Rikicin Kasar Mali
An Kashe Yan Tawayen Kasar Mali 100 A Safiyar Yau Jumma'a
Ministan tsaron kasar Faransa ya bayyana cewa sojojin hadin guiwa na kasashen yammacin Africa da na kasar Faransa sun sami nasarar kashe yan tawaye 100 a arewacin kasar Mali a safiyar yau jumma'a. Jean-Yves Le Drian ya bayyanawa jaridar Le Journal ta kasar Faransa haka ne a safiyar yau jumma'a kuma ya kara da cewa kasar faransa tana sane da cewa bangaren arewacin Mali inda yakin yake gudana a halin yanzu yana da matukar muhimmanci ga yan tawayen kasar, kuma ya tabbata cewa suna da shiri mai karfi a bangaren makamai da kuma horon soje. Minista Jean-Yves Le Drian ya fara ziyarar aiki na ba zata a kasar ta Mali ne a jiya Alhamis kuma a halin yanzu yana arewacin kasar inda sojojinsa da sauran sojojin kasashen yammacin Africa suke fafatawa da yan tawaye. A ranar 11 ga watan Jenerun da ta gabata ce sojojin kasar Faransa suka soma yaki da yan tawaye wadanda suke iko da arewacin kasar Mali na tsawon watanni kimani goma da sunan yaki da ta'addanci. A halin yanzu dai yakin kasar ta Mali ya fara yaduwa zuwa wasu kasashe masu makobtaka da kasar mali inda wasu masu goyon bayan ya tawayen suke garkuwa day an kasashen yamma don ganin an dakatarda yakar yan uwansu a arewacin kasar mali.
Ƙara sabon ra'ayi