Nau'o'in Mutane

Nau'o'in Mutane

Mutane sun kasu kashi daban-daban; akwai wadanda ake cewa kebanattu, ko masu tunani, ko kuma zababbu a cikin mutane. Su wadannan zamu kira su da sunan mutane na musamman ko masu tunanin al'umma. Don haka al'umma a ko'ina a duniya sun kasu gida biyu ke nan, akwai masu tunani da kuma masu bin duk wani tunani; wadannan kaso na biyu su ba kasafai suke tunanin kansu ba, duk wani abu da ya zo musu sai su yi imani da shi da gaggawa kuma su zauna a kai, wadannan mutanen ba sa bukatar dalili na shari'a ko na hankali, suna bukatar su ji ne kawai sai su yarda. Amma masu tunanin al'umma suna da tasu mahanga a kan kowane abu ne suka ji, kuma suna neman dalili a kai domin su samu gamsuwa, sannan kuma sai su bayar da nasu ra'ayi, wadannan a kowace al'umma su ne 'yan kadan.
Kafin mu yi nisa bari in ba mu misali; Da za a biyo wani mutum ana barawo! barawo! Wadancan kaso na farko da muke kira masu tunanin al'umma zasu nemi a tsayar da shi mai ihun da wanda aka koro ne a saurari me suke cewa! Ana neman hujja daga wurinsa ne cewa me aka satar masa? shi kuwa wanda aka koro za a tambaye shi haka ne ko kuwa? A nan ne shi barawon da wanda yake da'awar an yi masa sata zasu bayar da bayani domin a samu gamsuwa da maganar daya daga cikinsu, sannan sai a yanke hukunci tsakaninsu daidai gwargwadon yadda hujjoji suka tabbata. Amma sauran yuyar al'umma da ake kiransu 'yan bi ta zuwai ba haka suke ba, suna ma iya make wannan mutumin da aka biyo ana yi masa ihun barawo! Ba su sani ba ko wannan mai ihun sharri ne yake yi masa ko kuma yana jin haushinsa don wata hassada ne da yake so ya kashe shi saboda ita. Kuma tun da ya san mafi yawan mutane da halayensu na rashin sanya tunani a lamurransu, sai ya yi masa ihu don ya gama da shi!
Sai dai an yi sabani kan su waye kebantattun mutane masu tunani a cikin al'ummu; wasu suna ganin su ne masu karatu da ilimin al'umma, wasu kuwa suna ganin sun hada da masu mulki da marubuta, da masu arzikin al'umma, da likitoci, da injiniyoyi, da sauran masu mukamai a gwamnatoci. Sai dai dukkan wannan ra'ayi ya sha kaye, domin idan muka duba zamu samu wasu masu karancin tunani, da fahimta a cikin wadancan mutane da aka zana, kana iya samun shugaban kasa, ko gwamna, ko farfesa, ko shehin malami, ko babban dan kasuwa da attajiri, ko lauya, ko alkali, ko likita, da irin wancan siffofin na marasa zurfin tunani a cikin mutane!.
Don haka ne muka samu Ayatul-Lahi Sayyid Ali Khamna'i jagoran juyin musuluncin Iran yana kawo cewa: Ammawan mutane; (wato marasa tunanin al'umma) ba su ne wadanda ba su da ilimi mai zurfi ba, kana iya samun wanda ya kai kololuwar sani da ilimi amma yana cikin ammawan mutane, ba'amme (wato marasa tunani cikin al'umma) yana iya kasancewa talaka, ko mai kudi, jahili ko malami. Ammanci ba hannuna ko hannunka yake ba, don haka dole ne mu yi hattara kada mu fada cikinsu, don haka duk wani wanda ba ya aiki bisa basira to ba'amme ne, don haka sai mutun ya duba idan ba ya aiki bisa hankali da tunani da hangen nesa, sai ya yi gaggawar fita daga cikin wadannan mutane. Ya yi kokarin ganin ya samu ikon yin warwarar lamurran da yake fuskanta da tunani, ya kuma gano inda matsalar take, sannan sai ya yi amfani da ilimi domin samun mafita. (Laccar sayyid Khamna'i: ga Lashgari Muhammad Rasulul-Lah, 20, 3, 1375, H. Sh)".
