Bahasin Kur'ani

Bahasin Kur'ani    
 
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin K'ai
Hak'ik'a wannan (Littafin na) Kur’ani yana shiryarwa zuwa ga abin da shi ne ya fi zama daidai, kuma yana yi wa muminai wad'anda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa lallai suna da lada mai girma. 17: 9.

Littafin Allah Mad'aukaki
Hak'ik'a Allah ya saukar da kur’ani mai girma mai ingancin da babu wani kowanto a cikinsa, kuma b'arna ba tazo masa ta gabansa da ta bayansa,kuma ya jib'anci d'aukar nauyin kare shi da kansa.sannan kuma sai manzon Allah (S.A.W) ya yi sharhinsa yayi bayaninsa da maganganunsa da ayyukansa mad'aukaka, don haka babu wani abu da ya rage mana bayansa sai neman fahimtarsa da aiki da shi. Kuma kur’ani littafi ne da yake magana da mutane a kowane zamani da wuri, ya sauka yana mai bayanin komai. Sai dai kuma ba ya iya cimma fahimtarsa da gane shi sai da abin da ya zo da su na daga asasai da usulubai da wajibi ne a bi su. Wad'annan asasai dausulubai d'in kuwa ita ce wacce shi kur’anin ya bayyana ta saboda kaiwa zuwa ga fahimtarsa, kuma kowane malami da yake son bin ta zai iya kaiwa gareta. Yayin nan ne zai sami sharhin da annabi (S.A.W) ya yi mata. Kuma zai ga kur’ani da sunna suna kammala juna ne, kuma wannan ne zai bud'e masa wasu fagage sababbi masu fad'i da zai aminta da su a cikin bincikensa.

K'age A Kan ‘Yan Shi'a
Daga cikin b'ab'atu da tuhumar da ake amfani da su domin sukar Mazhabar Ahlul Baiti (A.S) domin rusa ko ruguza wannan mazhabi mad'aukaki da k'ima da daraja wanda yake dogaro da abin da ya zo daga wasiyyar annabi (S.A.W) ta biyayya ga Ahlul Baiti (A.S) bayansa, kuma ta dogara da kur’ani mai daraja da sunnar annabi (S.A.W) ingantacciya a kan hakan. Amma sai ga mak'iya wannan mazhaba mad'aukakiya ta alayen annabi (S.A.W) ba ta gushe ba tana samun zagon k'asa da suka daga mak'iyanta, da k'age-k'age da tuhumce-tuhumce, da kuma jafa’i da mugun k'ulli da b'atanci domin ganin sun ruguza k'ima da daraja da inganci na wannan mazhabi mai d'aukaka domin k'ok'arin ganin sun nisantar da dukkan al’ummar musulmi daga fahimtar sak'on da take d'auke da shi, wanda yake k'unshe cikin abin da muka ambata, da kuma kawar da su daga karanta littattafan wannan mazhabi mai daraja, da kuma neman hana sauran musulmai yin hulda da su da hana tattaunawa da su, domin kada su tasirantu da karfafan hujjojin da suke da su, wad'anda suka dace da fidirar dan Adam wacce ba ta gurbata ba.
Kuma sanannen al’amarine cewa wannan mazhabi yana amfani da hujjojin da suka ginu akan kur’ani da sunna da hankali masu gamsarwa da kowane d'an adam mai adalci zai mik'a wuya garesu bayan komawa zuwa garesu. Kuma duk wanda ya koma wa littattafansu to lallai zai iya fahimtar gaskiyar da yake cikin sak'onsu mai girma kuma duk wani hijabi da shamaki da aka gindaya masa domin k'iyayya ko nisanta daga wannan mazhabin to zasu yaye su kwaranye. Kuma wannan yana iya sanya shi mik'a wuya ga Ahlul Baiti (A.S) da karkata zuwa ga maganganunsu ko kuma mafi k'arancin abu da zai yi, shi ne; ya yi adalci ga mabiyansu.
Daga cikin mafi had'arin k'age da ake yi wa wannan mazhabin da mabiyinsu Shi'a shi ne; mas’alar cewa sun yi imani da tawayar kur’ani, kuma suna da wani Kur'ani koma bayan wanda yake hannun sauran musulmai! Da tuhumar cewa Shi'a sun jirkita Kur'ani, da cewa; kuma sun caccanza ayoyinsa da cewa; wai sun k'ara wasu ayoyinsa kuma sun cire wasu daga cikinsa! da sauran makamantan irin wad'annan tuhume-tuhume da k'age-k'age da b'atanci da k'arairayi marasa asasi da tushe.
Hujjar Masu Kage A Kan Shi'a
Masu kage sun dogara da wasu tsirarun ruwayoyin da aka samo a gun 'yan shi'a ne wad'anda ta yiwu wani ya iya fahimtar abin da ya yi kama da kagen da suke yi na cewa an jirkita Kur’ani mai girma, sai dai, manyan malaman shi'a da masu bincikensu, sun yi bayani kan wad'annan ruwayoyi inda suka nuna cewa wad'annan ruwayoyi sun zo cikin babi ne na nawadir, wanda irin wad'annan hadisan ba a iya dogaro da su, don kuwa mafi yawansu ruwayoyi ne wad'anda d'aid'aikun mutane suka ruwaito (wanda ake kira aahaad) ko kuma ka samu ba su da cikakken sanadi, mursalai ne, wad'anda ba a iya dogaro da su a irin wad'annan al'amura muhimmai.
A takaice lallai manya manyan masanan shi'a sun k'arfafa kan rashin canza Kur’ani mad'aukaki kuma sun kawo k'wararan dalilai wad'anda suke nuna cewa Kur'ani mai girma ba jirkitacce ba ne. Wato babu wani k'ari ko ragi a cikinsa, kuma mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun yi imani cewa Kur’anin da Allah ya saukar wa Manzo (S.A.W) shi ne dai wannan Kur’anin da aka sani, wanda kuma musulmai suke amfani da shi a tsakaninsu, a kowane zamani, shi ne kuma dai wannan Kur’anin da ake buga shi a k'asashen musulmi daban-daban, a Masar ko Suriya ko Lebanon ko kuma Irak'i ko Saudiyya ko Iran, ba tare da an samu wani bambaci tsakanin wad'annan Kur'anan ba, domin kuwa Allah mad'aukaki ya riga ya kare shi. Da kuwa za a ce an ga wani k'ari ko ragi cikin wani daga cikinsu, to da musulmai sun sani, kuma da sun guje shi, kana sashensu ya hana sashe amfani da shi. Ga abin da Allah Mad'aukaki Yake cewa dangane da kare Kur’ani: “"Hak'ik'a Mu muka saukar da Kur’ani kuma Mu masu kariya ne gareshi”. Hijr: 9.

