Sabanin Kasashen Sudan

Sabanin Kasashen Sudan
Sudan Zata Kai Karar Sudan Ta Arewa Kan Zargin Taimakwa Yan Tawaye
Gwamnatin kasar Sudan za ta bukaci  komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya gargadi kasar Sudan ta kadu kan tallafin da take bawa yan tawayen da ke yankin Darfur na kasar. Wata jaridar kasar Sudan wacce ake kira safari ce ta nakalto Daf'ullahi Hajj Ali jakadan kasar sudan a majalisar dinkin duniya yana fadar haka   Hajj Ali ya ce "Kasar Sudan zata mika wasika ta korafi ga komitin tsaro na MDD inda zata bayyana yadda gwamnatin JUBA take tallafawa kungiyar yan tawaye ta "Justice and  Equality Movement" a yankin Darfur, da kuma yadda ta samar da sansanin horar da dakarun wannan kungiyar yantawayen 800 a yankin. Jakadan ya kara da cewa wannan matsayin da gwamnatin  Juba ta dauka dai ya sabawa yerejejniyar da ta cimma da ita Sudan a birnin Adisababa na kasar Ethiopia a cikin watan satumban da ya gabata. A cikin yerjejeniyar Adisababab dai kasashen biyu sun fayyace yadda zasu warware sabanin da ke tsakaninsu kan lamura da dama , wadanda suka hada da rikicin fayyace wanda zai mallaki yankin Abiye mai arzikin man fetur da kuma wasu rigingimu na kan iyakokin kasashen biyu wanda ya kai tsawon kilomita 2000.

Ƙara sabon ra'ayi