Addinin Musulunci
Addinin Musulunci
Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci, kuma shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe, kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga sa’adar dan Adam, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al’amuran duniya da lahirarsu, kuma mai dacewa ga wanzuwa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma mai kunshe da dukkan abin da dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da zamantakewar jama’a da na siyasa. Da yake Shari’ar musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari’a da za tazo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.
Da an dabbaka Shari’ar musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da aminci ya game ‘yan Adam kuma da rabauta ta game su, kuma da sun kai kololuwar abin da dan Adam yake mafarkinsa na daga walwala, da izza, da yalwa, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.
Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko, kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummunan hali zuwa mafi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Ba riko da musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa musulmi wannan mummunan cibaya ba, sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu. Wannan kuwa shi ne abin da ya lahanta yunkurin cigabansu, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala’i da halaka har Allah (S.W.T) ya halakar da su saboda zunubansu. Allah madaukaki yana cewa:
“Wannan kuwa domin Allah bai kasance yana canja wata ni’ima da ya ni’imtar da ita ga wasu mutane ba face sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Surar Anfal 53.
Da fadinsa “Kuma wannan ita ce sunnar Allah a halittunsa cewa tabbas masu laifi ba sa cin rabauta”. Surar Yunus: 17.
Da fadinsa madaukaki: “Kuma Ubangijinka bai kasance mai halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
Da fadinsa: “Kuma haka nan kamun Ubangijinka yake idan ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai radadi ne mai tsanani”. Surar Hudu: 102.
Ta yaya ake sauraron Addinin musulunci ya tayar da al’umma daga dogon baccinta, alhali kuwa shi a wajanta kamar tawada ce a kan takarda da ba a aiki da mafi karanci daga koyarwarsa. Hakika imani, da amana, da gaskiya, da tsarkin niyya, da kyautata mu’amala, da sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, da makamantansu, tun farkon assasa Addinin musulunci musulmi sun yi bankwana da su tun da can har zuwa yau. Kuma duk sanda zamani ya ja gaba sai mu same su suna kara rarraba jama’a-jama’a da kungiya-kungiya, suna kifuwa da goggoriyo a kan duniya, suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra’ayoyi gagara fahimta, ko kuma a kan wasu al’amura da babu ruwansu a ciki, suka shagaltu ga barin asasin Addini da maslaharsu da maslahar al’ummarsu, da fadawa cikin jayayya game da halittar Kur’ani ko rashin kasancewarsa abin halitta, da batun narkon azaba da Raja’a, da kuma cewa aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halicce su ne nan gaba.
Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasu, babu abin da suke nunawa sai kaucewar musulmi daga madaidaicin tafarki zuwa ga halaka da karewa. Fandarewa ta karu tare da shudewar zamani, har Jahilci da bata suka mamaye su, suka shagaltu da abu maras kima, da camfe-camfe, da surkulle, da wahamce-wahamce, da kuma yake-yake, da jayayya, da alfahari, sai suka fada a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau yammacin Turai wayayye, fadakakke, babban sanannen makiyin mlusulunci, ya samu damar mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi, su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwa yadda har ya iya jefa su cikin mummunan halin da Allah ne kadai ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah madaukaki yana cewa: “Kuma Ubangijinka bai kasance yana halakar da alkaryu ba bisa zalunci alhali mutanenta suna masu gyara”. Surar Hudu: 117.
A yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita sai koma wa kawukansu su yi wa kansu hisabi a kan sakacin da suka yi, su yi yunkurin gyara kawukansu da zuriyoyi masu zuwa, ta hanyar ba su koyarwar Addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja’irci tsakaninsu. Da haka ne kawai zasu tsira daga wannan halaka mai girma, kuma babu makawa bayan nan su cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci kamar yadda Allah (S.W.T) ya yi musu alkawari. Kuma kamar yadda ake saurare daga addininsu da yake shi ne cikon addinai da ba a kaunar wani gyara na duniya ko lahira sai da shi[1].
Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa musulunci abin da aka lillika masa na daga bidi’o’i da bata kuma ya tserar da ‘yan Adam, ya kubutar da su daga abin da suka kai matuka gareshi na daga fasadi gama-gari, da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da kyawawan dabi’u da ruhin ‘yan’adamtaka, Allah ya gaggauta bayyanarsa ya saukake mafitarsa.
Hanyar Tabbatar Da Gaskiyar Addinin Musulunci
Idan muka yi jayayya da wani a kan ingancin Addinin musulunci zamu iya kayar da shi ta hanyar tabbatar masa da mu’ujizarsa dauwamammiya wato Kur’ani mai girma kamar yadda ya gabata game da kasancewarsa gagara badau. Haka nan Kur’ani shi ne hanyar gamsar da kawukanmu yayin da kokwanto ya fara zo mana, saboda irin wadannan tambayoyi da kokwanto ba makawa su taso ga mutum mai ‘yanci a tunani yayin karfafa akidarsa ko tabbatar da ita.