Littattafan Hadisai Gun Shi'a
Shi'a Imamiyya ba su yi imani da samuwar wani littafi na ruwaya wanda babu kuskure a cikinsa ba, kuma wannan littafin nasu ne ko na waninsu. Saboda haka littafi matuk'ar ba Kur'ani ba ne, ba sa ganinsa ma’asumin littafin da babu kuskure a cikinsa, domin kuwa dukkanninsu ba su wuce a yi bincike a cikinsu game da sanadinsu ko mataninsu ba domin tsage da fayyace ingantattun ruwayoyi da wad'anda ba ingantattu ba. Sabanin abin da Malaman Ahlus Sunna suka yi imani da shi kan cewa dukkan ruwayoyin da suka zo a cikin littafin Bukhari da Muslim ingantattu ne, don haka ne ma suka sanya musu sunan sahihaini, wato ingantattu biyu.
Idan dai har ya inganta mutum ya hukunta cewa 'yan Shi'a sun yi imani da jirkita Kur’ani ba don komai ba sai kawai domin wasu tsirarun ruwayoyi da aka samu a cikin littafansu, wad'anda ta yiwu wani ya fahimci irin abin da aka jingina musu cikin zalunci da kage inda aka ce wai sun yi imani da jirkicewar Kur'ani. Ahlussunna ba su da tacewa game da kagen da suke yi kan Shi'a game da al’amarin jirkicewar Kur'ani mai girma domin abin da ya zo a littattafansu ya wuce wanda suka samu yawa a cikin littattafan Shi'a na daga raunanan ruwayoyi. Kuma muna iya komawa ga misalai kamar haka:
Jirkicewar Kur’ani A Littattafan AhlusSunna
Ya zo cikin littafm Sahih Bukhari juzu'i na 2 babin Aswak, daga Ibnu Abbas cewa ya ce: Ukkaza da Majna da Zul Majar sun kasance kasuwanni a zamanin jahiliyya, yayin da musulunci ya zo sai suka dakatar da saye da sayarwa, sai Allah Mad'aukaki ya saukar da cewa: “Laisa alaikum junahun fi mawasimil Haj” Ma'ana: “Babu laifi a kanku cikin lokutan Hajji”, Sai aya ta sauko tana cewa za su iya yin kasuwanci a lokacin Hajji, alhali kuwa babu irin wannan aya mai lafazi kamar haka a Kur’ani, duk da kuwa cewa kasuwanci ya halatta da wasu ayoyin da suka tabbata a Kur’ani.
Kuma ya zo a cikin littafin Muwatta na Imam Malik juzu'i na biyu a kitabul Hudud cikin wani dogon hadisi cewa yayin da Halifa Umar bin Khattab ya taho daga Mina, har zuwa inda Halifa Umar yake cewa: Ahir dinku daga halaka kan barin ayar rajamu (jefe mazinata), kada wani ya ce mu ba mu ga wani zance a littafin Allah (kan jefe mazinata ba) to hak'ik'a Manzo (S.A.W) ya jefe mazinata kana mu ma mun jefe su, na rantse da wanda raina ke hannunsa, da ba don kada mutane su ce Umar ya k'ara wani abu cikin littafm Allah ba, to da na rubuta ta: (wato ayar da ta sauko kan batun jifa) "Ash sheikhu wash sheikhatu far jumuhuma albattata" ma'ana' "Tsoho da tsohuwa (da suka yi zina) to ku jefe su ba makawa" sai Umar bin Khad'd'abi ya k'ara da cewa: Lallai mun karanta wannan ayar.
To wannan ruwayar da aka ruwaito daga Umar bin Khad'd'abi dangane da jefe mazinata wanda ya nuna sun karanta ta, amma yanzu babu ita, ta zo cikin littafai da yawan gaske, wanda daga cikinsu akwai:
1. Sahih Muslim juzu'i na 3 babin hudud.
2. Sahih Bukhari juzu'i na 4 shafi na 179.
