Tsafi da Sihiri

Tsafi da Sihiri
Babu wani abu da ya zo a Kur’ani mai girma sai abin da yake nuna raunin tsafi da matsafa, da tona asirin surkulle da rufa idon da suke yi da nuna cewa; ba komai ba ne sai rufa ido; “Sai ga igiyoyinsu da sandunasu suna nuna masu da tsafinsu cewa; suna tafiya”. 1 kamar dai mai gani sai ya rika ganin igiyoyin nan da sandunan nan suna tafiya, da suke raya cewa tafiya ce ta rayuwar gaske.
Dabrasi yana cewa; ba suna tafiya ba ne, sai dai suna sanya yuranium a cikinsu ne, idan rana ta yi zafi sai yuranium ya mike, a sakamakon haka sai a samu motsi da masu kallo zasu dauka suna tafiya ne. Da wannan muna iya ganin ke nan ma’abota tsafi suna tasiri ne kan ganin mutane ta hanyoyin dubaru da surkulle iri-iri, ta yadda sai idanuwan mutane su nuna musu wani abu sabanin hakikanin abin da yake faruwa, ta yadda zasu ba shi wata ma’ana ta daban, sai suka nuna musu cewa; wadannan igiyoyin macizai ne.
Sai dai Allah madaukaki ya kira sihiri da tsafi da cewa abu ne mai girma domin girmama abin da mutane suke yi, sannan kuma girman shu’umancinsa da kawar da gaskiya da canja ta, da sanya wa gaskiya wata rigar ta daban. Wannan ke nan yana nufin sihiri ba komai ba ne sai kawar da tunanin mutane da zukatansu, da shagaltar da su da wani abu mai jan hankali sakamakon wani tasiri na musamman da aka yi a kan kwakwalensu, ko ganinsu, ko zukatansu.
Wani lokaci masu sihiri da tsafi, suna yin amfani da wasu abubuwa da suke ta karkashin kasa, wato; an boye su ga mutane, ta yadda mutane ba sa iya gani ko hango abubuwan da suke motsa wadannan igiyoyin da sandunan da makamantansu, sai mutane su yi tsammanin wannan motsin daga abubuwan da suke iya gani a zahiri ne. Irin wadannan dabarbarin ana kiran su da Simiyya da yaren Yunan wanda yake nufi rufa ido, ko tsafi, ko sihiri da larabci.
Wani lokaci sukan fesa wani abu a iska da zai iya sanya mutane su rasa hankulansu, sai su rika ganin abubuwan wasu iri kamar suna iya yin komai da motsinsu da zabin kansu, alhalin su mutanen ne aka yi wa sihiri har suka fada cikin wani yanayin da suke ganin hakan.
A nan muna iya gani a fili yake cewa; Kur'ani mai girma ba ya ganin tsafi a matsayin wani abu mai tasiri bisa hakikanin samammu, sai dai yana kawar da kwakwalen mutane da yin tasiri a cikin ganinsu ne, ta yadda zasu ga sabanin hakikanin abubuwan halitta, da abubuwan da suke faruwa. Don haka abin da muke gani ya yawaita na tsaface-tsaface a Afrika da sauran nahiyoyin duniya a bisa hakika ba komai ba ne sai rufa ido, da surkulle, da yaudara, da rudani, da kawar da hankulan mutane.
Sai dai hanzari ba gudu ba, tayiwu wani ya ce mana: Ai kuwa mun ga yadda tsafi yakan yi tasiri a bisa hakikanin abubuwa, sai mu ga ya yi tasiri wurin kashe mutane, da raba tsakanin masoya, da hada fada tsakanin mutane biyu, da sanya matattu su yi magana, da haukata mutane, da sauran miyagun ayyauka?
A nan muna iya cewa; da gaske akwai wannan tasirin, sai dai yana iya kasancewa ta hanyoyi mabanbanta: Imma dai ya kasance ta hanyar aljanu da Allah madaukaki ya yi nuni da cewa; suna taimakon mutane a kan abubuwa daban-daban musamman fadawa cikin sabo, kamar yadda ya zo a surar Jinni. Ko kuma ta hanyar wasu ilimomi wadanda suke da tasiri ga ruhin mutane kamar ilimin sunaye da haruffa wanda yake da tasirin gaske hatta wurin sanin abubuwan da zasu wakana bisa yakini ko kuma bisa hasashe. Ko kuma mutane masu karfin ruhi da Allah ya halicce su kuma ya hore musu abubuwa domin su amfani mutane, misalin maita da sarrafa abubuwan halitta sakamakon ruhi mai karfi da mai yin hakan yake da shi duk ya hada irin wannan, wannan yana kama da remot ne da yake iya sarrafa na'urori daga nesa a bisa misali.
Sai dai dukkanin wadannan lamurran ba sa iya kasancewa sai idan Allah ya so, don haka ne idan Ubangiji ya ga dama sai ya cire wannan karfin da tasirin, a sakamakon haka ne ba ya barin wannan tasiri ya wakana idan mai wannan karfin ruhin ko ilimin ya yi da'awar annabta da wannan ilimin ko sihirin.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Haidar Center For Islamic Propagation
Tuesday, September 15, 2009

Ƙara sabon ra'ayi