A cikin wannan bayanin nasa mai nuni da karancin tunanin ‘yan bita-zuwai game da abin da yakan kai ya komo, musamman a irin farfagandar da hukumomin yamma suke yadawa kan kasar Iran, Ayatul-Lahi Sayyid Khaman'i yana cewa: "Hukumar zalunci duk abin da ta ga dama sai ta fada, amma me ya sa mutane suke yarda?! Mutane shiru suke yi, kuma wannan ita ce matsalar da ake ciki". Amma da ya juya kan abin da ya faru na rashin imani da dabbaci da aka yi kan alayen Annabi (s.a.w), da kashe Imam Husain (a.s) a Karbala, ya yi nuni da yadda ammawan mutane suke da karancin tunani, ta yadda a lokaci guda kakan iya samun canji a tunaninsu ba tare da sanya hankali ba.  Sayyid a nan yana cewa: "A wannan lokacin lalacewa da gafala ta kai ga cewa; Jikan wadanda aka kashe a yakin Badar a hannun Imam Ali (a.s) da Hamza da sauran dakarun musulunci ya hau kan mukamin matsayin jagorancin al'umma da yake matsayi ne na manzon Allah (s.a.w), kuma ya kashe jikan manzon Allah (s.a.w) wanda yake shi ne sanyin zuciya da idanuwan manzon rahama (a.s). Ya kashe jikan Annabi (s.a.w) sannan ya kishingida a kan karagar mulki, yana wasa da kan jikan manzon Allah (s.a.w) da aka ciro masa, yana mai wakar isgili da addini yana cewa: "Ina ma dai Kakannina da aka kashe a Badar sun ga, yadda na daukar musu fansa". Tarih dabari: j 11, shafi; 358, a tsohon bugu.
Don haka kana iya samun mai sayar da dankali a bakin titi amma yana iya warware abubuwa bisa tunani da basira, yayin da kana iya samun laccara a cikin Jami'a amma yana bin yu-yu ba ya aiki bisa basira da fahimta! ba ya buda tunaninsa! ba ya aiki da hankalinsa! Wani ma halinsa ya kai munin da komai ya durfafa yana sanya masa fushi, da gaggawa, da karancin fahimta domin warwarewa! Irin wadannan mutane kana iya samunsu a Jami'o'inmu da manyan makarantu a matsayin masu jagorantar ilimin kasa. Wannan ya yi daidai da fadin Imam Ali (a.s) da yake cewa: Da yawa malamin da jahilcinsa ya kashe shi, kuma iliminsa yana tare da shi ba ya amfanarsa. Nahajul Balaga: Hikima; 102. Amma na ga direban Taksi (Tadi) a Sep, 2008, da na dade ban samu mai magana da hankali kamarsa ba! don haka kowace kasa, kuma a kowane wuri, kuma a kowane zamani, al'umma daya ne ba su da bambanci, babu bambanci tsakanin lokacin Annabi Adam (a.s) da lokacin Annabi Musa (a.s), da kuma lokacin Annabi Muhammad (s.a.w), da wannan lokaci namu, mutanen nan dai su ne mutanen!.
Wasu mutane sun kirkiro ruwayoyi hada da rashin fahimtar wasu ruwayoyin da suka dangana wa Annabi (s.a.w) cewa: "Lokacinsa ya fi kowane lokaci, sannan sai mai biye masa, sannan sai mai biye masa". Fatahul Bari: ibn Hajar, j 7, shafi; 6. Wannan lamarin ya saba wa Kur'ani da hankali; Kur'ani yana cewa: "Wadannan da suke kiran ka ta bayan dakuna mafi yawansu ba su da hankali". Hujurat: 4. Kamar yadda zamu ga ita wannan al'ummar ce dai da manzon Allah (s.a.w) ya bari ta kashe duk jikokinsa bayan wafatinsa da shekaru 50 kacal, kai ta yi sanadin mutuwar 'yarsa ma bayan wata biyu da wafatinsa babu wani wanda ya tausaya mata, hasali ma sun ce kukanta ya dame su, don haka aka fitar da ita gefen gari aka gina mata dan dakin da take kiransa da dakin bakin ciki. Haka nan ta sha wahala da ita da mijinta, da 'ya'yanta, alhalin jagoran al'umma kuma babanta, kuma Annabin karshe da babu wani wanda ya fi shi daraja, kuma kowa ya san hakan, kuma ya yarda da hakan, amma sai suka kasance cikin irin wadannan ayyuka munana!. Sannan abin mamaki yayin da matar manzon Allah (s.a.w) ta nemi taimakon al'umma domin yakar dan'uwansa kuma wasiyyinsa (a.s) sai ga al'umma ta ba ta cikakkiyar gudummuwa. A yanzu da wannan halin, sannan muna ganin yadda wata al'umma take kashe kanta a wannan zamanin saboda jagoranta, da tsananin soyayya da girmamawa ga 'ya'yansa, sannan sai mu ce al'ummun baya sun fi ta aiki da hankali da basira!?