3. Tafsirin Tabari juzu'i na 1 shafi na 361 a bugun Bulak. Kamar yanda Bukhari ya ruwaito a cikin tarihinsa daga Huzaifa yana cewa: "Na karanta wa Manzo (S.A.W) suratul Ahzab sai na manta aya saba'in (70) daga cikinta, kuma ban same su ba (wato sun b'ace)." Kamar kuma yanda Abu Ubaida ya fitar a cikin Gana'im haka nan Ibnul Anbari da Ibnu Murdawaihi daga Ummul Muminin A'isha tana cewa: "Suratul Ahzab ta kasance a zamanin Manzo ana karanta ta aya dari biyu (200) ne, to yayin da Usman (R.A.) ya rubuta mus'hafi bai sami sauran ayoyin ba sai abin da yake nan a yanzu (wato aya 73)."
Wannan ruwayar ta zo a cikin Durrul Mansur juzu'i na 5 shafi na 180, kamar yanda ta zo a cikin Itkan fi ulumil Kur'an juzu'i na 2 shafi na 25. Wanda duk yake neman k'arin bayani dangane da irin wad'annan ruwayoyin sai ya duba wad'annan littattafai da zamu ambata:
Sahihul Bukhari juzu'i na 3 shafi na 305 Al Itkan juzu'i na 1 shafi na 66
Tafsirin Ruhul Ma'ani juzu'i na 1 shafi na 20 da kuma na 25, bugun Munira a Masar.
Durrul Mansur juzu'i na 1 shafi na 105.
Amma duk da samuwar irin wad'annan ruwayoyi wad'anda suke bayani k'arara game da jirkita Kur’ani da tawayarsa wad'anda aka samu a littattafan malaman AhlusSunna, sai mu samu cewa AhlusSunna ba su yi imani da cewa Kur’ani yana da tawaya ko an jirkita shi ba, abin da dai suke yi shi ne suna tawilin wad'annan ruwayoyin ne ta yanda zasu kare darajar Kur’ani da nesanta shi daga tawaya ko jirkita.
A d'aya bangaren kuma za mu samu cewa mabiya mazhabar Ahlul Baiti ba su tuhumar 'yan uwansu musulmi Ahlus Sunna da cewa sun yi imani da tawayar Kur’ani, a dalilin wad'annan ruwayoyin da aka ruwaito cikin littattafansu, duk da cewa suna iya riko da irin wad'annan dalilan masu k'arfi wad'anda suke cike mak'il a manya manyan littattafan Ahlus Sunna wad'anda su malaman suka yarda da su, domin tuhumarsu kan imani da tawayar Kur’ani, sai dai saboda (Su mabiya mazhabar Ahlul Baiti sun) kyautata zato ga 'yan uwansu AhlusSunna, tare da kwad'ayin had'in kan musulmi wanda shi ne sirrin k'arfinsu gurin fuskantar mak'iyan musulunci masu neman ruguza shi, wannan shi ne ya sa suke kau da kai don k'arfafa dank'on zumunci da 'yan’uwantaka na musulmi.
Amma abin takaici shi ne yadda mak'iya son had'in kan musulmi daga cikin masu da'awar cewa su ma Ahlus Sunna ne, ba su iya aikata kwatankwacin abin da mabiya mazhabar Ahlul Baiti suka yi, gurin yi musu kyakkyawan zato dangane da hukuncin wad'annan ruwayoyin kamar yanda su (mabiya ahlul Baiti A.S.) suka kyautata musu zato ba!
Irin wannan hukunci mai fuska biyu yana haifar da wasu tambayoyi masu rikitarwa idan mutum ya yi la'akari da su, irin tambayar da ta yi kama da cewa: Shin irin wad'annan mak'iya had'in kan musulmi sun jahilci tarin wad'annan ruwayoyin ne masu bayani a fili k'arara kan jingina jirkita da tawaya ga Kur’ani a littafan Ahlus Sunna a zahirinsu? Ko kuwa suna da wata manufa ne? ko akwai wani hannu ne a b'oye wanda yake ingiza gafalallu da hadafin tayar da fitina ta hanyar bijiro da tuhumomi da k'age-k'age don kekketa al'ummar musulmi, domin amfanin mak'iyan musuluci da musulmi, domin su zama cikin kwanciyar hankali daga hatsarin da ka iya rusa su matsawar kan musulmi a had'e yake?

