Rai Da Jiki

Rai Da Jiki    

Jiki Da Rayuwa
A nan zamu so mu yi nuni da kusurwowin samuwar mutum guda biyu masu muhimmanci da ya hada da rayinsa da jikinsa da siffofin duka biyu da yadda ya kamata a tarbiyyantar da su. Wannan kuwa shi ne mafi muhimmanci a rayuwar dan Adam da idan ya gyaru to dukkan bangarorin sun samu gyaruwa, amma idan ya baci to dukkan bangarorin sun baci.  Jikin mutum yana da abubuwan da yake bukata na rayuwa domin ci gaba da samuwa, wadannan abubuwan idan babu su to karshensa ya zo ke nan. Yana bukatar abubuwa biyu na ciki da na waje, da kuma wani abu na uku da ya shafi rayuwarsa a matsayinsa na dan Adam.
Na ciki sun hada da ci, da sha, da magani domin waraka daga cututtuka, sai kuma abin da jiki yake furzarwa wadanda suke fita daga gareshi domin samun sauki kamar kashi, da bawali, da amai, da mani, ko wadi da mazi, da gumi ko zufa, da hawaye, da majina, da daudar kunne, da yawun baki.
Na waje kuwa sun hada da wanke dauda, da sanya tufafi kamar riga da wando, da takalmi da hula, da sanya abu mai kanshi kamar turare, da kayan ado kamar sarka da dan kunne, da awarwaro, da mai domin shafawa, da mai domin gyaran gashi, da jan farce. Kamar yadda yake bukatar wurin zama da inda zai samu rayuwa mai kyau da shakatawa, sannan ya samu wani abu da zai rage masa wahalar cirata daga wuri zuwa wani wurin kamar mota ko babur.
Amma a bangare na uku yana bukatar wasu abubuwa da suka shafi zaman tare na al’umma, da hukumar da yake karkashinta, idan mun duba irin wadannan abubuwan zamu ga suna cikin bayanai kamar haka:
Mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta kamar wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa, kuma yana bukatar kare duk wani abu da ya shafi jininsa, ko mutuncinsa, ko dukiyarsa. Amma sama da hakan akwai ‘yancin fadin ra’ayi da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci. Fadin ra’ayi yana kama da amai ko atisshawa ne da idan ba su fito ba to suna kumewa a cikin jiki, haka nan ra’ayi yakan zama ya kume a cikin tunani sai ya kasance wani bakin ciki da yake taruwa a cikin zuciya.
Akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wanda shi ne akidarsa, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali.
Idan mun duba sai mu ga kowane bangare sai da shari’a ta ba shi matsayi na musamman domin kamalar mutum. Don haka ne a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki a dunkule, mai son duba bayanai masu fadi sai ya koma wa littattafan shari’a.
Idan mun duba bukatun jiki na ciki sai mu ga shari’a ta muhimmantar da su ta yadda ta hana ci ko shan wani abu da yake cutarwa ko lahantawa, da yawa ayoyin da suka yi bayani kan haka a cikin littafi mai tsarki na Kur’ani, wasu ayoyin sun yi nuni da cewa: “… kuma ba a sanya muku kunci a cikin addini ba...” , wasu kuwa sun yi nuni da cewa: “... kuma yana haramta musu mai muni -cutarwa- ...” . A nan muna iya cewa hatta da abu mai sanya maye da aka haramta a shari’a yana komawa ga cutuwar mutum a hankalinsa ko jikinsa ne.
Sai shari’a ta haramta dukkan mai sanya maye da mai cutarwa domin ta kare tarbiyyar mutum ta jiki da ta rayinsa, da gujewa sanya masa kunci a cikin rayuwarsa, da kaucewa ransa ko jikinsa daga fadawa cikin wahala da halaka.
Dogaro da wannan maslahar ne shari’a ta sanya wajabcin yin magani ga wanda ba shi da lafiya domin ba ta halatta masa cutar da kansa ko wata gaba ta jikinsa ba, don haka ne ta hana sayar da wani bangare na jikinsa wanda zai kai shi ga cutar da ransa ko jikin, sai dai idan babu cutuwa a ciki kamar sayar da wani bangare na jininsa.
Sannan hikimar Allah ta sanya masa wasu dokokin da zai samu sauki a cikin jikinsa kamar furzar da majina ko miyau, ko amai, ko kuma fitar da dauda da dattin da ya taru a cikin jikinsa ta hanyar bawali da bayan gida, ko kuma fitar da maikon da yana iya daskarewa ta hanyar gumi da zufa. Da ba a sanya masa hanyoyin da zai samu sauki ba da ya halaka, da rayuwarsa ta kare, amma sai ya kasance an ba shi hanyoyin sararawa.
Sannan aka sanya masa hanyar sanyaya ransa da zuciyarsa ta hanyar yin kuka abin da yake ni’ima ce babba ga bayi da Allah ya yi musu. Kuma iyakacin bala’in da ya fada wa mutum da nauyinsa a kan zuciya ne ransa take bukatar fesar da shi ta hanyar yin kuka domin samun lumfasawa.
Ruwaya ta zo cewa: “Masu kuka mutum biyar ne...” . Kuka wani abu ne da ake son yin sa domin wasu abubuwa da suka hada da tsoron Allah ga wanda ya tuna zunubansa, ko yayin wata musiba kamar mutuwa. Wasu mutane sun so hana kuka yayin mutuwa, sai dai wannan ya taso daga rashin fahimtar maganar manzon Allah ne da wani sahabi ya yi, sai Ai’sha matar Annabi (s.a.w) ta gyara masa cewa ba haka ake nufi ba, sai dai abin da aka hana a kukan mutuwa shi ne fadin abin da ya saba wa shari’a.
Wata hanyar samun lafiya da Allah ya sanya wa bayinsa ita ce hanyar fitar wasu abubuwa da shari’a ta sanya wanka saboda fitarsu, wadannan abubuwan sun hada da mani, da jinin haila da na haihuwa, da na istihala idan yana da yawa sosai. Akwai kuma wasu ruwa masu fita daga mutum da ba a sanya komai a kansa ba don sun fita, wadannan su ne mazi da wadi, kuma shari’a a bisa mahangar Ahlul-baiti (a.s) ta yi musu hukunci da tsarki.
Wasu kuwa an sanya yin tsarki ne saboda fitarsu wadannan abubuwan sun hada da bawali da gayadi, wadannan idan sun fita sai mutum ya yi tsarkinsu. Akwai kuma wasu halaye su ma da ake son wanda ya yi su ya yi alwala, wadannan abubuwan sun hada da yin bacci ko suma.
Amma abubuwan da suke daga wajen jiki sun hada da tsarkin daudar jiki, shari’a ta sanya tsarkake jiki daga dauda domin kada ya yi wari ya cutar da kanda da mutane. Wata ruwaya tana cewa da mu: “An gina addini a kan tsafta ne” , wata kuwa tana cewa: “Tsafta tana daga imani ce” . Kazamin mutum ba ya samun kima da daraja a cikin mutane, mutane suna wulakanta wanda suka gani cikin kazanta komai kimarsa.
Akwai kuma kayan sawa da suka hada da riga da wando, da takalmi, da hula, da turare, da gashin mata, da sauran kayan ado kamar sarka da awarwaro da dan kunne, ko jan farce da sauransu. Shari’a dukkaninsu ba ta hana su ba, sai dai a tufafin mace ta wajabta mata rufe dukkan jikinta in banda fuska da tafuka.
Wadannan tufafin kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma dukkan shigar al’umma ba ta da wata matsala a shari’a matukar dai ba ta saba wa waccen doka da aka sanya wa mace ba. Al’adun Hausa mace tana iya sanya atamfa da dan kwali da zane, da mayafi, sai ta rufe duk jikinta da wannan, tana iya sanya wando ko ta hada zane da wando.