Don haka masu tunanin al'umma mutane ne da suke daga kowane nau'in mutane da suka hada da masu sana'o'i hatta da sana'o'in da ake wulakanta masu su, ana ganinsu a matsayin marasa kima. Ashe ke nan babu wani wanda ya isa ya daga kai cewa shi yana daga cikin masu tunanin al'umma domin kawai yana da dukiya ko ilimi, ko kuma domin yana da wani mukami ko kampani, balle kuma wanda ya fi kowa wauta mai takama da cewa; shi dan wane ne. Allah ya kira Annabi Ibrahim (a.s) al'umma daya, domin ya taso a cikin al'umma mai bautar gumaka, sannan sai ya barranta da wadannan gumaka, domin yana aiki bisa fahimta da warware al'amura cikin hankali, yana ganin gumakan da mutum ya sassaka sannan sai don wauta ya zo yana gurfana musu yana neman biyan bukatunsu! A nan ne Allah ya tabbatar da cewa; Annabi Ibrahim yana cikin masu tunanin al'umma, sannan daga baya ya ba shi matsayin annabta, kuma daga baya ya zabe shi a matsayin imami da yake matsayi na musamman da babu kamarsa!.
Mai karatu kana iya tabbatar da cewa; ke nan Allah yana yabon masu hankali, da lura, da fahimta, kuma yana kushiya da zargi ga marasa fahimta. Duba ayoyin Kur'ani masu yawa da suke cewa: Kadan ne masu fahimta! Kadan ne masu ganewa! Kadan ne masu ilmantuwa! Amma mamakin da duniya ta samu kanta a yau, sai ga shi akwai masu gaba da ilimi gaba mai tsanani, hasali ma wasu suna fitar da mai ilimin mantik da palsapa daga da'iran musulunci saboda tsananin jahiltarsu da nisantarsu daga hankali. Sai dai kada mu dauka duk masu tunanin al'umma suna kan daidai ne, don haka yaki ne ja a kanmu na ganin mun samu kanmu cikin masu fahimtar al'umma, amma wannan share fage ne kawai don mu sani! Share fage ne na fadawa wani dauki ba dadin shiga cikin zurfafa tunani domin tace daidai da gane abu na kwarai. Sau da yawa kana ganin masu tunanin al'umma amma sai su zabi wani abu daban da bai dace ba, wannan kuwa zabin bisa tunaninsu ne suke yinsa. Muna iya ganin wasu masu tunani da rikicin musulmi ya tashi sai suka goyi bayan Mu'awiya dan Abu Sufyan, alhalin sun san cewa; Ali (a.s) shi ne yake da gaskiya!. Sun sani sarai cewa; manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ali yana tare da gaskiya, kuma gaskiya tana tare da Ali (a.s), tana juyawa tare da shi duk inda ya juya. A nan ne ya kamata kowa ya san cewa; kasancewar mutun cikin masu tunanin al'umma ba yana nufin yana kan daidai ba!.
