Alayen Annabi (a.s)

Alayen Annabi (a.s)

Yayin da Ayar nan ta Suratul Ahzab: 33 ta sauka, wato; “Hakika kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gare ku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa”[1]. Sai Manzo (S.A.W) ya kira Ali da Fadima da Hasan da Husaini (A.S) ya lullube su da wani bargo da aka yi wa zane da bakin gashin rakumi. Wannan Hadisi[2] ya zo a littafin Muslim, da Buhari, da Mustadrik Alassahihaini, da Tirmizi da Abu Dawud da Tafsirin Bagawi, da Ibn Kasir, da gomomin Tafsirai da Littattafan hadisai, kamar yadda wannan hadisin ya maimaitu a lokacin mubahala da kiristocin Yaman da sauran wurare da dama.
Akwai wata mahanga da take ganin cewa Ahlul Baiti (A.S) su ne Alayan Ali, da Ja’afar, da Akil, da Abbas, wannan shi ne nazarin Zaid Dan Arkam. Amma kuma duk mahangan sun hadu a kan kore matan Annabi (R.A) daga kasantuwa cikin Ahlul Baiti. Game da mahangar Zaid kuwa muna iya cewa; idan aka ce ga maganar Manzo (S.A.W) ka sani cewa ba wata magana da take da kima bayanta.
Kamar yadda ruwayoyin sun yi nuni da cewa Ummu Salama (R.A) ta so ta shiga cikinsu yayin da manzo (S.A.W) ya fassara wannan ayar da ta sauka ta tsarkake Ahlul Bait a aikace wacce take cewa: "Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku ne Ahlul Baiti Kuma ya tsarkake Ku tsarkakewa" amma Manzo (S.A.W) da kansa ya nuna mata ba ta cikin Ahlul Bait (A.S) domin matansa ba sa cikinsu, sai dai ita ma tana da nata alheri da ta samu.
A wannan aya muna iya gain manzon rahama ya fassara ta da cewa; Ahlul Bait (A.S) su biyar ne, idan muka hada tad a wasu hadisai da suka zo da Karin tara daga 'ya'yan imam Husain (A.S) kamar yadda ya zo, wato; halifofinsa guda goma sha biyu da kuma Fadima (A.S) wanda na farkon su shi ne Ali (A.S) na karshensu shi ne Mahadi (A.S)[3], wannan yana nuna adadinsu gaba daya a matsayinsu su goma sha uku ne, idan ka hada da manzo mai tsira da aminci sun tashi goma sha hudu kenan.
Ya zo a Tafsirin Ibn Kasir a tafsirin Aya ta 55 ta Surar Ma’ida cewa[4]: Daga Maimun Dan Mahran daga Ibn Abbas, a fadin Allah mai grima da buwaya:“Kawai majibancin lamarinku (Jagoranku) Shi ne Allah da Manzonsa da wadanda suka yi imani wadanda suke tsayar da Salla suke bayar da Zakka alhalin suna masu ruku’u”. Yana mai cewa: Ta sauka ne game da Muminai kuma Ali Dan Abu Talib (A.S) Shi ne na farkonsu. Wato tana mai nuni da cewa na farkon wadanda za a mika wa wilaya da Shugabanci bayan Allah da Manzonsa shi ne Ali (A.S) Sa’annan masu biyo wa bayansa na daga wasiyyai, kamar yadda zamu ga ta sauka ne a lokacin da ya yi sadakar zobensa alhalin yana cikin ruku’i. Wasu littattafan suna cewa; ta sauka game da muminai Ali (A.S) ne na farkonsu, Mahadi (A.S) na karshensu[5].