Amma shari’o’in da suka gabata kamar Yahudanci da Kiristanci, ba mu da wata hujja ko hanyar da zamu gamsar da kanmu, ko kuma mu gamsar da mai tambaya game da ingancinsu, domin su wadannan addinan ba su da sauran wata mu’ujiza da ta rage garesu, abin da mabiyan wadannan addinan suke nakaltowa na daga abubuwan mamaki da mu’ujizozi da suke danganta su ga annabawan da suka gabata, su ababan tuhuma ne a kan haka. Kuma babu wani abu da yake cikin littattafan addinan da suka gabata da yake hannunmu a wannan zamani wadanda ake danganta su ga annabawan, kamar Attaura da Injila, da ya dace ya zama mu’ujiza madawwamiya da zai iya zama hujja yankakkiya, kuma dalili mai gamsarwa idan ba musulunci ne ya gasgata da ita ba.
Sai dai mu musulmi ya inganta ne a garemu mu gaskata annabacin ma’abota shari’un da suka gabata, domin bayan gaskatawarmu da Addinin Musulunci, to ya wajaba a kanmu mu gaskata dukkan abin da ya zo da shi. Kuma a cikin abin da ya zo da shi akwai gaskata annabcin wasu daga annabawan da suka gabata kamar yadda ya gabata a baya.
Don haka musulmi ya wadatu ga barin bincike game da ingancin shari’un da suka gabata, domin gaskatawa da shi gasgatawa ne garesu, kuma imani da shi imani ne da manzannin da suka rigaya da annabawa magabata, don haka bai wajaba ba a kan musulmi ya yi wani bincike game da gaskiyar mu’ujizar annabawa ma’abota wadancan shari’o’i, domin abin kaddarawa shi ne ya riga ya yi imani da ita ta hanyar imani da musulunci kuma wannan ya isar.
Na’am, idan da mutum zai yi bincike game da Addinin musulunci ingancinsa bai tabbata gareshi ba, to dole ne a kansa kamar yadda hankali ya wajabta neman sani da ilimi ya yi bincike game da Addinin Kiristanci domin shi ne Addinin karshe kafin Musulunci, idan ya bincika Addinin Kiristanci bai gamsu ba, to sai kuma ya dukufa a kan Addinin da ya gabace shi wato Yahudanci. Haka nan dai zai yi ta binciken addinan da suka gabata har sai ya kai ga yakini da ingancin addinan da suka gabata, ko kuma rashin ingancinsu sai ya yi watsi da su baki daya.
Sabanin wanda ya tashi a Addinin Yahudanci ko kuma Kiristanci, shi Bayahude imaninsa da Addininsa ba zai wadatar da shi ga barin binciken Addinin Kiristanci da Addinin Musulunci ba, dole ne a kansa ya yi bincike a bisa wajabcin hankali ga neman sani. Haka nan kirista ba zai isu da imani da Almasihu (A.S) ba, wajibi ne ya yi kokari wajen sanin Musulunci da ingancinsa, ba zai samu uzuri ba da gamsuwa da addininsa ba, ba tare da bincike ba. Domin Yahudanci da Kiristanci ba su kore shari’ar da zata zo bayansu mai shafe su ba. Annabi Musa (A.S) bai ce babu Annabi bayansa ba, haka ma Annabi Isa (A.S) ya yi bushara da zuwan Annabin da zai zo bayansa[2].
Ta yaya zai halatta ga Kiristoci da Yahudawa su gamsu da akidojinsu, su dogara da Addininsu kafin su yi bincike game da ingancin shari’ar da ta biyo bayansu, kamar Kiristanci dangane da Yahudanci, ko musulunci dangane da Kiristanci da Yahudanci. Wajibi ne a bisa hukuncin hankali su yi bincike game da shari’ar da ta zo daga bayansu, idan ingancinta ya tabbata gare su to sai su canja zuwa gare ta su bar Addininsu, idan kuwa ba haka ba to ya dace a bisa hukuncin hankli su wanzu a kan Addininsu na da, su kuma karkata zuwa gareshi
Amma musulmi kamar yadda muka riga muka fada idan har ya yi imani da Musulunci, to ba ya bukatar ya yi bincike game da addinan da suka gabaci Addininsa da kuma wadanda ake da’awa bayansa. Wadanda suka gabata dai domin shi ya yi imani da su, to don me kuma zai bukaci dalili ko hujja game da su, sai dai kawai ya yi hukunci da cewa ita shafaffiya ce da Shari’ar Musulunci, don haka bai wajaba ya yi aiki da hukunce-hukuncensu ko littattafansu ba. Amma wadanda ake da’awarsu daga baya kuwa dalili shi ne, saboda Annabin Musulunci Muhammad (S.A.W) ya ce: “Babu wani Annabi bayana”. Kuma shi Mai gaskiya ne kuma Amintacce. “Kuma shi ba ya magana a kan son rai, ba wani abu ba ne face wahayi da aka yi masa”. Surar Najmi: 3-4. Don haka saboda menene zai bukaci dalili a kan ingancin da’awar Annabcin da aka yi da’awarsa daga baya idan har mai da’awar ya yi da’awa.
