Labarun Kasar Nigeriya
Labarun Kasar Nigeriya
Shugaba Kasar Nigeriya Ya Kai Ziyara Zuwa Jihohin Borno Da Yobe Da Suke Arewacin Kasar
Shugaban kasar Nigeriya ya kai ziyarar aiki zuwa jihohin Borno da Yobe da suke fama da matsalar tabarbarewan matakan tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar a yau Alhamis.
Ziyarar aikin da shugaban kasar Nigeriya Goodluck Jonathan ya kai zuwa jihohin biyu a yau Alhamis shi ne irinsa na farko tun bayan zabensa a matsayin shugaban Nigeriya a shekara ta 2011 saboda matsalolin tsaro da jihohin biyu suke fama da su sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis-Sunna lid-Da'awati waj-Jihad da aka fi sani da kungiyar Boko Haram ke kai wa, tare da mayar da jihohin a matsayin tungarsu.
Rahotonni sun bayyana cewar shugaban Nigeriyan ya fara gudanar da ziyarar aikin ne da jihar Borno, sannan ya garzaya zuwa jihar Yobe a cikin jirgin sama kirar helikwabta cikin tsauraran matakan tsaro.
Kamar yadda a yayin ziyarar ta shi shugaba Jonathan ya ki amincewa da bukatar yin ahuwa ga 'yan kungiyar Boko Haram, bayan ya bayyana 'yan kungiyar da cewa mutane ne da suke boye kansu, kuma ba su da manufofi bayyanannu.
Ƙara sabon ra'ayi