Mahangar Ahlul Baiti (A.S) game da ma'asumai da Allah (S.W.T) ya sanya su hujja kan al’umma bayan Manzon rahama su goma sha biyu ne, idan ka hada da Ma'asumiya Sayyida Zahara (A.S) Ma'asumai sun zama goma sha hudu kenan, wato Manzon Allah (S.A.W) da Fadima (A.S) da halifofinsa goma sha biyu (A.S) da ya yi wasiyya da bin su da suka hada da: Ali Dan Abi Dalib (A.S) Hassan Dan Ali (A.S) Husaini Dan Ali (A.S) Ali Dan Husaini (A.S) Muhammada Dan Ali (A.S) Ja’afar Dan Muhammad (A.S) Musa Dan Ja’afar (A.S) Ali Dan Musa (A.S) Muhammad Dan Ali (A.S) Ali Dan Muhammad (A.S) Hasan Dan Ali (A.S) sai na karshensu Imam Muhammad Mahadi Dan Hasan (A.S) wanda zai cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci..Ahlul Bait A Hadisai
Kamar yadda muka sani cewa; duk wani mai hankali ba zai yiwu ya tafi ya bar gidansa ba, ba tare da mai kula da gidan ba, kodai matarsa ko wani makamancin hakan, kamar yadda hankali yana hukunci da wautar mutumin da yake tafiya ya bar al’ummar da yake shugabanta kara zube ba tare da ya ayyana mata mai kula da ita.
Idan haka al’amarin yake ba yadda za a yi Manzon rahama mai tausayi ga al’umma wanda ya bayyana mata hatta da hukuncin shiga ban daki da yadda ake fita ya zamanto ya bar wannan al’amari mai girma na tafiyar da al’amuran musulmi ba tare da ya ayyana mai kula da shi ba, alhalin ya san irin al’ummar da ya bari wacce take cike da munafukai da masu son ganin musulunci ya rushe, kuma ga kafiran duniya na daulolin farisa da rumawa sun fara kawo wa daula hari, hada da cewa akwai jahiltar hukunce-hukuncen addini da musulmi kansu suke bukatar wanda zasu cigaba da komawa zuwa gareshi domin dauke kishirwar tambayoyinsu da abubuwa masu yawa da ba sa kirguwa.
Ashe ba jingina kaskanci da wauta ba ne ga mafificin halitta gaba daya, mafi hikimarta, mafi iliminta, wasu musulmi suke yi ba da suke jingina rashin barin halifa ga Manzo (S.A.W) wanda zai tsayu da irin wadannan al’amuran da muka lissafo da ma wasunsu masu yawa.
Idan ya kasance Manzon rahama (S.A.W) ba ya iya barin Madina koda na dan lokaci kankani ba tare da ya ayyana wani mai kula da ita ba, ashe zai yiwu ya san cewa zai bar duniya gaba daya sannan sai ya zamanto bai ayyana wa al’umma wanda zai maye gurbinsa ba! Don haka ne bisa hikimar Allah madaukaki tun farkon kiransa yake shaidawa da cewa yana da wasiyyi a wurare masu yawa da suka zo a ruwayoyi gun Ahlul Bait (A.S) da kuma daga ‘yan’uwanmu Ahlussunna, wanda wasu daga cikin wadannan ruwayoyi suna masu kawo sunansa wato imam Ali (A.S).
Don haka ne ma cikin hikimar Allah bayan hajjin bankwana sai ya umarci Manzo da ya karbi bai’ar musulmi ga imam Ali a matsayin halifansa bayansa tun yana raye, domin wannan ya zama hujja a kan musulmi da duniya gaba daya, kuma Allah ya cika haskensa da ni’imarsa garesu da wilayar imam Ali da Ahlul Bait (A.S) bayan Annabin rahama (S.A.W).
Saboda haka sai Manzo (S.A.W) ya umarci a tara mutane bayan sun fito daga Makka a lokaci mai zafin rana, kuma ya yi umarni da a dawo da wadanda suka yi gaba; suka yi nisa, kuma a jira wadanda ba su iso ba a wani waje da ake kira KHUM. Game da irin wadannan matakai da ya dauka masu tarihi suna cewa; ya dauke su ne domin muhimmacin al’amarin kuma da hikimar ya zama ya wanzu a kwakwalen mutane ne.
