'Yan Ta'adda a Siriya Da Iraki

'Yan Ta'adda a Siriya Da Iraki
Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Siriya 42 Da Na Iraki 7 A Kusa Da Kan Iyakokin Kasashen Biyu.
Wasu 'yan bindiga sun kashe sojojin kasar Siriya 42 da na Iraki 7 a wani harin kofar rago da suka kai kan tawagar sojojin a kusa da kan iyakar kasashen biyu a jiya Litinin.
Lt Kanal Muhammad Khalaf Al-Dulaimi kwamandar rundunar tsaron kan iyakar kasar Iraki ya bayyana cewa: 'Yan bindigan sun kai farmakin bazata ne kan tawagar sojojin Iraki da na Siriya a yankin Manajim Ukashat kusa kan iyakar Iraki da Siriya da ke yammacin kasar Iraki, inda 'yan bindigan suna bude wuta da manyan makamai ta bangarori biyu a kan tawagar sojojin kasashen biyu lamarin da ya yi sanadiyyar lashe rayukan sojojin Siriya 42 da na Iraki 7 tare da jikkata wasu sojojin guda 12 kuma hudu daga cikinsu Irakawa ne.
Harin ya auku ne a lokacin da sojojin Iraki suke rakiya ga sojojin Siriya 65 da suka tsere cikin Iraki ta kan iyakar Ya'arubiyah da ke lardin Nainawa a arewa maso yammacin kasar Iraki a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da 'yan ta'addan Siriya suka fatattake su daga wajen da suke gadin kan iyakar Siriya.

Ƙara sabon ra'ayi