Muna iya ganin a wasu al’ummun namiji ne yake daura zane mace kuma wando, wannan yana nuna mana kowace al’umma tana da nata yanayin shiga, kuma babu wata shiga da musulunci ya hana sai dai kawai ga mace idan zai kai ga bayyanar da jikinta da ya hana.
Wasu jama’un namiji yakan iya sanya gajeren wando da ‘yar riga, mace kuwa ta sanya siket da riga. Musulunci bai hana su wannan shiga ba, sai dai mace idan zata yi siket ya ja har kasa ta yadda zai rufe dukkan kaurinta har kafarta babu wani haramci a kan hakan, kanta kuwa da jikinta ta sanya riga zuwa karshen hannunta, ta sanya kuma abin da zai rufe kanta.
Muhimmi a cikin tufafi shi ne kiyaye wancan ma’anuni da musulunci ya sanya, idan aka kiyaye wannan babu wani tufafin wata al’umma da ya fi na wata. Babu bambanci, babban tufafi da karami duka daya suke, babu bambanci tsakanin babbar riga da kot da wando a wurin shari’a wannan duk yana komawa ga tunanin al’adun mutane ne.
Muna iya ganin yadda hula take da muhimmanci a wata al’umma, a wasu al’ummu girman mutum yana kan hularsa ne, da zai je taro babu hula to da kimarsa ta fadi ke nan. Amma a wasu al’ummu hula ba ta da wata kima ta a zo a gani, wasu suna ganin cewa sanya hula da dare yana haifar da matsala a ganin mutum, wasu sun tabbatar da matsalar yawan rufe gashi kodayaushe.
Amma wasu al’ummu idan ba su sanya hula ba suna ganin kamar ba su kammala ba, kana iya ganin mutum yana rufe kansa da zafin rana, kansa yana ta yi masa kaikayi amma ba zai cire hular ba, mafi muni shi ne likita yana iya hana shi sanya hula amma don kada al’umma ta gan shi karamin mutum sai ya sanya, haka nan al’adu suke cutar da al’ummu daban-daban.
Musulunci yana son tufafi ne na takawa, don haka kowace irin shiga al’umma take da shi ba shi da muhimmanci a wurinsa, abu muhimmi a nazarinsa shi ne takawar mutum, mutumin da yake sanya gajeren wando da karamar riga yana mai jin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa shi ne abin so wurin Allah, amma mutumin da ya sanya rawani da alkyabba, ga babbar riga da mota mai tsada ba shi da wata kima wurin Allah sai idan shi ma yana da takawa.
Wannan ne ya sanya ma’aunin Allah da yake kallon bayinsa da shi ya saba da ma’aunin da mutane suke kallo da shi. Ma'aunin Allah ya doru bisa ganin dukkan halittarsa a daidai a cikin al'adunsu matukar ba su saba wa dokokinsa, amma tsukakken tunanin mutane yana girmama dan Adam ta cikin al'adu da abin duniya ne.
Idan muka waiwayi kayan adon mata haka nan babu wani ado da musulunci ya hana mace kowane iri ne, sai dai bai halatta ta bayyanar da adonta ga wasu mazaje ba sai dai ga mata ko mutane da suke muharramai kamar 'yan'uwanta, babu wani dan kunne ko sarka, ko man shafawa, ko karin gashi, ko rina gashi, ko jagira, ko jan farce, da sauran kayan ado da addini ya hana mace.
Sai dai namiji yana da dabaibayi da shari'a ta yi masa na cewa bai halatta ya sanya zenare ko azurfa ba, ko alhariri bisa sabani, don haka mace tana iya sanya zinare amma namiji bai halatta ya sanya shi ba. Zai iya yiwu wata al'ummar ya kasance namiji yana yin kitso ko ya sanya dan kunne da sarka ko awarwaro don adon namiji, shi ma a nan musulunci ya hana namiji sanya sarkar zinare, wannan haramcin na zinare ga namiji ba shi da bambanci a cikin al'ummu.
Game da wurin zaman rayuwa kamar gida, ko kuma wani abin hawa kamar mota, babu wani wanda Allah ya yi wa haramcinsa kamar namiji ko mace, a irin wannan abubuwan shari'a ba ta hana komai ba sai idan na haram ne. Idan gida ya kasance na kwace, ko filin kwace, to sai shari'a ta haramta zama da yin salla a cikinsa, kamar yadda ta haramta hawa motar sata ko ta kwace.
Wasu masu daskararren tunani game da musulunci sai suka hana mace tuka mota bisa jahilci, irin wannan jahilci ana yin sa a wasu kasase abin takaici da sunan musulunci. Kamar yadda zamu ga wasu kasashen ko kungiyoyi, ko ma wasu masu bayar da fatawa bisa tsukakken tunaninsu sun takaita kaya da irin na al'adarsu suna masu daukar cewa shi kadai ne na musulunci.
Amma a bangare na uku mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta da ya hau kan hukumar da yake rayuwa karkashinta ta samar masa da su, irin wadannan abubuwan sun hada da wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa.
Aminci wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam, idan babu shi to al’umma ba ta samun sukunin ci gaba. Don haka yana bukatar mai kare masa jininsa, da mutuncinsa, ko dukiyarsa. Kamar yadda yake matukar bukatar wanda zai kare masa ‘yancin fadin ra’ayinsa, da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci.
Sannan akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wato ‘yancin akida, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari’a ko na hankali. Kuma wannan akida wani abu ne da ya kafu a ransa, ya yi rassa a gabobinsa, don haka ne ba a tilasta mutum ya bar akidarsa, idan ana son gamsar da shi cewa akidarsa batacciya ce, to ya zama ta hanyar hankali ko hujjar shari'a.

Rai Da Rayuwa
Rai shi ne bangaren badini na dan Adam wanda ba a ganin sa amma ana riskarsa da mariskai na badini, don haka ne kowane mai rai yana riskar samuwarsa da cewa yana da samuwa. Amma jiki shi ne bangaren zahiri na dan Adam wanda yake ana riskarsa da mariskai na zahiri, kamar gani, ji, shaka, dandano, da sauransu. Da wannan ne zamu kai ga natijar cewa mutum yana da bangarori biyu ne na badini da zahiri, kuma asalinsa shi ne badininsa, amma a fili muna iya fahimtar asalinsa wato badininsa ta hanyar zahirinsa ne.
Ran mutum tana da rassa da bangarori kamar yadda jikinsa yake da gabobi, wadannan bangarori sun hada da zuciya, da hankali, da Saken tunani (Khayal), da Saken zuciya (Waham), sai kuma Rundunar Sha'awa, da Rundunar Fushi.
Zuciya: Ita ce bangaren samuwar mutum mai juya shi wacce idan ta samu haskaka da hasken shiriya babu wani abu da yake bubbugowa daga gareta sai umarnin alheri. Amma idan ta cika da duhun bata to sai ta lalace, sai ta kasance babu wani abu da zai zo daga wurinta sai umarni da sabo. Don haka ne ma ruwaya ta zo cewa a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuwa ta baci dukkan jiki ya baci, ita ce zuciya .
Kuma ita wannan zuciya ita ce gidan ubangiji a cikin duniya da bai yarda a sanya kowa a ciki ba sai shi, don haka ne wanda ya yarda ya sanya wanin Allah a cikinta to sai ya tabe. Sai dai sanya wanin Allah ba yana nufin babu wani a ciki ba, abin nufi shi ne idan akwai wani abu a cikinta to ya kasance don Allah, kamar dai son annabawa, da waliyyai, da bayin Allah saboda Allah.
Hankali: Shi ne bangaren rayukan bayi mai riskar sanin abubuwa kamar yadda suke ko sabanin hakan, ana son cika wannnan bangaren da hasken ilimi da sanin Allah madaukaki da siffofinsa, da annabawansa da wasiyyansu.