Bayan jama’a sun taru ne ya sa aka kafa wani mimbari ta yadda kowa zai ji shi, kuma ya gan shi, sannan sai ya hau kan mimbarin ya yi huduba mai tsayi, daga cikin abin da wannan huduba mai tarihi ta kunsa ya zo kamar haka:
Aka tara mutane aka yi masa minbari sannan sai annabi (S.A.W) ya hau kansa bayan ya yi salla a cikin wanan taron na musulmi sannan sai ya godewa Allah ya yabe shi, ya fada da sauti madaukaki da duk wanda yake wajan yana jin sa: “Ya ku mutane! Ya kusata a kira ni sai in amsa, ni abin tambaya ne, ku ma ababan tambaya ne, me zaku ce? Suka ce: Mun shaida ka isar da sako ka yi nasiha, ka yi jihadi, Allah ya saka maka da alheri. Ya ce: Ba kuna shaidawa cewa babu wani ubangiji sai Allah ba, kuma Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, kuma cewa aljanna gaskiya ce kuma alkiyama mai zuwa ce babu kokwanto a cikinta, kuma Allah yana tayar da wanda suke cikin kaburbura? Suka ce: Haka ne mun shaida da hakan. Ya ce: Ya ubangiji ka shaida. Sannan ya ce: Ni zan hadu da ku a tafki, kuma ku zaku zo mini a tafkin, wanda fadinsa ya kai tsakanin San’a’a da Busra, a ciki akwai kofuna na azurfa sun kai yawan taurari, ku duba ku gani yaya zaku kusance da alkawura biyu masu nauyi bayana”.
Sai wani ya daga murya yana mai tambaya; ya Manzon Allah (S.A.W) menene alkuwura biyu masu nauyi? Manzon Allah ya ce: Alkawari mafi girma shi ne Littafin Allah, gefensa a hannun Allah daya gefen a hannunku, ku yi riko da shi kada ku bata, dayan kuma mafi karanta su ne Ahlina (Ahlul Bait). Hakika (Ubangiji) mai tausayi mai sanin komai ya bani labari cewa; ba zasu taba rabuwa ba har sai sun riske ne a tafki, kuma na roka wa abububwan nan biyu wannan a wajan ubangijina. Kada ku shiga gabansu sai ku halaka, kuma kada ku takaita gabarinsu sai ku halaka”.
Sannan sai ya yi riko da hannun Ali dan Abu Talib (A.S) har sai da aka ga farin hammatarsu, mutane suka san su gaba daya. Sai Manzo ya ce: “Ya ku mutane wanene ya fi cancantar biyayyar muminai fiye da kawukansu? Suka ce: Allah da Manzonsa su ne mafi sani. Ya ce: Ubangiji shugabana ne, kuma ni ne shugaban muminai, kuma ni na fi cancanta da biyayyar muminai fiye da kawukansu, to duk wanda nake shugabansa wannan Ali shugabansa ne”, yana maimaita wannan har sau uku.
Sannan sai ya ce: “Ya ubangiji! Ka jibanci lamarin wanda ya bi shi, ka ki wanda ya ki shi, ka so wanda ya so shi, ka kyamaci wanda ya kyamace shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya bar shi, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya, ku sani wanda ya halarta ya isar wa wanda bai halarta ba”.
Sannan jama’a ba ta watse ba har sai da Jibrilu ya sauka da wahayin Allah da fadinsa: “Yau ne na kammala addininku gareku, kuma na cika ni’imata a gareku, kuma na yarda da musulunci addini gareku”[6].
San Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Allah mai girma a kan kammala addini da cikar ni’ima da yardar ubangiji da manzancina da shugabanci ga Ali (A.S) bayana”.
