Hadin Kai Sirrin Cin Nasara
Hadin Kai Sirrin Cin Nasara
Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Hadin kai mabudin cin nasara ne ga al’ummu a kan matsaloli daban-daban da kuma wajen ci gabansu, kai baki daya ma duniya tana tafiya ne a kan ka’ida da asasi na hadin kai.
Kananan koramu da suke haduwa a wuri guda su ne suke haifar da babban kogi, ta yadda su kuma koguna su shayar da tekuna manya-manya, haka nan digo-digon ruwa suke haifar da katuwar matattar ruwa ta yadda suke kasancewa masu karfi har su rika samar da wutar lantarki, sannan su shayar da manya-manyan filaye na noma, ta yadda wurare zasu koma kore gwanin ban sha’awa.
Haka nan mota sakamakon haduwar kanana da manyan sassa ta zama mota ta yadda za a iya shiga a je wuraren da ake bukata, haka itaciya daga sassa manya da kanana, kamar rassa da ganye idan ba su samu tushe daga sauya guda daya ba, to ba za a iya taba samun itaciya guda daya ba, ta yadda za a iya amfana da ita ta hanyoyi daban-daban.
Haka nan makaranta, ba tare da haduwar shugaban makaranta da malamai da ‘yan makaranta ba, makaranta ba zata taba samuwa ba, haka nan ajin karatu ba tare da jaka da littafi da alkalami ba, ajin karatu ba zai samu kammala ba. Haka nan fahimtar karatu yana bukatar natsuwa a kan abin da ake koyar da mutum, ba tare da wannan ba koyon karatu ba zai tabbatu ba. kamar dai na’urar daukar motoci dukkan karfinta ta mayar da shi ne a waje guda, ta haka ne take daukar abubuwan da take so ta kai wurin da take bukata ta ajiye su.
Tsakanin rundunonin sojoji guda biyu da suke fada, kawai rundunar da zata ci nasara ita ce, wacce ta kaucewa rabuwar kai da sabani a tsakanin juna kuma tana biyayya daga shugaba guda wanda ya san ya kamata, ta yadda zasu samu hadin kai mai karfin gaske a tsakaninsu, amma waccan rundunar da kowane daya daga cikin sojojinta yana wani abu daban da na dan’uwansa yake yi, tabbas ba tare da wani shakku ba, za a samu cin galaba a kansu.
Mutane ‘yan kadan wadanda kansu yake a hade zasu ci nasara a kan mutane masu yawa amma kawunansu a rarrabe, labarin sojoji guda dari uku wadanda wasu ‘yan fashi guda biyu kawai suka yi wa fashi kuma suka kwace musu makamai ya isa sheda a kan wannan al’amari na hadin kai da muke magana, a lokacin da aka kai wadannan barayi a kotu sai mai magana da yawun wadannan mutane 300, cewa ya yi sirrin nasarar wadannan barayi a kanmu shi ne sun kasance su biyu amma tare suke, amma mun kasance mu 300 amma ba tare muke ba.
A yau manya-manyan matsaloli na duniya ana taruwa a wuri guda sakamakon tattaunawa a tsakanin masana a warware su, idan har hankali da shari’a suna karfafa wannan lamari na hadin kai da tattaunawa tsakanin juna, sakamakon haka ne cewa hankalin mutum guda ba zai iya warware matsala ba ta fuskoki daban-daban kamar yadda mutane da yawa zasu iya kallon matsala ta fuskoki daban-daban kuma su warware ta sakamakon musayar ra’ayi tsakanin juna. Hakika hadin kai shi ne mabudin ci gaba da cin nasara a tsakani al’ummu.
Kur’ani Ya Muhimmantar Da Hadin Kai
Kur’ani mai girma a ko’ina yana kira ga musulmi da su kasance masu hadin kai a tsakani juna kuma yana yi musu kashedi da rarraba: “ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba” .
Mai yiwuwa an yi amfani da kalmar igiyar Allah ne a cikin wannan aya domin a nuna cewa mutanen da suke kansu a rarrabe kamar mutumin da ya fada ne a cikin rijiya, wato yana cikin duhun munafunci da magagin rarraba, sannan yana cikin matukar bukatar igiyar da zata fito da shi daga wannan duhun rijiya ta rarraba.
A mahangar Kur’ani daya daga cikin manyan abubuwa miyagu shi ne Allah madaukaki ya azabtar da wata al’umma da rarraba sakamakon wasu ayyuka nasu marasa kyawu, a kan haka ne Allah madaukaki yake cewa: “Ka ce shi mai cikakken iko ne wanda zai iya aiko muku da azaba daga saman kawunanku, ko kuma ta karkashin kafafuwanku, ko kuma ya sanya ku kungiya-kungiya ta yadda zaku dandani azaba a tsakaninku” .
Al’ummar da ta kasance kowane gungu ya yi wajensa, wato ba su karkashin shugabancin wani shugaba na Allah guda daya, ko alama ba su da alaka da Manzo (s.a.w) “Lallai mutanen da suka kasance sun rarraba addininsu kuma sun kasance kungiya-kungiya, to ko alama ba ka da alaka da su” .