Idan wannan bangare ya samu hasken ilmi to babu wani abu da zai yi sai kokarin haskakawa sauran gabobi da abin da ya dace da wanda bai dace ba, sai ya rika nuna hanya ga mutum domin ya kai shi zuwa ga rabautarsa. Shi fitila ce ta sauran bangarori da idan suka fada duhu zai haskaka musu, kuma shi zai bayar da mafita ta gari da nuni zuwa ga hanyar kwarai.
Amma idan ya jahilci ubangijinsa, da siffofinsa, da sakonsa, ya kasa tantance gaskiya da karya, sai ya rude ya shiga dimuwa, rundunar jahilci ta mamaye shi, sai wauta ta durfafe shi, duhun rashin sani ya lullube shi, sai ya jagoranci bangarorin sha’awa da fushi zuwa ga hanyar lalaci da bata, domin shi makahon jagora ne wanda bai san mafita ba.
Hankali shi ne jagoran tafiyar a dukkan wadannan bangarori na rai, kuma shi ne yake tantance mai kyau da maras kyau sai ya yi umarni da kyakkyawa, ya hana yin mummuna, kuma ya tace ya auna guda biyun sai ya ware mai amfanarwa da mai cutarwa domin ya yi umarni da da rinjayar da amfanuwa daga na farko, da kuma nisantar na biyu.
Saken Tunani (Khayal): Shi ne bangaren rai wanda yake tuna abubuwan da suke da surarsu da hotonsu a cikin tunani, wasu sun faru wasu kuwa ba su faru ba, yana iya haifar da wata sura ta wani abu mai kyau ko mai tsananin muni. Wannan bangare yana daga cikin bangaren da ya fi komai hadari domin yana sanya waswasi, da firgici, da tsoro, misali idan mutum yana shi kadai, ko yana cikin duhu musamman yara wannan bangaren yana iya azabtar da su har su fita da gudu.
Daga cikin ayyukansa yakan iya daukar surar abubuwan da ya riska sai ya hada su, kamar ya sawwala wani dokin zinare mai fika-fikai, da kaho. Da wannan ne zamu fahimci hadarin wannan bangare na Saken tunani, da cututtukan rai da yake jefa mutane kamar waswasi.
Saken Zuciya (Waham): Shi kuwa wani bangare ne na rai wanda yake da hadarin gaske, wanda yake tafiyar da Bangaren Sha'awa da Bangaren Fushi da suke bangarori ne na rai, yana da son holewa da kece raini, da son hutu da annashuwa, da tunkude duk wani abu da bai yarda da shi ba ga kansa. Bangare ne da yawanci yakan yi umarni da abin da ya fi sauki ne, misali yakan sawwala wa mutun hutawa da yin bacci yayin da ya ji kiran salla, ko ya sawwala masa son kallo ko jin wani abu wanda yake na haram. Idan aka yi sakaci ya fada hannun rundunonin jahilci wadanda suka fi kusa da shi domin abin da suke so ya fi sauki gareshi, to sai mutum ya fada cikin halaka, ya dulmiya cikin bata.
Wannan bangaren na Saken zuciya shi ne mai bayar da umarni da hanin da yawanci karkatacce ne domin abin da rai ta so shi take yi, abin da ta ki shi take bari, kuma yawanci takan bi mai dadi ne ta bar mai wahala, don haka sai ta koma wa hankali domin tantancewa. Idan wannan bangaren ya yi wa hankali tawaye to a lokacin ne halaka take zuwa, sai mutum ya fada cikin duk wani ashararanci da lalacewa, da holewa da kece raini.
Bangaren Sha'awa: Shi ne bangaren da yake neman jawo wa rai wani amfani da duk wani abu da take sha'awa, wannan abin kuwa ya hada da na badini ne kamar abin da ya shafi ruhi kamar son ilimi, ko son kai, jin dadin rai. Ko kuma abin da ya shafi zahirin rayuwa wanda ya shafi bukatun jiki, kamar son jima'i da son mata, da son kyau, da son ci da shan mai dadi, da hutawa, da son bacci.
Wannan bangaren yana bin abin da Saken Zuci ya ba shi umarni ne, kuma yakan motsa matuka domin cimma burinsa idan ya tashi, har ma ya gusar da hankali, kamar mutum mai tsananin sha'awa da ya kebe da matar da yake sha'awa gabansa, idan wannan sha'awar ta kai kashi 100 ta yadda ta gusar da hankali to yana iya rungumar ta ko ya auka mata.
Bangaren Fushi: Wannan bangaren shi ma yana bin abin da Saken Zuci ya ba shi umarni ne, kuma yana kunshe da kyamar duk wani abu da bai yi wa rai dadi ba. Yana gudun aibi, yana kyamatar duk wata tawaya ta badini kamar jahilci, da tawayar rai, da jin rashin kamala, da isar rai. Kamar yadda yana motsawa matuka idan ya fahimci aka yi masa wulakanci na zahiri, kamar renin wayo, da keta mutunci, ko izgili da akidarsa, ko ubangijinsa, ko iyayensa, ko kansa, don haka ne ma yake tashi da karfinsa duk sa'adda rai ta fahimci ba a yi mata daidai ba.
Hadarinsa yana da girma matuka, domin idan ya tashi ya kai wani mikdari mai tsanani kamar kashi 100 yana iya yin kisa, ko sata, ko hari kan duk abin da yake so ya kai wa hari, don haka ne aka yi umarni da nisarta fushi matuka a addinin musulunci. Sai dai larura ne ga mutum ya motsar da shi yayin da ake bukatar hakan, kamar ya fusata don kare mutuncinsa da na iyayesa, ko ya motsa don kare wani abu mai daraja gunsa kamar idan aka ci mutuncin addininsa.

Hankali da Jahilci
Hankali da Jahilci wasu rundunoyi biyu masu harin juna da gaba mai tsanani tsakaninsu, domin duk sa'adda aka samu wani abu to babu mai yarda wani ya dauka shi kadai, kuma babu mai yarda a raba, kowanne yana son ya mallaka shi kadai ne. Don haka ne idan mutum ya samu kansa a karkashin harin wadannan abubuwa biyu babu makawa ne ya zabi daya domin ba sa haduwa wuri daya, kuma filin yaki da dauki-ba-daninsu shi ne jikin mutum, kowannen daga cikin yana son ba shi umarni ne sabanin dayan.
Da dayan zai ce dauki haram dayan zai hana, haka nan kallon haram, ko taba haram, ko jin haram, ko cin haram, ko karbar haram, duk suna karkashin umarnin rundunar jahilci ne da hanin rundunar hankali, kamar yadda jin halal, da aikata halal, da karbar halal, da ganin halal suke karkashin hanin rundunar jahilci da umarnin rundunar hankali.
Amma kafin mu ga yadda za a warware wannan rigimar ta yadda za a samu rundunar hankali su yi galaba kan rundunar jahilci cikin sauki ba tare da daga jijiyar wuya ba, zamu so kawo wasu daga cikin misalan wadannan rundunoni biyu domin mu san su tukun.
Zamu yi kokarin kawo misalai game da wannan mummunar runduna mai karya garkuwar tsaron rayukan mutane, mai jan su zuwa ga azabar Allah da fushinsa. Ita wannan rundunar tana da bangarori biyu, na farko ya shafi hukuncin shari'a, na biyu kuwa ya shafi kyawawan halaye.
Sannan zamu fara kawo Rundunar Jahilci sannan Rundunar Hankali ne domin sai an yi wanka an wanke dauda an shafa mai, sannan sai a yi ado da kaya masu kyau a sanya musu turare. Haka nan ne yake game da wadannan lamurran biyu, sai an cire munanan halaye an cizge su daga zuciya da ayyukan jiki, sannan ne idan aka yi kyawawa sai su zauna daram cikin ado. Amma mutumin da yake warin dauda, ya yi bududu da kura, fuskarsa ta dusashe, ga gumi ya jike jikinsa warin dauda yana tashi, sai kuma ya sanya tufafi masu kyau a kan wannan daudar, to haka ne misalin wanda yake yin kyawawan ayyuka amma kuma bai bar munana ba, don haka muka fara kawo su kafin mu kawo kyawawan ayyuka.