Na’am yana wajaba a kan musulmi -ya yi bincike bayan tsawon lokaci tsakaninsa da ma’abocin sako (S.A.W), da sabanin mazhabobi da ra’ayoyi, da kuma samuwar kungiyoyi- ya yi bincike, ya bi hanya mafi dacewa wajen isar da shi ga sanin ainihin hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a, domin shi musulmi an kallafa masa aiki da dukkan hukunce-hukuncen da aka saukar na shari’a kamar yadda suka zo. Sai dai kuma ta yaya zai san cewa ita ce shari’ar da aka saukar kamar yadda take, alhali musulmi sun sassaba jama’a-jama’a, sun rarraba, babu salla guda daya, babu ayyukan ibada da aka yi ittifaki a kansu, ayyuka ba su zama daidai iri daya ba a cikin dukkan mu’amala. Don haka yaya zai yi? Ta wace irin hanya zai yi salla? Da wane ra’ayi zai yi aikin ibada da mu’amalarsa, kamar aure, da saki, da gado, da saye da sayarwa, da tsayar da haddi, da diyya da sauransu?
Kuma bai halatta gare shi ba ya bi ra’ayin iyaye ko ya koma ga abin da zuriyarsa da mutanensa suke a kai ba, sai dai ma babu makawa ya zama yana da yakini shi da kansa tsakaninsa da Allah (S.W.T), domin a nan babu wani boye-boye da nuku-nuku, ko sassauci, ko bangaranci. Na’am babu makawa ya samu yakinin cewa ya bi hanyar da ya yi imani da cewa zai sauke nauyin da yake kansa tsakaninsa da Allah, ya kuma tabbatar da cewa ba za a yi masa azaba a kai ba, Allah kuma ba zai zarge shi a kan bin ta da aiki da ita ba, bai halatta ba zargin mai zargi ya dame shi a kan tafarkin Allah “Shin mutum yana tsammanin za a bar shi haka nan ne sakaka kawai”. Surar Alkiyama: 36.
“Lalle shi mutum a game da kansa mai gani ne”. Surar Alkiyama: 14. “Lalle wannan fadakarwa ce, don haka ga wanda ya so ya kama hanya zuwa ga Ubangijinsa”. Surar Muzzammil 19.
Farkon abin da mutum zai tambaya shi ne; Shin ya kama tafarkin Zuriyar Gidan Manzon Allah ne ko kuwa tafarkin wasu daban? Idan ya kama tafarkin Ahlul Baiti (S.A.W) shin tafarkin Imamiyya Isna Ashariyya masu bin Imamai sha biyu shi ne ingantaccen tafarki ko kuma tafarkin wadansu daga bangarori daban-daban? Idan kuma tafarkin Ahlussunna ya kama to da wa zai yi koyi, daga cikin mazhabobi hudun ne ko kuma daga wasu mazhabobin daban da suka rushe? Haka nan tambayar zata yi ta zo wa wanda yake da ‘yanci a tunani da zabi har sai ya kai ga wata gaskiya a bar dogaro.
Saboda haka bayan wannan ya wajaba a kanmu mu yi bayani game da Imama, mu yi bincike a kan abin da yake biye da ita a akidar Imamiyya Isna Ashariyya.
Mai Shara’anta Musulunci
Mun yi imani da cewa ma’abocin sakon Addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi, kuma shi ne cikamakon Annabawa, shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar yadda shi ne shugaban ‘yan Adam baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci, babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali, babu wani kamarsa a kyawawan dabi’u: “Lalle kai kana kan manyan dabi’u masu girma”. Surar Kalam: 4. Wannan kuwa tun farkon samuwar dan Adam har zuwa ranar tashin kiyama[3].
[1]- Fadinsa madakaki: “Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa duniya bayina salihai ne zasu gaje ta, lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada”. Surar Anbiya’i: 105-106. Hadisai kuwa sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa: Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Fadima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
[2] - Duba fadinsa madaukaki: “Kuma yayin da Isa dan Maryam ya ce: Ya Bani Isra’la lalle ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskata abin da yake gaba gare ni na Attaura kuma mai bayar da bushara game da wani Manzo da zai zo bayana sunansa Ahmad. Sai dai a yayin da ya zo musu da hujjoji bayyanannu sai suka ce wannan sihiri ne bayyananne”. Surar Saff: 6.
[3] - Amirul muminin Aliyyu Dan Abi Dalib (A.S) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: “Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai kuma shi ne mabubbugar hikima”. Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminin (A.S) yana cewa: “Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa. Ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo a duwatsu masu tsauri.” (Nahajul Balagha Huduba: 108).
Wallafar Allama Muzaffar
Fassarar Hafiz Muhammad
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Ƙara sabon ra'ayi