Hadin Kai Daga Sunnar Manzo
A tarihin Manzo ma zamu ga cewa hadin kai tsakanin al’ummar musulmi wani abu ne wanda ya kasance abin yabo. Abu na farko da Manzo (s.a.w) ya fara yi a Madina shi ne, kulla ‘yanuwantaka tsakanin manyan kabiloli guda biyu na madina wato Aus da Kazraj. Wadannan kabiloli guda biyu a tsawon tarihi sun kasance suna yakar juna suna zubar da jini a matsayin abokan gaba guda biyu. Manzo mai girma da daukaka karkashin hukincin wannan aya ya daidaita tsakanisu wacce take cewa: “Lallai muminai 'yan’uwan juna ne don haka ku yi gyara a tsakanin ‘yan uwanku”. Da haka ne Manzo (s.a.w) ya kasance ya gyara tsakanin wadannan al’umma guda biyu ta yadda suka manta da tsohuwar gabarsu ta shekara da shekaru.
Hadin kai tsakanin musulmi ya zama wata babbar barazana ga yahudawan Yasriba, don haka ne har yanzu suke kokarin su ga sun kawar da wannan hadin kai da yake tsakanin al’ummar musulmi.
Juhudi Anudi wanda ake kira da (Shas) sakamakon hadin kai da Aus da kazraj suka samu, ya yi matukar bakin ciki don haka ne ya ingiza wani matashin bayahude ta yadda zai halarci taronsu ya kuma ci gaba da ambatar labaran yakunan da suka faru tsakanin wadannan kabilu guda biyu ta yadda zai kafa tushen munafunci a cikinsu, wannan makirci ne ya janyo wasu masu saukin fahimta daga cikin wadannan kabilu guda biyu, har ya kasance saura kadan su shiga yaki a gaban masallacin Manzo (s.a.w) kamar yadda suka saba a baya, ammacikin ikon Allah Manzo ya samu labarin abin da yake faruwa, cikin sauri Manzo ya shawo kan al’amarin da wadannan kalmomi nasa ta yadda ya sha gaban wannan rarraba wacce aka so kullawa ta hanyar wannan makirci. Ga abin da manzon yake cewa: “ku ji tsoron Allah, yanzu a gabana zaku raya sunnar jahiliyya, wannan kuma bayan Allah madaukaki ya shiryar da ku zuwa ga musulunci, sannan ya girmama ku da nisanta daga wannan muguwar Sunna, sannan ya tseratar da ku daga kafirci ya sanya zukatanku suka kusanci juna suna masu kaunar juna” .
Wani misali kuma abin da ya faru a shekara ta 6 bayan hijira, lokacin rundunar musulmi suka ci gaggarumar nasara a wani yaki a kasar bani Musdalak. Amma kwatsam a wannan lokaci tsakanin musulmai guda biyu tsakanin Muhajirun da Ansar suka fara rigima tsakanin juna a kan debo ruwa daga cikin rijiya, kowane daya daga cikinsu ya dauko makami sannan ya kira mutanensa da su taimaka masa, wato mutumin Makka ya kira mutanen Makka haka na Madina. A nan ma saura kadan wannan sabani ya janyo baraka da rarraba a tsakanin musulmi, amma sai Manzo a matsayinsa na wakilin hadin kai ya yi kokari ya kashe wannan wuta, sannan ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kauracewa irin wannan muguwar dabi’a.
Imam Ali (a.s) yana da wata magana mai kawatarwa a kan wannan al’amari:
“Kada ku rabu daga al’ummar musulmi masu yawa, domin kuwa taimakon Allah yana tare da al’umma, kuma ku guji rarraba domin kuwa mutumin da yake daban da al’umma to shi rabon shaidan ne, kamar yadda tunkiyar ware take rabon kura. “ Sannan imam a kan hakan ya ci gaba da cewa: “duk wanda ya janyo rarraba a tsakanin al’umma ku kashe shi ko da kuwa ya kasance ni ne.
Al’ummar musulmin sakamakon bin Kur’ani da Sunnar Manzo da Ahlul-baitinsa tsarkaka shekaru daruruwa sun kasance cikin wannan hadin kai wanda babu wata al’umma da take da wannan hadin kai kamarsu, sannan sakamakon haka ne suka samu damar warware wasu matsalolinsu da dama.
Amma abin bakin ciki wasu mutane masu karamin tunani sakamakon alaka da suke da ita da wasu makiya na waje suna so su kawo wasu matsaloli wadanda zasu kawar da wannan hadin kai mai dogon tarihi da yake tsakakin wannan al’umma.
Kasancewar yaki da irin wadannan tunane-tunane ya hau kan masana da malamai masu damuwa da al’amarin musulmin wannan al’umma, don haka ne muka ta shi tsaye domin amfani da koyarwar Kur’ani da Sunna mu bayyanar da ma’anar wadanan kalmomi (Shirka da Tauhidi) wadanda ake amfani da su domin raba kan al’umma, ta yadda za a haskaka wa matasa domin su kaucewa irin wannan matsaloli kuma su iya gane gaskiya daga bata, sannan su fahimci hikima daga safsada (amfani da wasu kalmomi masu kyawu domin batar da mutane) sannan su tserata daga wannan tarko mai kawo rarraba a tsakanin musulmi.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012
Ƙara sabon ra'ayi