Allah madaukaki yana cewa: "Ka ce ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta muku" . Kamar yadda ya lizimci musulmi ya nemi sanin wajibai haka nan ya lizimta masa neman sanin haram da kuma nisantar su, kuma mu a nan zamu kawo galibin abubuwan da aka haramta a fikihu ne musamman wadanda ana iya cin karo da su kamar haka:
Taimakawa ga yin sabo, Taimakon azzalumi, Nutsuwa da fushin Allah, Musun mu'ujiza, Musun ranar sakamako da tayar da jikin mutane ko wani daga asasin addini ko na mazhaba, Musun larurin addini, Kawar da kai daga ambaton Allah, Izgili ga muminai, Yin Barna, Dagewa kan kananan sabo, Sanya zoben zinare ga namiji, Jawo mani kamar da hannunsa ko da na wani amma idan ta hannun matarsa ne to ba komai, Cutar da muminai, Kauce wa hukuncin shari'a, Amfani da kwanon zinare da azurfa koda don ado ne, Wulakanta musulmi, Yada sirrin wanda bai yarda a yada ba, Yada sirrin juna tsakanin miji da mata, Rashin biyayyar mace ga mijinta cikin abin da yake wajibi ne ta bi shi, Rashin biyyar 'ya'ya ga iyayensu, Wasa da kayan caca tare da sanya kudi, Bayyana sabo, Yada alfahasha, Ci a Ramadan ko ranar azumin wajibi ba tare da wani uzuri na shari'a ba, Boye kaya, Rashin nisantar bawali da najasosi, Rashin yarda da Allah a cikin kaddararsa, Umarni da mummuna, Cutar da makwabta, Karbar lada a kan wajibi ayyananne, Karkata zuwa ga azzalumai, Jefa kai cikin halaka, Jingina yaro ga wanda ba babansa ba, Fitar mace ba tare da izinin mijinta ba, Sumbuntar namiji ko mace ga bare, Sumbuntar mutum waninsa don sha'awa sai dai miji da matarsa kawai ko baiwarsa, Bidi'a cikin addini, Mutum ya auri 'yarsa ko duk matar da take haramun gareshi, Mummunan zato da gini kansa, Yin Kage, Bayan gida tare da ba wa alkibla baya ko gaba, Girman kai ga barin bautar Allah, Adon namiji da zinare, Duban taurari, Girman kai, Barin salla wajiba, Barin kowane irin wajibi, Jinkirta hajji daga shekarar da ya samu iko, Karyata wani abu na Kur'ani ko hukuncin shari'a, Yin Barna, Jinkirta salla har lokacinta ya fita, Kai hukunci gun azzalumi ba larura, Halartar wajen shaye-shaye, Mace ta yi ado ga namiji bare, Hore mala'ika ko rohani ko aljani da sauransu, Sanya bacci na maganadisu, Boye aibin kaya da algus, Jinkirta rama Ramadan har wani Ramadan din, Barin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, Barin ladabtar da yara da zai kai ga fasadi, Haramta halal, Halatta haram, Leken aibobin mutane, Tsoratar da mumini, Barin takiyya wajen da yake dole, Kamantuwa da kafirai, Ji wa wani ciwo ko dukansa ko zaginsa ko yanke masa wata gaba, Rashin amsa sallama, Hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba, Tsare hakkin Allah, Tsare hakkokin mutane, Tsare wani babu wani hakki, Sanya tufafin alhariri ga namiji babu wani uzuri na shari'a, Hassada da kuma aiki da ita, Tozarta hakkin mutane, Kiyaye littattafan bata da jaridu ko mujallu na bata da sayar da su da sayansu da koyar da su da koyonsu da yada su, Cin dukiyar maraya, Shan abu mai sanya maye, Cin mushe, Cin naman alade, Cin naman dabbar da aka haramta, Cin naman dabbar da ba a ambaci sunan Allah ba wajen yanka ta ko ta rasa wani sharadi na yanka, Cin tabo ko sauran abubuwan da aka haramta, Yin Ha'inci, Kayan kide-kide da muzik, kamar sayar da su da sayen su da kuma ajiye su da amfani da su, Yin Yaudara, Neman auren mace mai miji ko kuma mai idda, Cin maniyyin tumaki, Cin sauran abubuwan da aka haramta a jikin dabba, Sayar da karen kwararo ko alade da sayansu, Yakar shugaba adali, Cin najasa ko abu mai najasa da shan su, Karya ga Allah da manzonsa da Imamai (a.s), Buga ganga ko garaya da molo da ihu tare da maganganun banza da suka saba wa shari'a, Yin Sata, Yada barna, Kashe gaskiya.
Sannan akwai wasu abubuwan da aka haramta su a matsayin halaye munana da suka zo a ilimin fikihu da zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:
Daudanci da hada zina tsakanin mutum biyu, Yin Karya, Shiga kungiyoyin bata, Shiga addinan bata, Kiyayya da mumini, Son makiya addini, Zagi musamman ga Allah da Annabi da Imami da addini da Kur’ani da mazhaba da sauran abubuwa masu tsarki, Taba littafin Kur'ani babu tsarki, Mai baki biyu; ya yabi mutum idan ba ya nan kuma ya zage shi, Karbar rashawa da cin hanci domin boye gaskiya da bayyanar da karya, Karbar rashawa da bayar da ita cikin al'amuran hukunci sai da larura, Karbar riba da bayar da ita da rubuta sheda a kanta da zama tsakatsaki a kai, Zama kasar da mutum ba zai iya kare addininsa ba ko gusar da alamomin musulunci, Zuwa kasar da zata cutar da addinin mutum, Yin Fashi, Aske gemun wani ba da yardarsa ba, Yin Rawa musamman mace gaban mazaje ajnabiyyai, Shiga cikin cacar ful, Tafiya makarantun da zai kai ga fasadi, Tafiya bandaki da wurin wanka na iyo da makarantu da wuraren da ake cakudar da ba ta dace ba tsakanin maza da mata, Raddi ga Allah da manzonsa da imamai da marja'ai da suke kan tafarkinsu cikin hukuncin shari'a, Yarda da sabo, Jifan wani da zina, Yin Annamimanci, Sauraron annamimanci, Zuwa sinimar da ake nuna fasadi da barna, Kokarin rusa masallatai, Taimako ga azzalumai koda dan aike ne, Amfani da kayan kida da caca da kuros da sauransu, Waka da fadin karya a ciki, Toshe titi da hanyar musulmi, Aibata mumini da wulakanta shi da zarginsa, Karanta girman zunubi da zai kai ga jinkirta tuba, Fitar mata ba tsari da kuma cire lullubi, Shirka da Allah mai girma, Yada alfasha, Saba wa karya, Warware alkawri, Yin Shedar zur, Sharadi da sanya kudi na tsere sai dai abin da aka fada a littafin fikihu a babin tsere da harbi, Yin Rufa ido, Yin Munafunci, Ba wa azzalumi da 'yan bidi'a uzuri da kaunarsu, Tozarta wanda ake ciyarwa, Wasa da tattabaru da tsuntsaye da sauransu na daga abubuwan da sukan