Sannan sai ya yi umarni aka kafa hema ga Ali (A.S) kuma musulmi su shiga wajansa jama’a-jama’a suna yi masa sallama da bai’a a kan shugabancin muminai, sai duk mutane suka yi hakan, ya umumarci matansa da sauran matan muminai da suke tare da shi su ma suka yi bai’a.
Daga cikin na gaba wajan yi masa murna da bai’a akwai Abubakar da Umar dan Khaddabi, kowannensu yana cewa: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abu Talib, ka wayi gari, ka yi yammaci shugabana kuma shugaban dukkan mumini da mumina[7].
Bahasin Son Ahlul Baiti (A.S)
Madaukaki ya ce: “Ka ce ni ba na rokon ku wani lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai”. Surar Shura: 23. Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko da Ahlul Baiti (A.S), wajibi ne a kan kowane musulmi ya dabi’antu da sonsu da kaunarsu domin a ayar da aka ambata an takaita abin da ake nema daga mutane da nuna soyayyar makusantansa (A.S). Ya zo ta hanyoyi masu yawa da cewa; Son su alamar imani ne kin su kuma alamar munafinci ce, kuma duk wanda ya so su ya so Allah da manzonsa, wanda kuma ya ki su, to ya ki Allah da Manzonsa (S.A.W).
Hakika son su wajibi ne daga laruran addini da ba ya karbar jayayya ko kokwanto. Domin dukkan musulmi sun hadu a kan hakan duk da sabanin mazhabobinsu da ra’ayoyinsu, in ban da kadan daga wasu jama’a da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda aka sanya musu sunan “Nawasib” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyar Annabi (S.A.W), don haka ne ma ake kirga su a cikn masu inkarin abin da yake wajibi na addinin musulunci tabbatattu, wanda kuma yake karyata larurar Addini ana kirga shi a cikin masu karyata ainihin sakon musuluncin koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada, saboda haka ne kin Ahlul Baiti (A.S) ya zama daga alamomin munafunci son su kuwa ya zama daga alamomin imani kuma don haka ne kinsu ya zama kin Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W).
Kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai wajabta son su ba sai don su sun cancanci soyayya da biyayya ta bangaren kusancin su da Allah da manzonsa, da tsarkinsu, da nisantar su ga shirka da sabo, da kuma dukkan abin da yake nisantarwa daga karimcin ubangiji da yardarsa. Ba zai taba yiwuwa ba a suranta cewa; Ubangiji ya wajabta son wanda yake aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa, domin shi ba shi da wata kusanci ko abotaka da wani, mutane a gurinsa ba komai ba ne sai bayi ababan halitta masu matsayi daya, kadai mafificinsu a gurin Allah shi ne mafi tsoronsu gareshi. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafi takawarsu, kuma mafi darajarsu baki daya, ba don haka ba, da waninsa ya fi cancantar wannan soyayyar, kuma da ya kasance kenan Allah yana fifita wasu mutane a kan wasu a wajabcin so da biyayya haka nan kawai ko da wasa ba tare da cancanta ko daraja ba.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Monday, 27 July 2009

[1] Ahzab: 33.
[2] Muslim: J 4, h 1871. Da Tirmizi: j 5, s 351, h 3205. Da Baihaki: 7: 63. Da Masnad Ahmad: 6: 292, 304.
[3] Ma’a rijalul fikr: j 1, sayyid murtadha arridhawi: shafi 230.
[4] Tafsirin Ibn Kasir: a tafsirin Aya ta 55 ta Surar Ma’ida.
[5] Ma’a rijalul fikr: j 1, sayyid murtadha arridhawi: shafi 230. Da kuma littafin: Al’anbiya afdhalu minal mala’ika, wa nabiyyuna afdhalul anbiya, markazul musdapha, shafi: 410.
[6] - Ma’ida: 3.
[7] - Tarihin yakubi: 3/112. Masnad Ahmad: 4/281. Albidaya wannihaya: 5/213. Mausu’atul gadir: 1/43, 165, 196, 215, 23, 238. 11/131.

Ƙara sabon ra'ayi