A yanzu akwai mai kokwanton cewa; Fir'auna yana cikin masu tunanin al'umma? ko akwai mai kokwanto Ma'amun mai zurfin ilimi da tunani yana cikin kebantattun al'umma? Ko akwai mai kokwanto cewa; Hitla yana cikin zababbun masu tunanin al'umma? Kai babu wani mai kokwanto ko kusa cewa; da yawa daga cikin shugabannin Amurka na da, da na yanzu da sauran kasashen yamma ba sa cikin masu zurfin tunani da hangen nesa? Amma a wadannan mutane masu tunani duk wanda ya kauce wa tafarkin gaskiya imaman Ahlul Bait (a.s) ba su kira shi mai hankali ba, sai suka kira abin da yake yi da shedana. Shedana ba ta fitar da mutum daga cikin masu tunani, sai dai tana fitar da shi daga cikin masu hankali, sai ya kasance yana da tunani amma ba shi da hankali. Domin hankali shi ne amfani da tunani wurin bin gaskiya da ilimi, shi ne abin da aka yi amfani da shi wurin biyayya ga Allah! Idan aka yi amfani da tunani wurin kaucewa gaskiya bisa kowane dalili ne sai a kira ta shedana, wannan ce amsar da imam Sadik (a.s) ya bayar game da Jagoran "Fi'atul Bagiya" wato; al'umma mai kauce hanya. Alfusulul Muhimma: j 1, shafi; 123. Da Nahajul Balaga: j 2, shafi; 180. Kuma ita ce dai amsar da zamu iya bayarwa kan mai bayar da shawara na Yazid. Yazid ba'ame ne ba ya cikin masu tunani, amma mai ba shi shawara Akhdal Kirista ne kuma yana daga cikin masu tunanin al'umma, sai dai tunaninsa ba komai ba ne sai shedana, ba hankali ba ne domin ya kaucewa gaskiya! Domin ba ya tunani sai shirya yadda za a ruguza tsarin manzon Allah da kawar da jikokinsa daga doron kasa!. Al'agani: j 7, shafi; 170.
Sai dai wasu masu tunanin sukan samun matsalar shamaki ne mai yawan gaske, ga kuma jahiltar hakikanin gaskiyar addinan Allah da wahalar bincikar gaskiya game da su yana taimakawa! al'adu da gado suna dankwafarwa! Sannan kuma ga karfin yanayin al'adun al'umma da dan Adam yake tasowa a cikinsa yana tare da tunkudar da tafi karfin ya sha gabanta!. Don haka ne sai ka ga mai tunanin al'umma amma yana cikin wani yanayi da zai iya kasa gane gaskiyar lamurra, sai ya sanya hankalinsa amma ba ya iya fita daga gargajiyar al'ummarsa. Mu sani da yawa akwai masu tunani a kasar Indiya, amma tunaninsu ya kasa fita daga cikin wannan al'adunsu, sai suka fassara komai bisa ga yadda suka gada. Mr Sarkar game da nazarinsa na yadda duniya zata kare a karshenta a fili yake cewa tasirin al'ada da addini suna cike cikin nazarinsa da ra'ayoyinsa. Kwamacalar al'adu da take kasar Indiya ba zata bari masu tunaninta su fita daga wancan kangin ba, wannan kwamacalar ko a jiya an nuna a kafafen watsa labarai yadda ake kashe 'ya'ya mata a Indiya a cikin wannan wata na August. Masu tunaninsu ba su nuna musu cewa; Namiji ke da Koromozoms ba, don haka haihuwar mace ko namiji daga kwayoyin maniyyinsa ne, babu wata takaitawar mace a ciki. Kai hatta da kasashenmu da yawa suna jin haushin matansu don suna haihuwar mata saboda jahilci, bai san cewa abin daga gareshi ba ne!?
Irin wannan dabaibayi na jahilci da rashin samun sako, ga kuma al'adu da wayewar da mutum ya taso a cikinta, ga kuma tarbiyyar da ya samu a cikin al'ummarsa ko kabilarsa, duk suna da tasiri matuka wurin ganin an samu ma'abota tunani sun kaucewa hanya. Sai dai wasu abubuwa ne da Allah yake karbar uzurin wasu daga ciki; Allah madaukaki yana cewa: "Ba mu kasance mai azabtarwa ba har sai mun aika manzo…". Surar Isra': 15, don haka ne wasu lamurran suna iya warwaruwa. Amma akwai abubuwan da suka saba wa hankali, wadannan abubuwa ne da Allah ba ya bayar da uzuri a kansu: A yanzu wane uzuri ne ga Farfesa a Mathematic, da Mantik, da Palasapa, yake da shi yayin da yake bauta wa shanu da sauran halittun dabi'a a kasashen Indiya! Ina hankalinsa yake! Kuma wane uzuri ne ga wanda yake binne 'ya'ya mata yana kashe su a kasashen Indiya a yau din nan!? Wane uzuri ne ga masu sace mana dukiya suna jibgewa a kasashen yammacin duniya domin su ci da su da 'ya'yansu kawai alhalin al'ummarsu tana cikin bala'in talauci da rashi!? Mai irin wadannan halayen komai tunaninsa da zurfin hankalinsa abin da yake yi sunansa Shedana!