kai ga haram kamar sanya kudi, Zalunci da ta'addanci, Yin Zihari, Saba wa iyaye, Aikin tsafi da kuma abin da zai raba miji da mata ko kuma abin da yake sanya son wani ba tare da sonsa ba, Cin dukiyoyin mutane da barna, Jiji da kai a ibada, Yin Algus, Wakar bata da sauraronta, Canja wasiyya, Fushi da yakan kai ga haramun, Giba wato rada da sauraronta, Fasadi a bayan kasa, Yin Fitina, Fasikanci da fajirci, Sayar da littafi madaukaki, Sayar da makami ga kafirin yaki, Kiyafa wato danganta mutane da iyayensu ta hanyar kallon kafafunsu ko jikinsu da canke, Caca da kayan shadaranji idan an sanya kudi, Yanke salla wajiba, Rantsuwa bisa karya, Tone kabari, Yanke zumunci, Jingina 'ya'ya ga Allah, Yin Bokanci, Bayar da fatawa ba da ilimi ba, Fada da tafarkin Allah, Kisa ba da hakki ba, Auren mace da aka haramta da nasaba ko shayarwa ko surukuta, Aurar namiji da aka haramta aurarsa, Kin zuwa jihadi domin kare kai da addini yayin da aka kawo masa hari, Gudu daga filin daga, Yin Kafirci, Kasuwanci da abin da aka haramta sayarwa, Tauye mudu da awo, Boye sheda, Boye gaskiya, Wake da siffanta mace mai kamewa ko yaro a ciki, Zambon mumini a waka, Bude al'aura ga wanda ya haramta ya gani, Yin Luwadi, Wasannin banza na holewa, Taba jikin ajnabi ko ajnabiyya (mace ko namiji bare), Taba mace ko namiji da sha'awa ba ta hanyar halal ba, Amfani da kayan maye kamar sha, da saye, da sayarwa, da dasa su ko shuka su, da aikinsu, da cin kudinsu, da kai wa wani, da kuma hayar kanti ko abin hawa ko wani abu daban don sayarwa, da kuma sauran amfani kamar yin magani da su idan ba da larura ba, Saba wa bakance, Aikata abubuwan da aka haramta wa mai harama da aikin hajji, Zuwa wajen bokaye da 'yan bori da 'yan camfi da masu halarto da rauhanai da aljanu da sauransu, Mata su shafi juna da sha'awa, Maza su shafi juna da sha'awa, Hana zakka ko humusi ko sauran hakkoki na wajibi, Jinkirta hakkoki, Yin Hannu da ajnabiyya babu kyalle a tsakanin hannayensu, Jayayya da Allah da manzonsa da Imami bisa shisshigi, Saba wa Allah da manzonsa da imamai (a.s), Keta umarnin Annabi (s.a.w), Shisshigi da wuce gona da iri musamman ga Allah, Leken gidajen makwabta, Zama a kan teburin da ake shan giya, Hana aikata kyakkyawa, Shiga ayyukan azzalumai, Keta alfarmar Ka'aba da wurare masu tsarki, Yanke kauna daga rahamar Allah, Ruku'u da sujada ga wanin Allah, Rantsuwa da barranta daga Allah da manzonsa ko Imami ko addinin musulunci, Kai wa zuwa ga mulki ba ta hanyar shari'a ba, Azabtar da mutane don su fadi wani abu da ake bincike.
Muna iya ganin wasu abubuwan da muka fada kafirci ne yin su wasu kuma shirka ne, wasu kuma manyan zunubai ne, wasu kuma akwai kaffara a kansu wasu kuwa akwai haddi ga yinsu kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a littattafai.
Sannan akwai munanan halayen dadabi'u da suke munana kuma ya kamata ga dukkan musulmi ya kaurace musu kuma suna da yawa malaman ilimin kyawawan halaye sun ambace su a littattafansu kuma a nan zamu kawo wasu daga ciki, duk da wasu ma an haramta su a shari'ance, wadanda suka hada da:
Daukar fansa, Yin Alfahari, Cutarwa koda ba da haramun ba kamar ya gina gidansa ta yadda zai kare wa makwabcinsa rana ko iska, Wulakanci ko da bai kai haddin haramci ba, Wulakanta mutane, Tsoratar da mutane koda bai kai haddin haramci ba, Yada abin da ake son boyewa, Karya a cikin raha, Yin Izgili, Wuce iyaka kamar ya zauna tarabbu'i a waje mai tsukuku, Wulakanci cikin alheri, Kage cikin raha; kamar ya ce wane yana da ci, Magana da abin da babu ruwan mutum, Dogaro kan mutane, Aikin lagawu (wasannin banza), Boye abubuwan da aka boye da ba su shafi mutum ba, Raki gun musifa, Jur'ar yin munana, Bakin ciki a kan abin da ya kubuce na duniya, Rashin kula da al'amuran lahira, Son yabo da kurantawa, Son shugabanci da girma, Son dukiya, Son duniya, Hassada matukar ba ta kai haddin haramci ba, Yin Kwadayi, Dora nauyi kan wani, Hikidi da mugun kuduri da mugun kulli, Tsoron mutane, Kutsawa cikin munanan halaye, Neman zabar rayuwar da ya so ta duniya kamar kayyaduwa da nau'in tufafi da sauaransu, Saba alkawari, Riya koda a wanin ibada ne, Munana zato ga Allah, Munana zato ga mutane, Yin Mummunar dabi'a, Halartar Mummunan waje, Kokarin aikta mummuna da ba haramun ba ne, Rashin yarda da rabo, Zama da kaskantattun mutane, Kukan sha'anin rayuwa, Yin Rowa, Shige gona da iri a rayuwar duniya, Shagube koda ba na haramun ba, Kaskanta mutane, Kaskantar da kai, Kaskantacciyar himma, Dukan kai, Kwadayi, Yawan bacci, Dogon buri, Rashin kishi, Kishi a inda bai dace ba, Yin Gaggawa, Shisshigi daidai gwargwadon da bai kai haram ba, Kyautata zato ga kansa, Kabilanci da bangaranci, Rashin girmama babba, Rashin tausaya wa karami, Rashin dogara da Allah, Fushi babu wani dalili na shari'a, Yawan wadatar da ta kasance dalilin dagawa da girman kai, Yin Dimuwa, Yin Gafala, Fankama da abin mutane, Mummunar magana koda ba haramun ba ce, Tayar da fitina, Kekasar zuciya, Raba kan mutane da rashin jituwa, Yin Girman kai, Boye gaskiya koda kuwa boyeta bai kai wajibi ba koda kuwa ta hanyar shiru ne, Ganin alherin kansa da yawa, Karanta alherin wani, Yawaita sharrin wani, Karanta sharrin kansa, Butulcewa ni'ima, Rashin godiya, Yawan raha, Rashin daidaituwa tsakanin zahiri da badini koda kuwa a kan al'amuran duniya ne, Rashin kunya, Nisantar muminai, Zaman banza, Yawan dariya, Waswasi a al'amuran duniya, Yawan shagaltuwa da rayuwa, Kazanta da rashin lizimtar tsafta, Rashin adalci, Shisshigi a al'amuran duniya, Sakaci a ciki, Zama da masu sabo, Yunkune da bata fuska, Rashin kulawa da mustahabbai, Lizimtar makaruhai, Rashin kulawa da abin da ya ce da abin da aka ce game da shi, Rashin bayar da muhimmanci ga hukuncin shari'a.