Ra’ayoyim Malaman Shi'a
Manyan malaman Shi'a sun dage kuma sun yi tsayin daka domin kwaranye shamakin da ya lullube wannan mummunan makirci ta hanyar kore samuwar kowane nau'i na tawaya ko jirkita ko k'ari a cikin littafin Allah Mai girma, kamar haka:
1- Abu Ja'afar As-Saduk Muhammad bin Ali bin Husain bin Babawaihi Al-Kummi wanda ya yi wafati a shekara ta 381 bayan hijira, yana cewa: "Ak'idarmu dangane da Kur’ani mai girma wanda Allah ya saukar, wa manzonsa (S.A.W) shi ne wannan Kur'ani da ke tsakanin bango biyu. Wato; daga Fatiha zuwa Nasi, babu k'ari babu ragi, kuma duk wanda ya jingina mana cewa mun ce Kur’ani ya fi wanda ke hannun mutane yawa, to shi mak'aryaci ne. Littafin Al’I’itik'adat.
2-Imam Khumaini (Allah ya ji k'ansa) yana cewa lallai mu muna hana samuwar tawaya ko jirkita cikin Kur’ani hani mai tsanani kamar yanda wannan shi ne mazhabar masana daga malaman sunna da shi'a kamar yanda wannan shi ne abin da dukkan b'angarori biyu na musulmai suka yarda da shi. A wani wajen kuma a halin yana yin raddi ga wanda ya raya cewa akwai jirkita cikin Kur’ani, sai ya k'ara da cewa: To muna ce masa: Lallai b'acin wannan mummunar magana, kana b'acin irin wannan yasasshen ra'ayi ya fi k'arfin ya b'uya ga duk wani mai hankali.
Littafin Anwarul Hidaya fit ta'alik'at alal kifaya shaft na 243.
3-Sheikh Tusi babban malami masanin fikihu a mazhabar Jaafariyya wanda aka fi sani da sheihut ta'ifa wanda ya yi zamani tun shekaru dubu da suka gabata yana fadi a Muk'addimar Tafsirinsa; Tibyan cewa: k'ari ko ragi sam bai dace da martaba da matsayin Kur’ani ba.
Muk'addimar Tafsirin Ala'ur Rahman shafi na 25.

Hafiz Muhammad Sa’id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center for Islamic Propagation
Saturday, May 17, 2008

Ƙara sabon ra'ayi