Wani lokaci tsoro da kwadayin duniya yana sanya masu tunanin al'umma su kauce wa hanyar kwarai: misalin wannan a lokacin imam Husain (a.s) a fili yake; wannan son duniyar yana iya kasancewa gida ne yake kwadayi ko kuwa mace, ko dukiya, ko mukami, ko neman suna, ko kuma domin kada ya rasa wata rayuwa tasa. Tana iya kasancewa domin kada a jefa 'ya'yansa cikin wahala, ko kuma a kwace masa dukiya, ko hana shi kasuwancinsa, ko ma a takura ko kashe danginsa, ko mafi muni lalacewar rai da miyagun halaye!. Da a ce alkali shuraihu, da Shibs bin Rubi da wasunsu na daga masu matsayi da fada a ji a cikin mutanen garin Kufa ba su ji tsoro ba, tayiwu da yanzu ba a samu faruwar rana irin ta Karbala da aka kashe jikokin manzon rahama (a.s) daya bayan daya a wurin ba! Da a ce mutanen Kufa zababbunsu da mabiyansu ba su nuna tsoro da kwadayin duniya ba, da ba a samu irin wannan mummunan abin da ya faru ba a tarihi na kawar da jikokin ma'aikin Allah daga doron kasa ta hanyar kisan wulakanci.
Masu tunanin wannan al'umma duk sai suka kasance sun dulmuye cikin son duniya da dalilai mabambanta; wani cikin tsoro da razanin kada ya rasa ransa, wani kuma kada ya rasa matsayinsa da dukiyarsa, wani kuma kada ya rasa 'ya'yansa, sai suka mika wuya, sai mabiyansu suka goya musu baya!. Al'amarin al'umma yana da bam mamaki! Yayin da al'ummar garin Kufa ta kasance da sallar isha tana goyon bayan Muslim dan Akil da imam Husain (a.s) ya aiko, sai ga shi saboda kawai an samu juyawar bayan masu tunaninta da dalilai mabambanta da muka kawo, aka yada mata jita-jita cikin dare, sai ga shi a wannan daren da garinsa ya waye babu koda mutum daya tare da Muslim dan Akil. Wannan ne halin 'yan bita zuwai, suna bin duk inda suka ji an karkata ne, idan aka yi yamma sai su yi nan, idan aka ce masu ai gabas ne sai su koma can, idan kuwa aka ce ku yi arewa, sai su gargada da sauri babu wani tunani. Sai ga mutanen da suka kirawo Imam Husain (a.s) su ne suka koma masu yakarsa a cikin lokacin kankani. Da wannan muna iya gani a fili yake cewa; da mutane masu tunanin cikin al'umma da saraun jama'a duka suna cikin hadari, don haka tambaya a nan me za a yi domin samun tsira!?
Don haka ne Allah (s.w.t) ya sanya wa kowace al'umma jagororin da zasu kare ta daga fadawa cikin bata da halaka, sai ya sanya wa kowace al'umma Annabi (a.s), ko mai gargadi wadanda yawancinsu wasiyyan annabawa (a.s) ne da suke bari bayan wucewarsu. Haka nan zamu ga manzon rahama (s.a.w) mafi daukakar bayi a doron kasa (s.a.w) ya zo cikin wannan al'ummar, kuma da zai tafi sai ya bar mata imamai goma sha biyu masu wanzuwa a cikinta har tashin alkiyama domin kariya ga kebantattun al'umma da sauran al'umma daga kaucewa, wannan shi ne sirrin samar da jagora daga Allah a cikin kowace al'umma, sai dai ita al'umma tana da zabi ko ta bi ko kuma ta ki!

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center
Sunday, August 30, 2009

Ƙara sabon ra'ayi