Amma idan muka waiwayi rundunar Hankali zamu ga akwai misalai masu yawa game da wannan rundunar, wasunsu sukan kasance ta babin fikihu ne, wasu kuwa ta babin kyawawan halaye, a babin fikihu muna da misalai masu yawa. Ubangiji madaukaki yana cewa: "Allah yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma baiwa ga ma'abocin kusanci" . Sai ya lizimta mana sanin wajibai da aiki da su da zamu kawo wasu daga ciki a nan:
Ba wa mace sadakinta ko ladanta, Ba wa mai shayarwa ladanta, Ba wa mai girbi hakkinsa, Ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa, Bayar da zakka, Bayar da dukiyar maraya, Tsoro da takatsantsan ga abin da Allah ya hana, Rikon ado gun masallaci, Rikon abin da Manzo da Ahlul Baiti (a.s) suka zo da shi, Bayar da amana, Bayar da sheda, Bayar da hakkin Allah da na mutane, Neman izinin shiga gidan mutane, Umarni da kyakkyawa, Aikata kyakkyawa, Imani da Allah da ranar lahira, Kaskantar da kai ga Allah, Barranta daga makiyan Allah da waliyyansa, Kin makiya Allah, Neman tsani zuwa ga Allah, Neman yardar Allah, Kin ma'abota bidi'a, Kwana gun matarsa, Biyayya ga Annabi da alayensa, Bin limami a salla, Kawar da fasadi, Tuba, Tabbata kan gaskiya, Tabbata a kare kai, Nisantar mummnan zato, Nisantar bauta ga wanin Allah, Nisantar karya da shedar zur da muzik, Karkata zuwa ga sulhu, Amsa wa Allah da manzonsa, Son Allah da waliyyansa, Hijabin mace ga namiji bare, Yin aikin Hajji, Zantawa da ni'imar Allah, Haramta abin da Allah da manzonsa suka haramta, Kyautata zato ga Allah,
Renon 'ya'ya, Kiyaye farji, Kiyaye salla da ibadu da alkawura da amana, Hukunci da abin da Allah ya saukar, Neman yafewar wanda aka zalunta, Gaisuwa, Tsoron Allah da rusuna masa, Kaskan da kai ga muminai, Humusi, Tsoron Allah, Addu'a, Kira zuwa ga Allah, Kariya ga addini da rayuka, Kare mummuna, Ambaton Allah a kowane hali, Tarbiyyar yara, Amsa sallama, Shiryar da mutane zuwa ga gaskiya, Yarda da hukuncin Allah, Ziyarar Annabi da imamai, Mika wuya da tsarkake wa ga Allah, Rige zuwa ga gafarar Allah, Sauraron Kur'ani mai hikima, Tafiya a bayan kasa domin daukar darasi, Godiya ga Allah da iyaye, Yin Hakuri, Soyayyar iyaye da makusanta, Gaskiyar magana, Gyara tsakanin mutane, Azumin wata Ramadan, Rama abin da ya jawo lalacewarsa da batansa, Ciyar da mai jin yunwa, Neman arziki, Neman ilimi, Biyayya ga Allah da manzonsa da majibinta lamurra, Bayyana gaskiya, Bayyana ki ga masu sabo, Bautar Allah, Daukar darasi daga darussan rayuwar wasu, Yin Adalci, Zama da mata da kyakkyawa, Sanin ilimin wajibi na asasin addini da rassansa da kyawawan halaye da ladubba, Taimakekeniya, Runtse gani daga haram, Neman gafara, Yin Kishi, Matsawa wasu a mazauni, Ilimin addini, Tunawa da ni'imar Allah, Hukunci da gaskiya, Tsayar da addini da aiki da shi, Fadin kyakkyawa, Daidaita al'amura, Neman halal, Kasancewa tare da masu gaskiya, Nisantar wanda Allah ya la'anta, Hana kafirai shiga masallatai, Nadama kan zunubai, Nasiha ga mumini da taimaka masa, Ciyarwa a tafarkin Allah, Yin Aure, Hana mummuna, Hanuwa daga abin da Allah da manzonsa suka hana, Komawa zuwa ga Allah, Niyyar gaskiya da kyakkyawa, Yin Tahajjudi, Hijira saboda Allah, Rushe bata, Son ma'abota kusanci, Tsentseni a haram, Awo da ma'aunin adalci, Cika alkawari, Kare rai da iyali daga wutar lahira, Dogaro da Allah, Yakini da Allah da ranar lahira.

A bangaren kuwa kyawawan halaye da aka yi umarni da siffantuwa da su muna iya ganin akwai dabi'u mafifita abin yabo da musulunci ya yi maraba da su kuma ya yi umarni a siffantu da su, da ya kamata mutum musulmi ya siffantu da su kuma suna da yawa, amma zamu kawo abin da ya samu daga cikinsu kamar haka;
Nutsuwa da alkawarin Allah, Yin sannu-sannu a al'amura, Kaskantar da kai gun Allah, Adalci da fadin gaskiya game da mutane, Wadatuwa daga mutane, Fifita wasu a kan mutum kansa, Ciyarwa a tafarkin Allah, Taimakon mutane, Saba wa kai aikata alheri, Umarni da kyakkawa, Hani ga mummuna, Gyara tsakanin mutane, Ikhlasi a ayyuka, Nutsuwa da Allah, Biyayya ga iyaye, Kaskan da kai, Ziyartar juna, Jituwa da juna, Tuba daga aikata haram, Mika wuya ga umarnin Allah a komai, Dogaro ga Allah, Tabbata kan al'amura kyawawa, Yin Hakuri, Aikata Kyawawan halaye, Kiyaye hakkin makota, Son Allah da wanda Allah ya yi umarni a so, Soyayya saboda Allah, Kiyayya saboda Allah, Jin Tsoron Allah, Kaunar Allah, Jin Tsoron aikata zunubai, Rashin dogaro da ayyuka, Cudanya da mu'amala da mutane, Magana da kawukanmu, Cudanya da iyalinmu da 'ya'yanmu, Yarda da rabon Allah, Yin Zuhudu, Yin Baiwa da kyauta, Sitirta sirrin mutane, Gyara aibobin kai, Dadada magana, Godiya ga mai ni'ima wanda ya yi maka alheri, Gyara ga mutane ta hanyar hikima da wa'azi, Sakin fuska, Yawaita sadaka da taimakon raunanan mutane, Sadar da zumunci, Yada sallama, Bin halaye da raunana da marasa lafiya suke ciki, Yin Tsafta, Suturta aibobin mutane, Daidaituwar zahiri da badini a komai, Yin Gaskiya da nisantar karya koda a raha, Yin Hakuri, Karbar bakuncin muminai, Amsa kiran bakuntar muminai, Aika wa da kyauta wuraren da suke na alheri da kuma karbarsa, Rangwame ga mutane, Kame kai, Adalci a komai, Girmama ma'abota addini, Nisantar kaskantattun dabi'u, Yin Kishi, Son talakawa, Mujahada da rai, Bayar da rance, Biyan bukatun muminai, Kame cutar da su, Kiyaye sirri da rashin yada shi, Ambaton mutane da alheri, Gaggauta alheri, Yi wa kai hisabi, Nasihar muminai yana mai neman shawara ne ko kuwa, Yin Niyyar alheri, Tsarkake kai da kawar mata munanan halaye, Yin Takawa, Yin Tsentseni, Nisantar shubuha, Juriya kan barin sabo, Juriya kan bin Allah, Ambaton mutuwa, Wadatar zuci, Jin Kunya, Sakin fuska.

Samun Tsira
Samun Tsira; hanya ce da zamu iya bi domin samun galaba a kan rundunar jahilci cikin sauki kamar yadda zamu kawo, domin duk wani ciwo yana da magani, wannan ciwon na rai ne ko na jiki. Malaman tarbiyya masana ran dan Adam kuma wasiyyan Annabi (s.a.w) daga alayensa sun sanya hanyoyin da mutum zai bi domin fita daga cikin kangin wannan cutar domin samun rai mai lafiya mai kubuta daga dukkan aibi, ta yadda rai zata zauna da nutsuwa cikin jiki mai lafiya maras aibi. Masu hikima sukan ce: Hankali -wato Rai- mai lafiya cikin jiki mai lafiya.
