadu zuwa wasu yankuna ba. Mutum daya da ya rasa ransa dai makiyayi ne. Majiyar labarai a yankin na Bako ta bayyana cewa a cikin yan watannin da suka gabata ana samun karuwan rikici tsakanin makiya da manoma a yankin, wanda yakamata a ce hukumomi su shiga don ganin an takatar da rikicin haka.   

Ƙara sabon ra'ayi