Tunani Da Fikirorin Wahabiyanci

Tunani Da Fikirorin Wahabiyanci
Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Sabunta Tunani A kan Addini
Sabunta tunani a kan addini wanda a yau ake ta magana a kansa a jaridu, ba wani abu sabo ba ne wanda a yanzu a aka fara magana a kansa, wannan al’amari ya dade a tarihi ana magana a kansa, sannan tarihi da ala’dun musulunci sheda ne a kan hakan.
Bayan wafatin Manzo (s.a.w) da kuma cakudar musulunci da al’adu da tunanin daular Rom da mutanen Hindu da na Iran a wancan lokaci, don haka wannan fikira ta sabunta tunani a kan addini ta fara a cikin garuwan musulmi, wasu suka daga tuta da sunan masu kawo gyara da jaddada addini da kawar da bidi’a suka kafa kungiyoyi da wannan manufa. Sai dai kash aikin wadannan kungiyoyi bai taikata a kan su yi yaki da bidi’a ba, ai sai suka kawo wata sabuwar bida’ar ma a cikin addini. Wadanda suke kallon al’amuran daga nesa suna ganin cewa wadannan mutane suna gyara ne  da sabunta addini, amma a halin gaskiya su ne ma’anar wannan ayar da take cewa: “Idan a ka ce musu kada ku yi barna a bayan kasa sai su ce: Lallai mu masu gyara ne. “
Daga karshe a wannan zamani sai sabunta addini (Tajdidi) ya sanya sabuwar riga da sunan yaki da shirka, da wannan suna ne mai kawatarwa wanda yake kada zuciyar mai imani da Allah, ya yi amfani da shi wajen yada manufofinsa nakansa, sannan tarihin wanda ya kafa wannan akida yana komawa ne zuwa karni na takwas bayan hijirar Manzo mai tsira, bayan kashe wannan guguwa tasa, sai ta sake tashi a karni na sha biyu ta hanyar wani Mabiyinsa da sunan raya abin da wancan ya yi a shekarun da suka gabata, sannan sai karni na sha hudu bayan hijira aka ci gaba da yada wannan akida da manufar siyasa zuwa sassa daban-daban na kasashen musulmi.
Domin mai karatu ya san tarihin wanda ya kafa wannan akida da wadanda suka jaddada wannan tunani nasa na yaki da shirka, zamu ce wani abu a nan.
Ahmad Bn Taimiyya Harrani Damashki an haife shi a shekara ta 662H a wani gari da ake kira da Harran, a shekara ta 726 ya rasu a cikin gidan kurkuku a Garin Damashk a kasar Siriya. Ya fara yada tunaninsa na yaki da shirka da bidi’a daga shekara ta 698, amma ba tare da bata lokaci ba ya fuskanci kalu bale daga malamai da masanan zamaninsa. Sakamakon wannan fito na fito da ya fuskanta daga malamai ya sanya wannan kira nasa ya samu matsala da rashin ci gaba, saboda haka bai samu karbuwa ba ta a zo a gani a wannan lokaci, saboda haka sai ya kasance tunaninsa kawai za a iya samunsa ne a cikin littafansa da na almajiransa kamar su Bn kayyum Jauziyya (a tsakanin shekaru na 691-751). Amma bayan wucewar karni hudu sai duniyar musulunci ta kara fuskantar wannan ra’ayoyi nasa, domin kuwa Abdul wahab Najdi ya dukufa wajen rayawa da yada wannan ra’ayoyi na Ibn Taimiyya, wannan kuwa ya faru ne a tsakanin shekara ta (1115-1206) a kan wannan manufa kuwa ya samu karfafawar iyalan Ali sa’ud ta fuskar abin da ya shafi kudi da iko wajen yada wadannan ra’ayoyi na Ibn Timiyya, Amma duk da haka ra’ayoyin Ibn Taimiyya ba su isa zuwa sauran sassan duniyar musulmi ba, kawai sun takaita ne a kasashen Jaziratul Arab wato Makka da kewayenta.
Bayan faduwar daular Usmaniya da zuwan hukumar ali sa’ud da mamayewar da ta yi wa muhimman cibiyoyi kamar Makka da Madina, daga nan ne fa kuma wannan akida ta ci gaba da yaduwa. Bayan samun man fetur da wannan gwamnatin ali sa’ud ta yi a wannan lokaci, sai kuwa suka samu damar saye marubuta masu son duniya domin yin amfani da su wajen yada wannan akida ta su, suka kuwa taka muhimmiyar rawa a wannan fage.
Ta bangare guda kuwa a wannan lokaci malamai daga Sunna da Shi’a a Iraki, Sham da Misra suka ta shi tsaye wajen yaki da wannan akida mai hadari ta Ibn Taimiyya wanda a fasali na goma zamu fadi wasu manyan masana daga bangarorin guda biyu. A wannan gabatarwa kawai zamu yi dan gajeren bayani dangane da wannan akida, kamar yadda ake cewa itaciya mai nagarta ana ganeta daga ‘ya’yanta, don haka daga ‘ya’yan wannan itaciya masu daci na wannan akida zamu gane hakikanin wannan itaciya.
Muna iya takaita akidun wannnan mazhaba ta wahabyanci a cikin abubuwa guda uku kamar haka:

Abubuwan Da Wahabiyanci Ya Siffantu Da Su
1-Akidar Siffanta Allah Da Jiki
Yana daya daga cikin abuwan da musulunci yake alfahri da su shi ne tsarkake Allah madaukaki daga dukkan wani nau’i na jiki, sannan yana daya daga cikin taken musulunci a kan cewa “Babu wani abu da yake kama da Allah”. Don haka ne malaman Falsafa da Akida na muslunci shekaru masu tsawo suka ta shi tsaye wajen yaki da kalu balantar wannan akida ta siffanta Allah da jiki, Sakamakon haka ne suka kare musulunci kuma ba su ba da dama ba ga wadannan ma’abota wannan batattar akida su bata musulunci. Sannan kuma suka ci gaba da kalu balantar attaurar da take hannun yahudawa a yanzu wacce take ba ta asalin ba wacce Kur’ani yake siffantawa da mai haske da shiryaswa , wato wacce take siffanta Allah da jiki. Sannan ta sakko da martabar Ubangiji zuwa kasa, wacce har yake shiga cikin hemar Annabi Yakub har ma su yi kokowa da shi.  
Amma abin bakin ciki tauhidi a wajen Ibn Taimiyya, tauhidi ne na siffanta Allah madaukaki da jiki ta yadda ya sakko da Allah a kasa ya siffanta shi da malami mai wa’azi kamar yadda malami yake hawa a kan mimbari ya taka matakala daga wannan zuwa wannan, Shi ma haka Allah yake tafiya daga wannan wuri zuwa wannan wuri (Inda Ibn Taimiyya yake cewa Allah yana sakkowa daga al’arshi zuwa sama ta daya kamar yadda zamu gani a nan gaba kadan).
2-Tauye Daraja Da Matsayin Annabawa Da Waliyyan Allah
Annabawan Allah su ne mafi girma da daukaka a cikin halittun Allah, kuma Kur’ani da hadisan Manzo suna bayar da shaida a kan matsayi da daukakar Annabawa da cewa rayuwa da mutuwarsu duk abu guda ne kamar yadda suke da alaka da mutane a lokacin da suke raye, haka nan suna da alaka da al’ummar musulmi a yayin da ba su raye a duniya.
Amma a cikin mazhabar Ibn Taimiyya matsayin annabawa da waliyyan Allah daya yake da na sauran mutane wato da zarar sun bar duniya alakarsu da mutanensu zata yanke don haka ba su da wata ta cewa ga al’ummarsu.
 
3-Kafirta Sauran Al’ummar Musulmi
Ma’aiki mai girma a lokacin rayuwarsa ya yi iya kokarinsa wajen tabbatar da 'yan'uwantaka a tsakanin al'ummar musulmi wadanda suke da’awar kadaita Allah. Sannan ya hada kansu domin fito na fito da kafircin duniya. Sannan Al’ummar musulmi ma sakamakon tsayuwarsu a karkashin tutar tauhidi suka iya tsayuwa tsayin daka domin fito na fito a yakin da ya auku tsakanin musulmi da kiristoci, da kuma masu bautar gumaka wato Magul, ta yadda suka iya mai da makiyinsu daya daga cikinsu kuma daga baya ma ya zama daya daga cikin masu yada addininsu wato musulunci.
Amma abin bakin ciki wannan hadin kai wanda yake akwai a tsakanin al’ummar musulmi sakamakon zuwan wahabiyanci aka wayi gari an rasa shi a tsakaninsu. Sakamakon haka ne kawai wanda yake bin wannan mazhaba ta Ibn Taimiyya zai rabauta da sunan musulmi, amma duk wanda ba shi ba, to ya fita daga inuwar musulunci.
Wannan bangare yana daya daga cikin abin bakin ciki na wannan mazhaba ta wahabiyanci. Amma abin tambaya a nan shin wanda yake shugaban wannan mazhaba ta wahabiyanci za a iya kiransa da gwarzon addinin musulunci kuma mai raya sunnar Manzo da kawar da bidi’a?
Wannan littafi da yake a gabanka ya kai mai karatu, yana kunshe da cikakken bayani a kan wannan mazhaba kuma a cikin lafazi mai sauki. Da fatan wannan littafi ya zama kamar wata fitila mai haske a kan hanya wacce zata haskakawa matasa musulmi wajen fahimtar hakikanin musulunci, sannan ya kare su daga fadawa cikin tarkon masu yada wannan mazhaba.
Idan har wannan rubutu ya cancanci lada daga wajen Allah madaukaki, to ina sadaukar da ladan zuwa ga ruhin mahaifina Ayatullahi Sheikh Muhammad Husain Khiyabani Tabrizi (Allah ya jikansa). Domin kuwa shi ne farkon wanda ya fahimtar da ni hakikanin wannan mazhaba ta wahabiyanci.
Mu’assasar Imam Sadik (a.s) Kom  - Ja’afar Subhani  - 29 Zulkida 1421H - 5-12-1379 H.SH
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.comwww.hikima.orgwww.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ƙara sabon ra'ayi