Kamar yadda muka kawo cewa jiki shi ne fagen wannan yakin, sai dai mu sani cewa a nan jiki ba don shi ne yake samun sakamakon munana ko kyawawan halaye ba, ba kuma don cewa shi kadai ne yake fagen wannan gumurzun ba. Sai dai jiki a nan shi kansa rai tana amfani da shi ne domin samun burinta na gyaruwa ko lalacewa, don haka sai ya kasance kamar wuka ce a hannun dan fawa, ko fatanya a hannun manomi
Bayan wannan gabatarwa sai mu fara da cewa duk sa'adda wani ya tashi domin maganin runudunar jahilci, ya hau kasan ya fara da sanin cewa a yanzu shi wani fage ne na wannan gumurzu, kuma ya san cewa akwai wadannan mayaka da suke karkashin kwamandoji biyu masu girma wato Hankali da Jahilci, wannan bangaren muna kiran sa "waiwaye". Bayan haka sai kuma ya yarda cewa Saken Zucinsa zai rusuna wa umarnin Hankali ba na Jahilci ba, sannan sai ya daura damarar biyayya ga umarnin Hankali, da yakar duk rundunar jahilci, wannan muna kiran sa da "azama ko himma".
Sannan sai ya karfafi azamarsa da wani haske mai cewa a ransa gyara fa zai yiwu, idan ya sake a nan Saken tunani ya yi galaba a kansa ya sanya masa waswasi to ya fadi ke nan, kuma ba zai sake waiwayen hanyar gyara ba. Don haka ne a farko muka gabatar da cewa saken tunani yana da hadari matuka, domin hadarinsa bai gaza na saken zuci ba, saboda haka sai ya sanya wa kansa cewa gyara mai yiwuwa ne, kuma yana da sauki.
Yawancin mutanen kasarmu sun sha kaye ne a wurin Saken tunani, ta yadda da zarar ka yi wa mutane maganar gyara sai su ga ba zai yiwu ba, a nan ne al'ummarmu ta sha kaye ta kasa ci gaba, a nan ne duk lalaci ya fada mana, har wasu suka lalace da jin cewa tun da gyara ba zai yiwu ba ni ma bari in lalace, da wannan ne zamu sake lurasshe da mutane cewa hadarin wannan bangare fa ba karami ba ne.
Kafin mu sha magani sai mun yarda da wanda ya yi magana cewa amintacce ne, kuma maganinsa yana da garantin cewa idan mun sha babu wata matsala zamu samu waraka domin ya san dukkan cututtukanmu. Don haka ne kafin mu kai ga magani dole ne mu san cewa akwai Allah madaukaki wanda yake da matukar girma, kuma shi mai iko ne, sannan yana ganin mu duk abin da muke yi, kuma yana sane ba ya mantawa.
Sannan shi ne ya yi mana dukkan ni'imomin da muke amfana daga garesu kamar iska, ruwa, yanayi, tufafi, hankali, fasaha, da sauransu, da mutanen duniya sun taru a kan su yi mana lumfashi daya, ko digo daya na ruwa ba zasu iya ba, da sun taru a kan su ba mu kwayar samuwa da sun kasa, to wannan ubangijin da ya yi mana wadannan ni'imomi shi ne yake son mu tashi mu yi tunani domin mu kasance kamar yadda yake so, ba kamar yadda muke so ba.
Sannan a wani bangaren yana da karfin kamu mai tsanani idan mun saba, ba zamu iya gujewa azabarsa ba, don haka ne wasu ruwayoyi suka yi nuni da cewa; idan zamu iya fita daga karkashin mulkin ubangiji da ni'imominsa to sai mu saba masa, amma tun da kuwa ba zamu iya ba, babu mu babu saba masa. Don haka duk inda muka je yana nan, ba zamu iya guje masa ba, ba zamu iya tsere wa kamunsa ba, idan kuwa haka ne sai mu ji tsoronsa.
Amma maganar magani da muka ce zamu kawo bayaninsa zai kasance kamar haka ne; da farkon dai akwai abin da muke cewa Sharadi, sannan sai Lura, na karshe kuwa shi ne Hisabi. Don haka bayanin namu zai kewaya ne karkashin wadannan abubuwa guda uku:
Sharadi: Sharadi shi ne abu na farko kuma yana nufin cewa a kullum mutum zai duba kansa ya kuma duba girman ubangijinsa, sannan sai ya duba wadancan rundunonin Jahilci na shedan ya dauki alkawari tsakaninsa da Allah cewa ba zai aikata ko daya daga cikinsu ba saboda muninsu, don haka ba zai aikata koda mummuna daya ba. Sannan sai ya duba rundunonin hankali wadanda suke su ne kyawawan ayyukan da aka dora masa ya aikata su, sai ya dauki alkawari ga Allah cewa zai aikta su ba tare da takaitawa ba, gwargwadon yadda zai iya.
A nan fa mutum ya sani wani alkawari ne zai dauka tsakaninsa da Ubangijinsa wanda ba shi da wani abu da yake boye masa, wannan ubangijin duk da mun san ba shi da ‘yan sanda ko masu gadi da muke gani a fili, amma mu sani yana da wadanda suka fi wannan, domin akwai mala’iku da suna ganin komai namu, su ba sa gajiya, ba sa bacci, ba sa gafala, ko sha’afa, kuma ba sa mantuwa, kuma suna rubuta dukkan abin da muke yi.
Idan mai daukar alkawari ya san girman Ubangijinsa to zai san girman wannan alkawari da ya dauka, idan kuma ya san cewa wannan alkawarin da ya dauka ba fa amfanin Allah ba ne, ko wani daban, dukkaninsa amfaninsa ne, to a nan ma zai sake sanin kimar wannan alkawarin.
Lura: Lura ita ce abu na biyu kuma tana nufin cewa wannan alkawarin da muka dauka da wayewar safiya, zamu yi kokarin ganin mun kiyaye mun aikata shi tun safe har zuwa dare. Sai mu kiyaye mu ga ba mu yi wani abu na sabo ba tun safiya har dare, idan muka fara yin rada ko gibar wani muka tuna sai mu daina, idan hannunmu zai taba haram sai mu tuna sai mu fasa, idan idanuwansu zasu kalli haram, ko kunnenmu zai ji haram, ko kafarmu zata je wurin haram, duk idan muka tuna da wannan alkawarin da sharadin sai mu janye.
Haka nan idan muka ga zamu ki aikata mai kyau, kamar muka ki tausaya wa wani muka hana shi sadaka, ko muka ji nauyin tashi mu yi salla, ko muka ki taimaka wa wani, ko muka ki fadin gaskiya, sai mu tuna cewa mun yi alkawarin zamu yi kyakkyawa saboda Allah, don haka sai mu yi kyakkyawan.
Hisabi: Hisabi shi ne abu na uku, kuma yana nufin cewa da dare ya yi lokacin da zamu kwanta sai mu yi kawukanmu hisabi, mu duba mu ga cewa shin mun aikata wani mummuna a yau kuwa, idan muka ga mun yi wani mummuna sai mu nemi gafarar Allah madaukaki da cewa ya yafe mana. Kamar idan mun saba wa Allah da yin karya, sai mu nemi gafara kuma mu yi niyyar ba zamu sake ba, amma idan mun cuci wani ne da wani abu nasa to sai mu nemi gafara kuma mu mayar masa da kayansa kamar mun karbi kudinsa kuma muka hana shi, sai mu mayar masa da shi.
Sannan mu sake dubawa idan mun ki yin wani kyakkyawa, kamar wani ya zo neman taimako wurinmu kuma muna da yadda zamu taimaka masa amma ba mu yi, to sai mu yi alkawarin zamu taimaka masa, kuma ba zamu sake yin wannan halin na rashin yin alheri ba. Haka nan idan muka ga ba mu yi salla kan lokaci ba, ko ba mu fadi gaskiya ba wato mun yi shiru alhalin da bukatar mu fadi gaskiyar, to sai mu yi alkawarin zamu kiyaye daga yanzu ba zamu sake saba wa yin alheri da gaskiya ba.
Idan zai yiwu bayan neman gafara sai mu yi sallar dare raka’a takwas, mu yi shafa’i da wutiri raka’a uku, domin neman gafara da kuma neman dacewa nan gaba, wannan ya zo a ruwaya cewa; sallar dare kaffarar zunuban rana ce. Idan kuwa ba zamu iya yin salla ba, to sai mu nefi gafarar Allah da bakinmu ta hanyar neman gafararsa, da kuma a zuciyarmu ta hanyar jin cewa ba zamu sake ba, kuma wannan ya kasance da gaske saboda sabawa a nan tana nufin wasa da alkawarin da muka daukar wa Allah madaukaki.
A game da yi wa kai hisabi ne Imam Ali (a.s) ya ce: “Wanda ya yi wa ransa hisabi to ya rabauta, wanda kuwa ya gafala daga shi -ran nasa- to ya yi hasara, wanda ya ji tsoro ya aminta, wanda ya yi lura ya samu basira, wanda ya samu basira ya fadaka, wanda kuwa ya fadaka to ya samu ilimi” .
Bayan dukkan bayanan da suka gabata, zamu so mu kawo wasu misalai guda biyu daga Kur’ani mai daraja kan samarin da suka tsaya gaban rundunar sha'awa da rundunar fushi suka hana su damar halakar da su. Kamar yadda ya gabata cewa jiki yana da bukatu kamar yadda rai take da su, wani lokaci wadannan bukatu suna karo da juna, kamar mutumin da yake son shan giya, a lokaci guda kuma yana rage masa tunani da kaifin hankali, sau da yawa wasu sukan rinjayar da bukatun jiki, sai duniyar dan Adam ta dauka idan an biya wadancan bukatu na jiki komai ya gyaru ke nan, a sakamakon rinjayar da bukatun jiki a kan na rai ne ya sanya dan Adam shan kaye da faduwa kasa da lalacewa a rayuwarsa.
Don haka sai bala’o’i suka yawaita, zubar da mutunci ya yi kamari, sai fyade, da sata, da kisa, ga rashin kimanta juna, da rashin ganin mutuncin juna, sai ya zamanto mutum ya koma kurar mutum, idan mutum ya ga mutum tamkar tunkiya ta hangi kura saboda tsoron cutuwa, ko kuma rashin shiri da juna kamar kura da damisa.
Barin sha'awa ta yi rinjayi duniyar dan Adam ne ya haifar da son tara komai ta kowane hali, sai ya shiga sata domin samun abin ci da sha, da gida, da tufafi, da sauran kayan rayuwa, domin babu wata iyaka da ransa take da shi wurin cimma burinsa, wannan lamarin yakan kai shi ga kashe mutane domin cimma hadafinsa.
Kame kai daga abin da take so yana da matukar wahala, idan mutum bai yi wa ransa dabaibayi da bin hankali da kayyaduwa da umarninsa ba, to sai ya fada cikin bala'in tarkon sha'awa mai tsananin tarnaki. Tsayawa gaban sha’awa abu ne mai matukar wuya sai an yaki abin da rai take so, abu ne wanda rai take karkata domin cimma sa da dukkan hankoronta.
Annabi Yusuf (a.s) saurayi ne da ya ba mu babban misali a nan yayin da matar sarki ta kira shi, ga ta mai tsananin kyau da kamala, ga ado mai kayatarwa, sannan ga kamshi da kyalkyali da sheki, a daya bangaren shi saurayi ne mai sabuwar samartaka, amma sai ya kasance ya sadaukar da sha’awarsa, ya guje wa wannan fitina mai hadari, ya tuna cewa cin amanar ubangijinsa ce, don haka sai ya kama hanyar gudu daga gareta.
Maimakon wannan kyawun da sheki na duniya, sai ya zabi gidan sarka shekaru masu yawa, wannan lamarin ne ya sanya shi cikin manyan annabawan Allah da babu kamarsu, sannan ya samu daukakar da ba ta da iyaka a cikin bayin Allah na gari.
Annabi Yusuf (a.s) a matsayinsa na gwarzon kin biye wa sha’awar rai abin da take so ya toshe wa zuciyarsa dukkan wani uzuri duk da kuwa yana iya fuskantar kisa idan matar sarki ta yi masa sharri sakamakon kin yarda da ita da ya yi, sai dai Allah mai son sa ya tausasa zuciyarta ba ta so ganin kisansa ba, sai ta takaita abin da gidan sarka da azaba da wahala, domin dai ya karkato ya amsa mata bukatunta.
Idan muka waiwayi yakar rundunar fushi zamu ga babban gwarzonta shi ne Annabi Isma'il (a.s), wanda lokacin yana dan shekaru 13 babansa ya samu umarnin yanka shi, amma sai ya ture duk wani tsoro, ya sallama wa umarnin Allah madaukaki. Annabi Isma'il bai bayar da wani uzuri ba, sai ya yarda ya sallama domin a yanka shi kamar yadda ake yanka raguna, wannan lamarin ba mai sauki ba ne ga wanda bai ci galaba kan rundunar fushinsa ba.
Samar da alaka mai karfi tare da Allah da Annabi Isma'il (a.s) yake da shi ya sanya shi bai yi musu ba, ya mika wuya ne ga Allah madaukaki, bai kawo maganar hakki ko 'yancin dan Adam ba, domin shi tarbiyya ce ta Allah, don haka ya sallama wa Allah, yana mai gaya wa babansa (a.s) "Ka aikata abin da aka umarce ka" . Hakuri daga abin ki yana da wuya kamar juriyar rashin bin sha’awar rai dukkaninsu sai da juriya, don haka wannan matsayi na Annabi Isma'il (a.s) matsayi ne mai karfi da kima da ya cancanci jajirtawa.
Allah madaukaki yana cewa: Nagarta (biyayya da alheri da aikata kyakkyawa) ba shi ne kawai ku fuskantar da fuskokinku gabas da yamma ba, sai dai nagarta shi ne wanda ya yi imani da Allah, da ranar lahira, da mala’iku, da littafi, da annabawa, kuma ya bayar da -kyautar- dukiyarsa alhalin yana son ta; ga makusanta, da marayu, da miskinai, da dan tafarki -matafiya-, da masu tambaya -mabarata-, da kuma ‘yanta bayi, kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, da masu cika alkawari idan sun dauka, da masu hakuri a cikin tsanani, da cutuwa, da lokacin tsananin -yaki-, to wadannan su ne wadanda suka gaskata, kuma wadannan su ne masu tsoron Allah (Bakara: 177).
Don haka ne a shari’a da wasu ruwayoyi aka yi nuni da cewa ba kawai sallar mutum zaka kalla ba, sai dai ka kalli wadannan halayen nasa, to a nan ne zaka yi masa hukunci da kasancewarsa na Allah ne. Wato kasancewar mutum na gari shi ne ya hada siffofin kamala da halaye, da mu’amala da mutane, a kan tsarkin zuciya saboda Allah, ba kawai ibada ba. Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Kada ku duba yawan sallarsu, da azuminsu, da yawan hajjinsu da kyakkyawa da kuma rurinsu da dare -wato karanta Kur'ani da dare-, sai dai ku duba gaskiyar magana da rikon amana" .
Sannan wannan kyakkyawar mu'amalar ita ma ta kasance a kan tsoron Allah ba don yabon mutane ba, domin idan ta kasance babu fandeshan mai karfi to zata kasance hasara ne ga mai yin ta, maimakon ya samu ladan Allah sai ya samu azabarsa. Manzo mafi daraja dan Abdullah al'Mustafa yana cewa: "Allah ba ya duba surorinku (kaloli da fuskoki da shakaloli) da ayyukanku, sai dai yana duba zukatanku da niyyoyinku ne" .
Godiya Ta Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai
Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Tuesday, May 25, 2010

Ƙara sabon ra'ayi